"A Koresu": Kungiyar 'Yan Arewa Ta Ba Tinubu Shawara kan Rashin Tsaro

"A Koresu": Kungiyar 'Yan Arewa Ta Ba Tinubu Shawara kan Rashin Tsaro

  • Ana ci gaba da kokawa kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita a sassan daban-daban na Najeriya
  • Kungiyar Northern Ethnic Nationality Forum (NENF), ta ba da shawara ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
  • Kungiyar ta bukaci shugaban kasan da ya sallami wasu daga cikin ministocinsa wadanda ba su tabuka komai

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Kungiyar Northern Ethnic Nationality Forum (NENF), wadda ta kunshi shugabannin al’adu da na siyasa daga jihohi 19 na Arewacin Najeriya, ta aika sako ga Mai girma Bola Tinubu.

Kungiyar ta yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya gaggauta yin garambawul ga majalisar ministocinsa da kuma tsarin tsaro na kasa saboda tsanantar rikice-rikice a Najeriya.

An ba shugaban kasa Bola Tinubu shawara
Hoton shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yana addu'a Hoto: @DOlusegun
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jagoran kungiyar, Dominic Alancha, ya sanyawa hannu a ranar Lahadi, 7 ga watan Satumban 2025, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

An sake taso Tinubu a gaba kan cafke shugaban Falsɗinawa, an 'gano' makirci a ciki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiya ta ce 'yan Najeriya na cikin mawuyacin hali

Kungiyar ta ce ta yi nazari kan mawuyacin halin da al’ummar Arewacin Najeriya da kasa baki ɗaya ke ciki.

Ta bayyana cewa bayan shawarwari da dama ta yanke shawarar yin kira da a ɗauki matakan gaggawa don kawo sauyi.

Ƙungiyar ta bayyana rashin gamsuwa kan rashin katabus daga wasu ministoci, tana gargadin cewa ministocin ba su da wata kwarewa ko karfin siyasa da zai iya tafiyar da manufofin gwamnati.

Wace shawara aka ba Shugaba Tinubu?

"Nadin minista ba wai kawai tukuici ba ne, babban aiki ne mai matukar muhimmanci. Saboda haka muna kira ga Shugaba Tinubu da ya gaggauta rushewa da kuma sake fasalin majalisar zartarwa ta tarayya (FEC)."
"Inda za a maye gurbin ministocin da ba su tabuka komai da mutanen da su ke da gogewa, kwarewa ta musamman da kuma karfi a siyasa."

- Dominic Alancha

Kungiyar NENF ta koka kan rashin tsaro

Kara karanta wannan

"Yaudara ce": Gwamna Uba Sani ya fallasa 'yan siyasa kan matsalar rashin tsaro

Game da batun tsaro, kungiyar NENF ta yi tir da cewa ’yan bindiga, ta’addanci da garkuwa da mutane sun kassara noma, kasuwanci da sufuri a jihohi da dama, tana bayyana lamarin a matsayin “babban bala’i da ya kai kololuwa.”

Ana fama da rashin tsaro a Najeriya
Hoton shugaban kasan Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @DOlusegun
Source: Facebook

Ƙungiyar ta bayyana cewa hafsoshin tsaro na yanzu sun gaza duk da dimbin albarkatun da ke hannunsu, don haka ta bukaci a sallame su nan take.

Haka kuma, ta yi kira da a nada sababbin hafsoshin tsaro wadanda za su samar da sakamakon da ake bukata, sannan ta nemi a ayyana dokar ta-baci kan tsaro a Arewacin Najeriya.

Tambuwal ya yi zarge-zarge kan Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya yo zarge-zarge kan gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da jam'iyyar APC.

Tambuwal ya yi zargin cewa Shugaba Tinubu da APC ne su ke kunna wutar rikici a jam'iyyun adawa domin hana su zaman lafiya

Sanatan mai wakiltar Sokoto ta Kudu a majalisar dattawa ya bayyana cewa shugaban kasan da jam'iyyar APC suna shirya makircin da zai ruguza jam'iyyun adawa a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng