Sulhu Alheri ne: Yadda Yan Bindiga Ke Kare Yan Gari daga Harin Miyagu daga Waje

Sulhu Alheri ne: Yadda Yan Bindiga Ke Kare Yan Gari daga Harin Miyagu daga Waje

  • An yi sulhu da yan bindiga a wasu kananan hukumomi a jihar Katsina bayan fama da hare-hare
  • Kamar a Jibia da ke jihar, ’yan bindiga da suka shiga yarjejeniya da al’umma yanzu suna kare kauyuka
  • Majiyoyi sun tabbatar da cewa yan bindigar suna kare yan gari daga hare-haren waje maimakon kai musu farmaki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Katsina - An samu zaman lafiya da fahimtar juna a wasu yankunan da ke jihar Katsina bayan sulhu da yan bindiga.

Biyo bayan yarjejeniyar zaman lafiya a Jibia da ke Katsina, ’yan bindiga da ke addabar yankin sun fara kare al’umma daga hare-haren waje.

Wasu yankunan Katsina sun yi sulhu da yan bindiga
Taron yan siyasa, sarakuna yayin sulhu da yan bindiga a Safana a Katsina. Hoto: @ZagazOlamakama.
Source: Facebook

Wani rahoton Daily Nigerian ya tabbatar da cewa wasu yan bindigar na kare yan gari bayan zaman sulhu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan bindiga: Kananan hukumomin da suka yi sulhu

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi wa jami'an tsaro kwanton bauna a Katsina, an samu asarar rayuka

Yankuna da dama a jihar Katsina sun yi zaman tattaunawa da yan bindiga domin kawo karshen rasa rayuka.

Akalla kananan hukumomi hudu ne suka samu damar zama da yan bindiga domin samun zaman lafiya a yankunansu.

Daga cikin kananan hukumomin da suka yi zaman sulhu akwai karamar hukumar Safana da Jibia a wannan shekara.

Sauran sun hada da karamar hukumar Danmusa da kuma Batsari duk domin a samu sauki kan hare-haren da ake kai wa.

Wasu yan Katsina na ganin amfanin sulhu da yan bindiga
Taswirar jihar Katsina da ke Arewa maso Yamma. Hoto: Legit.
Source: Original

Mazauna jihar Katsina sun yaba da sulhu

Wani mazaunin Magama, Abubakar Mohammad, ya shaida cewa sun godewa Allah bisa zaman lafiya da ake samu yanzu a yankin.

Ya bayyana cewa kusan watanni shida da suka gabata aka shiga yarjejeniyar zaman lafiya da ’yan bindigar, tun daga lokacin babu hare-hare.

A cewarsa:

“Yawancin waɗannan ’yan bindiga mun san su, muna rayuwa tare da su, wasu abokanmu ne kafin su ware kansu.
“Mun godewa Allah tun da suka rungumi zaman lafiya, yanzu suna zuwa kasuwa ba tare da dauke da bindiga ba.

Kara karanta wannan

Mutanen gari sun cire tsoro, sun yi gaba da gaba da 'yan bindiga a jihar Sakkwato

“Idan ka shiga daji, za ka ga suna dauke da bindiga suna kare mu daga hare-haren Zamfara ko wasu kananan hukumomi.”

Sulhu: Yadda yan Katsina suka koma gona

Mohammad ya ce yanzu mutane sun koma gonaki bayan dogon lokaci suna tserewa, yana bayyana lokacin a matsayin lokacin amfanin gona.

Wani mazaunin yankin, Uzairu Rabiu, ya ce:

“Wata biyar zuwa shida kenan babu hare-haren ’yan bindiga, muna cikin farin ciki.
“Babban matsalar mu yanzu ambaliya ce, ta lalata gidaje kusan 50 a Bagaruwa, muna neman taimakon gwamnati.”

Sakataren 'Jibia People’s Forum', Zubairu Sani, ya yaba wa Gwamna Dikko Radda kan jajircewarsa, yana bayyana cewa yarjejeniyar ’yan bindigar ma suka nema.

Wasu al'umma sun yi sulhu da yan bindiga

Mun ba ku labarin cewa shugabannin al’ummar Kurfi sun nema wa kansu mafita a kan harin da ’yan bindiga a jihar Katsina.

Fitattun manayan ’yan bindiga sun yi alƙawarin daina kashe-kashe, garkuwa da mutane da kuma satar shanu da su ka saba.

Al’ummar Kurfi sun kulla yarjejeniya da 'yan bindiga da fatan a kawo karshen dauki daidai da 'yan ta'adda ke masu a yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.