"Mun Gano Tushen Matsalar": Gwamna Uba Sani Ya Fadi Dalilin Sulhu da 'Yan Bindiga
- Gwamnan jihar Kaduna, ya fito ya yi magana kan matakin da gwamnatinsa ta dauka na yin sulhu da 'yan bindiga
- Uba Sani ya bayyana cewa sai da su ka gudanar da bincike don gano ainihin abubuwan da suke haddasa matsalar rashin tsaro
- Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa dole ne shugabanni su dauki alhaki kan matsalar rashin maimakon dora laifin a kan wasu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya yi magana kan shirin sulhu don samun zaman lafiya da gwamnatinsa ta bullo da shi.
Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa shirin ya haɗa sarakunan gargajiya, shugabannin addini da sauran masu ruwa da tsaki.

Source: Facebook
Gwamna Uba Sani ya bayyana hakan yayin da jawabi a wajen wani taro da kungiyar Izala ta shirya a Kaduna, cewar rahoton jaridar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wadanne matsaloli suka haddasa rashin tsaro?
Uba Sani kawo misali da Birnin Gwari, inda Sarkin ya jagoranci kokarin da ya haifar da zaman lafiya bayan shafe watanni shida ana tattaunawa domin fahimtar ainihin dalilan rashin tsaro.
"Mun gano cewa talauci, rashin ayyukan yi, karancin makarantu, asibitoci, da harkokin kasuwanci a karkara ne suka tura mutane cikin aikata laifi."
- Gwamna Uba Sani
Gwamna Uba Sani ya jaddada cewa dole ne shugabanni su ɗauki alhakin matsalar tsaro maimakon jefa laifi kan wasu, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.
Megasa Uba Sani ya yi sulhu da 'yan bindiga?
"Bai kamata mu yaudari jama’armu ta hanyar cewa Shugaba Tinubu ko mai ba da shawara kan harkokin tsaro na kasa, Nuhu Ribadu, su ne masu alhakin matsalar ba."
"Bai kamata mu sa ran za su je Giwa, Birnin Gwari ko dajin Dansadau don su magance mana matsalar ba. Mu ne jama’a suka zaɓa, kuma mu ne ke da alhakin yin duk mai yiwuwa don kare mutanenmu.”
"Na yanke shawarar ɗaukar hanyar yin sulhu a Kaduna wajen magance matsalar tsaro, saboda ni Allah zai tambaya a ranar lahira."
- Gwamna Uba Sani

Source: Facebook
Hakazalika, Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa bindigogi kadai ba za su iya kawo karshen matsalar rashin tsaro ba.
Sai dai wannan martanin ya zo ne ’yan kwanaki bayan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, ya soki shirin tattaunawa da ’yan bindiga.
Karanta wasu labaran kan 'yan bindiga
- 'Yan bindiga sun yi wa jami'an tsaro kwanton bauna a Katsina, an samu asarar rayuka
- 'Yan bindiga sun kashe mutane, an yi awon gaba da wasu 130 a Katsina
- Ado Aleiro: Jagoran 'yan bindiga ya kashe mayakansa a Zamfara, an ji dalili
- Yadda yan bindiga ke karbar haraji har N500,000 kafin a birne mamaci a kabari
Musulman Kudancin Kaduna sun yi korafi
A wani labarin kuma, kun ji cewa Musulman Kudancin Kaduma sun koka kan yadda ake kawo rarrabuwar kawuna a yankin.
Musulman karkashin kungiyar Concerned Muslim Ummah, ta bayyana cewa wasu manyan mutanen yankin suna raba kawuna jama'a ta hanyar amfani da tarihi da siyasa.
Kungiyar ta kuma karyata ikirarin da ake yi na cewa yankin Kudancin Kaduna, na da mutane Kiristoci ne kawai.
Asali: Legit.ng

