'Yan Bindiga Sun Yi Wa Jami'an Tsaro Kwanton Bauna a Katsina, an Samu Asarar Rayuka

'Yan Bindiga Sun Yi Wa Jami'an Tsaro Kwanton Bauna a Katsina, an Samu Asarar Rayuka

  • 'Yan bindiga dauke da muggan makamai sun yi ta'addanci bayan sun farmaki wani kauye a jihar Katsina
  • Lamarin ya auku ne lokacin da 'yan bindigan suka farmaki kauyen Magajin-Wando a karamar hukumar Dandume
  • Gwamnatin jihar Katsina ta tabbatar da aukuwar harin, inda ta bayyana irin barnar da 'yan bindigan suka yi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Katsina - ’Yan bindiga sun kai hari a kauyen Magajin-Wando da ke karamar hukumar Dandume a jihar Katsina.

'Yan bindigan sun kashe akalla mutane bakwai tare da yin garkuwa da wasu mutum uku a yayin harin.

'Yan bindiga sun kai hari a Katsina
Hoton gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, yana jawabi a wajen wani taro Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Source: Twitter

Shafin Zagazola Makama ya rahoto cewa lamarin ya faru ne a daren Juma’a kuma ya ci gaba har zuwa safiyar ranar Asabar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda 'yan bindiga suka kai hari a Katsina

Wasu ganau sun bayyana cewa maharan sun kutsa cikin kauyen ne sannan suka rika harbe-harbe kan mai uwa da wabi.

Kara karanta wannan

Mutanen gari sun cire tsoro, sun yi gaba da gaba da 'yan bindiga a jihar Sakkwato

Lamarin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyar nan take, yayin da wasu mutum biyu suka mutu daga ciwon harbin bindiga.

Yan bindigan sun kuma yi garkuwa da mutane uku, mata biyu da kuma wani yaro yayin harin.

Rahotanni sun ce mambobin kungiyar tsaro ta C-Watch sun yi musayar wuta da maharan a yunkurin ceto mutanen da aka sace tare da kwashe waɗanda suka ji rauni zuwa asibitoci a Funtua da Katsina.

Sai dai, a kan hanyarsu ta dawowa, 'yan bindiga sun yi musu kwanton bauna inda suka kashe karin mutane biyu tare da jikkata wasu mutum takwas.

Gwamnatin Katsina ta yi magana kan lamarin

Gwamnatin jihar Katsina ta tabbatar da mutuwar mutane bakwai a harin da 'yan bindigan suka kai a kauyen, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kwamishinan tsaron cikin gida da harkokin cikin gida na jihar, Dr Nasir Mu’azu, shi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar a Katsina.

"Gwamnatin jihar Katsina ta tabbatar da wani mummunan lamari da ya faru daren jiya, misalin karfe 11:00 na dare, inda rayuka bakwai suka rasu a lokacin da ’yan bindiga suka kai hari a kauyen Magajin-Wando da ke karamar hukumar Dandume."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi wa jami'an tsaro kwanton bauna, an samu asarar rayuka

"Godiya bisa saurin daukar mataki da kuma jarumtar da jami'an rundunar CWC suka nuna. Sun fatattaki maharan, wanda hakan ya hana abin zama bala’i mafi muni ga al’ummar."

- Dr. Nasir Mu’azu

'Yan bindiga sun yi barna a Katsina
Hoton gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Kwamishinan ya bayyana cewa waɗanda suka samu raunuka a lokacin harin an kwashe su cikin gaggawa zuwa asibiti don samun kulawar da ta dace..

"Sai dai, a hanyarsu ta zuwa asibiti, waɗannan maharan da suka rabu kashi-kashi sun yi musu kwanton bauna."
"A yayin musayar wutar da ta biyo baya, an ragargaza motar CWC da harbin bindiga, amma jami'an sun yi jarumta, suka kuɓuta daga kwanton baunan sannan suka koma lafiya."

Dr. Nasir Muazu

A cewar kwamishinan, an kona motar jami'an rundunar CWC a lokacin kwanton baunan.

'Yan bindiga sun sace mutane a Katsina

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hare-hare a wasu kauyukan jihar Katsina.

'Yan bindigan sun kwashe kwanaki uku suna kai kai hare-hare a kauyuka guda uku na karamar hukumar Sabuwa.

A yayin hare-haren, sun kashe mutane shida tare da yin awon gaba da wasu sama da mutum 130.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng