Sukar Tinubu Ta Jefa Sowore a Matsala, an Hada Shi Fada da Kamfanin X
- Hukumar DSS ta baiwa shafin sada zumunta X wa'adin awanni 24 don cire wani rubutu na Omoyele Sowore da ya yi
- Sowore ya yi wani rubutu inda ya ke zargin Shugaba Bola Tinubu da karya kan abin da ya shafi cin hanci a gwamnatinsa
- Sai dai Sowore ya yi martani mai zafi kan lamarin wanda ke nuna cewa ba zai taba janyewa daga abin da yake yi ba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Hukumar DSS ta tura wasika ta musamman ga kamfanin X da aka fi sani da Twitter a baya kan Omoyele Sowore.
Hukumar ta bukaci shafin sada zumunta X da ya goge wani rubutu na Omoyele Sowore da ke zagin Shugaba Tinubu.

Source: Twitter
Gargadin DSS kan rubutun Sowore a X
Hukumar ta bayyana cewa rubutun ya “wulakanta” Shugaban kasa, kuma yana barazana ga tsaron kasa, cewar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ce rubutun na iya haddasa tashin hankali a kasar duba da cin mutunci da Sowore ya yi ga Tinubu kan kalamansa game da cin hanci.
Sowore ya bugi kirji kan rubutun da ya yi
Sai dai Sowore ya fitar da sanarwa a X inda ya yada wasikar da kamfanin ya turo masa game da bukatar DSS.
A cikin rubutun, Sowore ya ce ba zai taba cire wannan rubutu ba kuma babu wansa ya isa ya saka shi.
Sowore ya ce:
"Da safiyar yau, X (wanda ake kira Twitter a baya) ya tuntube ni kan wasiƙar barazana da takaici da ya samu daga hukumar DSS saboda rubutuna kan Tinubu.
"Ɗaya daga cikin zabin da 'ba zan taɓa yi ba' shi ne gogewa ko share wannan rubutu da na yi, nagode, @X."
Sowore dai ya kasance dan gwagwarmaya da ke yawan sukar gwamnati da jami'an tsaro kan abubuwan da suke aikatawa.

Source: Twitter
Wasikar da DSS ta turawa X kan Sowore
A wasikar DSS, an nuna cewa rubutun da Sowore ya wallafa a ranar 25 ga Agusta ya kira Tinubu a matsayin mai laifi kuma makaryaci a Brazil.
DSS ta ce wannan rubutun yana iya haifar da tarzoma, 'da lalata suna' kuma zai iya kawo sabani tsakanin jama’a tare da barazana ga tsaron kasa.
Hukumar ta kara da cewa rubutun ya saba dokoki da dama ciki har da dokar kafofin sada zumunta da kuma ta hana ta’addanci a kasa.
DSS ta gargadi X cewa idan ba ta cire rubutun cikin awanni 24 ba, gwamnati za ta dauki matakai masu tsauri don kare martaba da tsaro.
Zulum ya yi martani mai zafi ga Sowore
Kun ji cewa Gwamna Babagana Zulum ya karyata zargin Omoyele Sowore da ya yi zarge-zarge kan gwamnatin jihar Borno.
Sowore ya yi ikirarin cewa an kashe biliyoyin kuɗi kan tubabbun yan Boko Haram yayin da matasa ke tsare ba bisa ka’ida ba.
Kakakin Zulum ya bayyana cewa shirin DRR yana taimaka wa waɗanda rikici ya shafa, ba wai kawai ga tsofaffin ’yan Boko Haram ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


