Za a Iya Samun Matsala kan Wadatar Fetur, Dillalan Mai Sun Taso Dangote a Gaba
- Kungiyar PETROAN ta sanar da dakatar da daukowa da rarraba man fetur na kwana uku a Najeriya baki daya
- Matakin kamar yadda aka tabbatar zai fara aiki daga 9 ga Satumbar 2025 don adawa da danniya a kasuwar man fetur
- Shugaban PETROAN Billy Gillis-Harry ya ce matakin na lumana ne, domin kare hakkin ma’aikata
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Kungiyar masu gidajen man fetur PETROAN ta sanar da shirin dakatar da daukowa da rarraba man fetur a fadin Najeriya.
Kungitar ta ce za ta kawo tsaiko na kwana uku daga 9 ga Satumbar 2025 saboda shirin attajiri Aliko Dangote wanda suke ganin babu adalci.

Source: Getty Images
Yan kasuwa sun taso Dangote a gaba
Matakin ya biyo bayan sanarwar NUPENG cewa ma’aikata za su daina aiki daga 8 ga watan Satumba saboda batun rarraba mai na Dangote, cewar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
PETROAN ta fitar da sanarwa ranar Asabar da Joseph Obele ya rattabawa hannu, inda ta ce dakatarwar za ta fara daga safiyar Talata.
Ta ce:
“Kungiyar PETROAN ta bayyana cewa za ta dakatar da daukowa da rarraba man fetur na kwana uku daga 9 ga Satumba 2025 domin adawa da danniya.”

Source: Facebook
Musabbabin shirin kawo cikas ga rarraba fetur
Shugaban PETROAN na kasa, Billy Gillis-Harry, ya ce za a dauki matakin ne don yin adalci a fannin rarraba mai da kuma adawa da danniya a kasuwa.
Ya bayyana matakin a matsayin “na doka da lumana”, yana mai cewa hakan na nuna jajircewar PETROAN wajen kare ma’aikata da farashin mai da ‘yan Najeriya.
Gillis-Harry ya roki shugaban kasa Bola Tinubu, ministan mai, shugabannin NNPC, NMDPRA, DSS, da IGP su dauki mataki don kauce wa matsaloli.
Ya ce ma’aikatan gidajen man PETROAN suna karkashin NUPENG, wanda suma sun yi barazanar yajin aiki, don haka ba za a hukunta wadanda suka kauracewa aiki ba, Punch ta tabbatar.

Kara karanta wannan
Ba imani: Mahaifiya ta daure jaririyar da ta haifa ta birne ta da rai a dajin Kebbi
A bangaren kasuwa, Gillis-Harry ya soki dabarun kasuwanci na Dangote, yana mai cewa hakan na iya rusa ‘yan kasuwa da direbobin mota.
Ya gargadi ‘yan Najeriya kada su ruɗu da ragin farashi na wucin gadi, saboda danniya na iya haddasa rashin aikin yi da tasirin tattalin arziki.
PETROAN ta ce tana ci gaba da tattaunawa a Lahadi da Litinin, amma za ta ci gaba da shirin idan ba a samu mafita ba.
Kungiyar dillalan mai ta kara da cewa ta kafa kwamitin mutum 120 domin sa ido a gidajen mai da kuma kare kadarori yayin wannan mataki
Dangote, yan kasuwa sun fitar da farashi
Mun ba ku labarin cewa kamfanonin Dangote, Aiteo da AA Rano sun daidaita farashin litar man fetur daga N821 zuwa N823 a Najeriya.
Masana sun bayyana cewa wannan sauyi ya samo asali ne daga hauhawar farashin danyen mai a kasuwar duniya wanda ake da tasiri a farashin mai.
Rahotanni sun nuna cewa farashin gidajen mai bai sauya ba tukuna, amma ana iya ganin karin farashi a yan kwanakin nan masu zuwa.
Asali: Legit.ng
