Mutanen Gari Sun Cire Tsoro, Sun Yi Gaba da Gaba da Yan Bjndiga a Jihar Sakkwato
- Mutanen gari sun tunkari yan bindiga bayan sace masu shanu da yan uwa a yankin karamar hukumar Tureta ta jihar Sakkwato
- Tawagar mazauna garin Bimasa sun samu nasarar ceto wadanda aka sace masu tare da kashe 'yan bindiga 10
- Shugaban karamar hukumar Tureta, Aliyu Tureta ya tabbatar da wannan nasara da aka samu kan yan ta'adda a yankinsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Sokoto - Jama'a sun fara cire tsoro tare da fuskantar 'yan bindiga domin kubutar da 'yan uwansu da aka yi garkuwa da su a jihar Sakkawato.
Mazauna garin Bimasa da ke karamar hukumar Tureta a jihar Sakkwato a Arewacin Najeriya sun nuna jarumtaka wajen fuskantar ’yan bindiga.

Source: Original
Mutane sun tunkari 'yan bindiga a Sakkwato
Jaridar Leadership ta kawo rahoton cewa jama'ar garin Bimasa sun yi kukan kura, sun afkawa 'yan bindiga, kuma bisa sa'a, sun ceto ’yan uwansu da aka yi garkuwa da su.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bugu da kari, mutanen da suka yi wannan jarumta, sun yi nasarar kashe fiye da yan bindiga 10 yayin artabu.
Rahotanni daga mazauna yankin sun bayyana cewa mutanen kauyen sun bi sawun ’yan bindigar har cikin daji, suka yi musu luguden wuta, sannan suka kashe akalla yan ta'adda 10 daga cikinsu.
An ceto mutanen da aka yi garkuwa da su
Baya ga haka, jaruman mutanen Bimasa sun ceto mutanen da aka yi garkuwa da su tare da kwato dabbobin da aka sace masu kwanakin baya.
Haka zalika, sun kuma kwamuso mutum daya daga cikin ’yan bindigar, inda suka dawo da shi cikin gari.
Shugabannin al’ummar garin Bimasa sun yaba da wannan jarumtaka, tare da rokon hukumomi da su kara karfafa tsaron saboda gudun ramuwar gayya daga ’yan bindigar.
Mutanen gari sun hallaka 'yan bindiga
Shugaban karamar hukumar Tureta, Aliyu Tureta, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an kashe ’yan bindiga shida (6) tare da kwato shanun jama’a da dama.
Karamar hukumar Tureta ta shafe tsawon lokaci tana fama da matsalar tsaro kama daga hare-haren ’yan bindiga, garkuwa da mutane, da kuma raba dubban jama’a da muhallansu.

Source: Facebook
Jama'a sun fara nuna fushinsu kan tsaro
A baya-bayan nan, daruruwan mazauna yankin sun gudanar da zanga-zanga kan halin da suke ciki ma rashin tsaro.
Yayin zanga-zangar, sun bukaci gwamnatin tarayya da ta jiha su dauki matakan gaggawa don shawo kan matsalar.
Matasa sun yi barazanar daukar makamai don kare kansu idan gwamnati ta kasa samar da tsaro mai inganci.
Matasa sun farmaki mataimakin gwamnan Sakkwato
A wani labarin, kun ji cewa wasu fusattatun matasa sun farmaki ayarin mataimakin gwamnan jihar Sakkwato saboda yawaitar hare-haren yan bindiga.
Majiyoyi sun shaida wa 'yan jarida cewa mataimakin gwamnan ya kai ziyara Shagari domin jaje ga mutanen da ‘yan bindiga suka tarwatsa lokacin da matasan suka yi kansa.
Tuni dai jami'an tsaro suka fara bincike kan lamarin kuma sun kama mutum hudu da ake zargin suna da hannu a kai wa mataimakin gwamnan hari.
Asali: Legit.ng

