'Yan Bindiga Sun Kashe Mutane, an Yi Awon Gaba da Wasu 130 a Katsina

'Yan Bindiga Sun Kashe Mutane, an Yi Awon Gaba da Wasu 130 a Katsina

  • 'Yan bindiga dauke makamai sun yi ta'asa bayan sun kai hare-haren ta'addanci a wasu kauyukan jihar Katsina
  • Miyagun sun sace mutane masu yawa tare da hallaka wasu da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba a karamar hukumar Sabuwa
  • Mutanen yankunan sun yi bayanin yadda 'yan bindigan suka rika bi gida-gida suna aikata barna

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Katsina - ‘Yan bindiga sun kashe mutane shida tare da yin garkuwa da fiye da mutane 130 a cikin jerin hare-haren da suka kai a jihar Katsina.

'Yan bindigan sun kai hare-haren ne a kauyuka daban-daban na karamar hukumar Sabuwa ta jihar Katsina cikin kwanaki uku.

'Yan bindiga sun yi ta'asa a Katsina
Hoton gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda a wajen wani taro Hoto: @dikko_radda
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ce wasu mazauna yankunan da abin ya shafa ne suka tabbatar mata da hakan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda 'yan bindiga suka yi barna a Katsina

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi wa jami'an tsaro kwanton bauna a Katsina, an samu asarar rayuka

Sun bayyana cewa a ranar Lahadi da misalin ƙarfe 11 na dare, ‘yan ta’adda sun kai hari kauyen DanKurmi, inda suka shafe akalla sa’o’i huɗu suna shiga gidaje suna yin ta'asa.

A karshe, sun yi garkuwa da akalla mutane 79 bayan sun kashe wasu mutum huɗu.

Wata majiyar ta bayyana cewa a wasu gidajen sun yi garkuwa da magidanta, matansu da ‘ya’yansu gaba ɗaya, yayin da a wasu gidajen kuma suka sace mata da yara, tare da ɗaukar wasu kayayyaki masu daraja.

“Ba maganar kawai kayayyakin da suka kwashe ba, ciki har da babura da kayan abinci. Haka kuma sun harbe mutum huɗu ciki har da karamin yaro. A yanzu haka mahaifiyarsa tana kwance a asibiti."
"Ba a kauyen DanKurmi kaɗai suka kai hari a cikin daren ba, sun kuma kai hari wasu kauyuka da ke kusa. Bisa ga kididdigarmu, adadin waɗanda aka sace na iya kaiwa har mutum 200 daga dukkan kauyukan."

- Wata majiya

Wani mazaunin yankin ya tabbatar da wannan labari inda ya bayyana cewa an kai hari a kauyen Gamji, inda aka kashe mutum biyu aka kuma sace mutane 31.

Kara karanta wannan

Mutanen gari sun cire tsoro, sun yi gaba da gaba da 'yan bindiga a jihar Sakkwato

Ya ƙara da cewa an kuma sace wasu mutane 27 a Tsaunin Jino.

Hare-haren sun kuma shafi kauyukan Unguwar Goje, Unguwar Sani da Zagi-Zagi, inda aka kuma yi garkuwa da mutane da dama.

"Ba mu da cikakkiyar kididdiga tukuna, amma idan aka haɗa duka, mutanen da ke hannun ‘yan bindigar a yanzu za su iya kai mutum 200."

- Wata majiya

An tabbatar da harin 'yan bindigan

Kokarin yin magana da shugaban karamar hukumar, ɗan majalisar dokoki na jiha mai wakiltar Sabuwa, da kuma ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kankara/Faskari/Sabuwa, ya ci tura.

Sai dai wani babban jami’in gwamnati daga yankin, wanda ya roƙi a sakaya sunansa, ya tabbatar da faruwar hare-haren.

'Yan bindiga sun kai hare-hare a Katsina
Taswirar jihar Katsina, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ya bayyana cewa masu ruwa da tsaki daga karamar hukumar sun tafi babban birnin jihar domin ganawa da gwamnatin jiha kan yadda za a samu taimako wajen dakile wannan masifa.

“Gaskiya ne, duk waɗannan hare-haren sun faru ne cikin kwanaki uku; kuma bisa ƙididdigarmu, mutum huɗu aka kashe a Dan Kurmi aka kuma sace mutum 74."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi wa jami'an tsaro kwanton bauna, an samu asarar rayuka

"A kauyen Gamji, an sace mutane 31 sannan aka kashe mutum biyu. Kuma ‘yan bindigan sun je wasu kauyukan, sai dai ban da cikakken lissafi a yanzu."

- Wani jami'in gwamnati

Mutane na cikin tashin hankali

Sahabi Abdulrahman ya shaidawa Legit Hausa cewa mutane na rayuwa cikin fargaba saboda tsoron harin 'yan bindiga.

"Rayuwa ta koma ana yin ta cikin dar-dar. Miyagun mutanen nan sun hana jama'a sakat."
"Muna rokon Allah ya kawo mana karshen lamarin domin abin babu dadi. Ana kashe mutane tare da wulakanta su."

- Sahabi Abdulrahman

Jagoran 'yan bindiga ya kashe mayakansa

A wani labarin kuma, kun ji cewa jagoran 'yan bindiga, Ado Aleiro, ya hukunta wasu daga cikin mayakansa.

Jagoran 'yan bindiga ya kasbe mayaka bakwai bayan ya zargesu da cin amanarsa wanda hakan ya fusata shi.

Ado Aleiro wanda aka dade ana nemansu ruwa a jallo, ya zarge su ne da yin garkuwa da mutane ba tare da izninsa ba

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng