Asabar: NiMet Ta Yi Hasashen Sharara Ruwan Sama a Kaduna, Gombe da Wasu Jihohi
- Hukumar NiMet ta fitar da hasashen yanayi na Asabar 6 ga Satumba 2025, inda ake sa ran ruwan sama da guguwa a sassa daban-daban
- An yi gargadin cewa ruwan sama na iya kawo matsaloli kamar hazo, zamewa a kan hanya da kuma katse ayyukan jama'a a ƙasar nan
- NiMet ta shawarci al’umman da ke zaune a wuraren da ake fama da ambaliyar ruwa da su kasance cikin shiri da lura sosai
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta sanar da hasashen yanayi da zai shafi sassan Arewa da Kudancin Najeriya a ranar Asabar, 6 ga Satumba, 2025.
Sanarwar da aka fitar a ranar Juma’a 5 ga Satumba 2025, ta bayyana cewa za a fuskanci ruwan sama da guguwa a lokuta daban-daban na rana, musamman da safe da kuma yamma.

Source: Original
Hukumar hasashen yanayin ta bayyana haka ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na X da yammacin ranar Juma'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hasashen yanayin ruwa a jihohin Arewa
A cewar hasashen, da safiyar Asabar za a samu ruwan sama tare da guguwa a wasu sassan jihohin Sokoto, Kebbi, Kaduna, Taraba da Adamawa.
Da yammaci kuma, ana sa ran samun ruwan sama mai matsakaicin ƙarfi a wasu yankuna na Borno, Bauchi, Gombe, Zamfara, Kebbi, Katsina, Kaduna, Taraba da Adamawa.
Hukumar ta shawarci al’ummar yankin da su kasance cikin shiri, musamman masu zirga-zirga da masu amfani da hanyoyin ƙasa, saboda ruwan zai iya shafar hanya da kuma jinkirta tafiya.
Hasashen NiMet a wasu jihohin Arewa
A Arewa ta Tsakiyar Najeriya, NiMet ta bayyana cewa akwai yiwuwar ruwan sama mai sauƙi da guguwa da safiyar Asabar a jihohin Neja, Kwara, Nasarawa da Benue.
Sai dai a yamma kuma, ana hasashen ruwan sama mai ƙarfi a wasu sassan Nasarawa, Neja, Filato, Kogi, Kwara da Babban Birnin Tarayya Abuja.
Wannan na iya jawo matsaloli ga jama’a musamman masu kasuwanci da kuma manoma da ke aiki a gonaki a wannan lokaci.
Hasashen yanayi a jihohin Kudancin Najeriya
A kudancin Najeriya kuwa, NiMet ta ce da safe za a fuskanci gajimare tare da yiwuwar ruwan sama a wasu sassan Cross River da Akwa Ibom.
Hukumar ta ce da yammaci kuma, ana sa ran samun ruwan sama mai sauƙi a mafi yawan jihohin yankin.

Source: Getty Images
Hukumar NiMet ta gargadi al’umma
Hukumar ta yi gargadi ga jama’a da su yi hattara yayin da suke gudanar da ayyukansu a waje saboda iska mai ƙarfi da ruwan sama na iya katse hanyoyin sufuri.
Haka kuma, an shawarci al’ummomin da ke zaune a wuraren da ake fama da ambaliya su kasance cikin shiri don guje wa mummunan sakamako idan ruwan sama ya ƙaru.
An yi ambaliya a jihar Adamawa
A wani rahoton, kun ji cewa an yi mummunar ambaliyar ruwa a jihar Adamawa da ta jawo asarar dukiya mai yawa.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a wasu yankuna na karamar hukumar Numan da ke jihar.
Bayanan da Legit Hausa ta samu sun nuna cewa hukumar ba da agajin gaggawa ta NEMA ta riga ta yi gargadi kafin ambaliyar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

