Jerin Kananan Hukumomin Katsina da Su ka Rungumi Sulhu da 'Yan Ta'adda

Jerin Kananan Hukumomin Katsina da Su ka Rungumi Sulhu da 'Yan Ta'adda

Gwamnan jihar Katsina, Umaru Dikko Radda na daga cikin wadanda su ka yi kaurin suna wajen adawa ta kai tsaye da yin sulhu da 'yan ta'adda.

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar KatsinaA baya-bayan nan, ana samun karin kananan hukumomi a jihar Katsina da ke kulla sulhu da shugabannin 'yan ta'adda domin kawo karshe kashe su ba dare ba rana.

Ana shiga yarjejeniya da yan ta'adda a Katsina
Gwamnan jihar Katsina, Umaru Dikko Radda Hoto: Dr. Umaru Dikko Radda
Source: Facebook

Ga jerin wasu daga cikin kananan hukumomin Katsina da ke neman zaman lafiya da 'yan ta'adda:

1. Mazauna Jibia sun yi sulhu da 'yan ta'adda

A ranar 28 ga Fabrairu, 2025, mutanen ƙauyen Kwari, a karamar hukumar Jibia, kungiyar Jibia People’s Forum, su ka karbi mutane 10 a daga hannun 'yan ta'adda.

Kara karanta wannan

Wasu ma'aikata sun jawo wa kansu, gwamna ya kore su daga aiki nan take

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daily Trust ta wallafa cewa wakilan sojoji, DSS, 'yan sanda, jami'an tsaro na al'umma, masu gadi, sarakunan gargajiya da jami'an gwamnati na karamar hukuma sun halarci zaman sulhun.

An samu labarin cewa Audu Lankai, wani sanannen shugaban 'yan bindiga a yankin, ne ya fara wannan yunkuri na zaman lafiya.

Wata majiya mai tushe a Jibia ta ce:

"Gwamnatin jiha ba ta da hannu kai tsaye a cikin wannan batu. Gwamna ya sha nanatawa cewa ba zai yi sulhu da 'yan bindiga ba sai idan sun mika wuya a ƙarƙashin matsin lamba."
"Amma a wannan karon, shugabannin al'ummarmu sun gana da wani babban jami'in gwamnati kuma sun ba mu goyon baya, muddin za a yi hakan bisa sharuddanmu."

2. 'Yan ta'adda sun mika wuya a Batsari

Daily Post ta wallafa cewa a watan Agusta ne mutum 14 daga cikin manyan 'yan bindiga da ke aikata ta'asa a ƙananan hukumomin Batsari da Jibia sun mika makamansu.

Kara karanta wannan

Fetur: Yadda harajin Tinubu zai shafi ma'aikata, masu sana'a, 'yan kasuwa da sauransu

Sun kuma bayyana cewa sun yi haka ne a kokarin su na ganin sun rungumi zaman lafiya da dainu kashe mazaunu yankunan.

Jagoran Ayyukan ƙungiyar Peace For All Organisation, Hamisu Sai’id, wanda ƙungiyarsa ke jagorantar ƙoƙarin sasanci a tsakanin mazauna yankin da 'yan ta'addan.

Sai’id ya ce wannan nasara ta biyo bayan watanni na tuntuba, tattaunawa da gina alaka mai kyau a tsakanin mazauna yankunan da 'yan ta'adda.

Ya ce:

“A Batsari, muna da ƙungiyoyi takwas (8) na 'yan bindiga da suka mika wuya. Daga cikinsu akwai Abu-Radde, wanda ke da fiye da mayaka 500 a ƙarƙashinsa; Umar Black, wanda ke da sama da 300; da Turkur Dan-Nigeria, wanda ke da fiye da 200."
“A Jibia kuma, ƙungiyoyi shida (6) sun mika wuya, ciki har da Langai, Sahabi, da Ori."

3. Danmusa: Jama'a sun yi sulhu da 'yan ta'adda

Al’ummomi da ke Karamar Hukumar Danmusa a Jihar Katsina sun kulla yarjejeniyar zaman lafiya da ƴan bindiga.

Idan za a iya tunawa, a ranar Juma’a, 28 ga Fabrairu, an kulla yarjejeniya irin wannan da wasu manyan kwamandojin ƴan bindiga a Karamar Hukumar Jibia.

Kara karanta wannan

Yadda shugaba Tinubu ke yawan nadin mukamai ya warware daga baya

Wannan na zuwa ne bayan kulla yarjejeniyar zaman lafiya a Batsari da wani yanki na Karamar Hukumar Safana, duk a cikin jihar Katsina.

A duk yarjejeniyoyin da aka kulla, babban sharadi da aka cimma shi ne sakin duk wani wanda aka yi garkuwa da shi ba tare da wani sharadi ba.

An kuma bukaci ƴan bindiga da su dakatar da kai wa jama'a hari da aikata sauran laifuffua, yayin da su kuma aka ba su damar shiga cikin al’umma da kasuwanni ba tare da wata barazana ba.

4. An yi sulhu a karamar hukumar Safana

Karamar Hukumar Safana da ke Jihar Katsina ta kulla yarjejeniyar sulhu da ƴan bindiga da ke gudanar da ayyukansu a cikin dajin Gemi.

A cewar rahoton, dukkanin ɓangarorin sun amince cewa manoma da makiyaya za su sami 'yancin yin aikin noma da kiwo, kasuwanci, da kuma samun damar cin gajiyar ayyukan gwamnati ba tare da tsoro ko barazana ba.

Karamar hukumar ta kuma yi alƙawarin gyara makarantu, asibitoci da dam ɗin ruwa da ke amfani da al’ummomin Fulani a yankin, kamar yadda Daily Post a wallafa.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari ya karyata zargin kashe N100bn don samar da jirgin saman Najeriya

Mai sharhi ya magantu kan sulhu da 'yan ta'adda

Mai Sharhi kan al'amuran tsaro a Kano, Ambasada Nasiru Isah a Kano ya shaidawa Legit cewa shi sulhu alheri ne, amma akwai bukatar a yi taka-tsan-tsan wajen shiga yarjejeniya da 'yan ta'adda.

Ya ce:

"An yi irin wannan a Zamfara, an yi Neja, an zauna da wandannan yan bindiga. An samu nasarar yin hakan? An daina? Ba a daina ba."
"Wadanda ke kiran kansu 'yan ta'addan sun kasu kashi kashi, bayan an tsaya kan wani sai wasu su bullo, idan aka yi da su, wasu ma su sake bullowa, to su wane na gaskiya."

Ya ce dole ne kananan hukumomi su rika sanya jami'an tsaro a kan gaba idan batun tsaro ya taho.

Katsina: Gwamnati ta ja kunnen ƴan bindiga

A baya, mun wallafa cewa gwamnatin jihar Katsina ta aika da saƙon gargaɗi ga tubabbun ƴan bindiga da suka amince da zaman lafiya tare da ajiye makamansu. Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Nasir Mu’azu, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin, 16 ga watan Yuni, 2025, inda ya ce su shiga taitayinsu .

Mu’azu ya ce gwamnatin jihar ba za ta yi shakkar ɗaukar matakin da ya dace ba idan aka karya alƙawuran da aka cimma na tsagaita wuta wajen farmaki jama'a.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng