Kano: An Sake Tono Badakalar Biliyoyi da Ta Shafi Jami'in Abba da Gwamna Yake Landan
- Kwamishinan jihar Kano, Abdulkadir Abdulsalam, ya amince da sa hannu wajen biyan N1.17bn lokacin da yake Akanta Janar
- Hukumar ICPC ta ce an biya kudin ne ga kwangila maras tushe sannan aka karkatar da shi ta hannun dillalan canjin kudi
- An riga an dawo da N1.1bn cikin asusun ICPC yayin da ake ci gaba da bincike kan badakalar N6.5bn da ake zargin karkatarwa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano – Badakalar rashawa da ake bincikenta a gwamnatin jihar Kano ta sake fadada bayan da aka ce wani babban jami’i ya amince da hannu wajen karkatar da makudan kudi.
Rahotanni sun nuna cewa Kwamishina a Kano, Abdulkadir Abdulsalam, ya tabbatar da cewa ya sa hannu kan biyan N1.17bn da ya ke Akanta Janar a Nuwamban 2023.

Kara karanta wannan
Sabuwar hukumar Kano ta zuba buri, tana shirin tarkato harajin N5bn kafin karshen 2027

Source: Facebook
Wani rahoto da jaridar Premium Times ta fitar ya nuna cewa binciken hukumar ICPC ya bayyana cewa hakan ne ya kafa tubalin badakalar N6.5bn da ake zargin an karkatar daga kudin jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan sabon lamari ya kara dagula lamarin da ke ci gaba da rura wutar bincike da hukumar ICPC da EFCC ke gudanarwa kan zargin barnar makudan kudi a jihar Kano.
Bayani kan yadda aka karkatar da kudin
ICPC ta ce Abdulsalam ya amince da biyan N1.17bn ga wasu kamfanoni guda biyu, A.Y. Mai Kifi Oil and Gas da Ammas Petroleum Company ta hanyar takardun bogi da aka ce shi da kansa ya shirya.
Shugabannin kamfanonin daga bisani sun shaida wa masu bincike cewa ba su taba yin wannan kwangila ba, sai dai sun sanya hannu ne bisa umarninsa.
Bayan biyan kudin, an gano cewa sun shiga hannun 'yan canjin kudi; Gali Muhammad da Nasiru Adamu wadanda suka karɓi kuɗin kai tsaye daga asusun jihar.

Kara karanta wannan
Ministan Buhari ya karyata zargin kashe N100bn don samar da jirgin saman Najeriya
A cewar shaidun da aka tattara, daga cikin kudin an mika dala miliyan 1 a hannun Abdullahi Rogo a ofishin Kano Liaison da ke Abuja.
Maganar shaidu da kuma amsar ICPC
Shaidun da ICPC ta tattara sun tabbatar da cewa Abdulsalam da Rogo sun hada kai wajen karkatar da kudin jihar ta hanyar kasuwar canjin kudi.
A yayin tambayoyi, Abdulsalam ya amince da sanya hannu kan biyan kudin, amma bai iya bayyana dalilin da ya sa aka biya kudi ta hannun 'yan canji ba.

Source: Facebook
Hukumar ta kuma sanar da cewa ta riga ta dawo da N1.1bn daga cikin kudin da aka karkatar zuwa asusunta na musamman.
A halin yanzu, adadin kudin da aka gano an dawo da su ya kai N1.3bn, ciki har da wadanda aka gano a hannun Rogo.
An gayyaci shugabar karamar hukuma a Kano
A wani rahoton, kun ji cewa 'yan sanda sun gayyaci wata shugabar karamar hukuma domin amsa tambayoyi.
Rahototanni sun nuna cewa shugabar karamar hukumar da aka gayyata ita ce jagoran shugabannin kananan hukumomin Kano.
Wani bincike ya bayyana cewa ana zargin shugabar ne da muzguna wa wani mutum wajen amfani da jami'an tsaro ba bisa ka'ida ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng