Rasuwar Tsohon Shugaban Yan Sandan Najeriya Ta Bar Baya da Kura, An Samu Bayanai

Rasuwar Tsohon Shugaban Yan Sandan Najeriya Ta Bar Baya da Kura, An Samu Bayanai

  • Kwamishinan hukumar da'ar ma'aikata ta Najeriya kuma tsohon dan Majalisa ya yi bayani kan rasuwar tsohon sufetan yan sanda, Dr. Solomon Arase
  • A yan kwanakin nan dai an fara yada jita-jitar cewa Arase ya mutu ne sakamakon gubar da ya ci a abinci
  • Jita-jitar ta kuma jero sunayen wasu manyan mutane da ake zargin su suka hada baki wajen ganin bayan tsohon shugaban yan sandan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - An fara yada jita-jitar cewa tsohon sufetan rundunar yan sandan Najeriya, Dr. Solomon Arase ya mutu ne sakamakon gubar da aka sanya masa a abinci.

Wannan rahoto ya fara yawo a kafafen sada zumunta kwanaki kadan bayan tabbatar da rasuwar Arase a birnin tarayya Abuja.

Marigayin Arase.
Haton marigayi tsohon sufetan yan sandan Najeriya, Dr. Solomon Arase Hoto: @PoliceNG_CRU
Source: Twitter

Da gaske an sa wa Arase guba a abinci?

Kara karanta wannan

El Rufai ya fusata bayan 'yan sanda sun hana taron ADC a Kaduna

A rahoton Tribune, tsohon ɗan Majalisar Wakilai, Hon. E.J. Agbonayinma, ya karyata jita-jitar cewa Arase ya mutu ne bayan cin abinci mai guba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja, Hon. Agbonayinma ya bayyana waɗannan maganganu a matsayin “ƙarya, ɓatanci, kuma marasa tushe,” inda ya roƙi jama’a da su yi watsi da su.

“Babu wata guba da aka sa masa a abinci, labarin da ake yadawa kirkirarre ne," in ji shi.

Ya kuma musanta sunayen fitattun mutane da ake yadawa cewa suna da hannu a rasuwar Arase.

Su wa suka kirkiro karya kan rasuwar Arase?

Ya jaddada cewa irin waɗannan labaran na bogi aiki ne na “mutane marasa gaskiya da ke ƙoƙarin cin mutuncin wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa ƙasa hidima.”

Hon. Agbonayinma ya tabbatar da cewa Arase ya yi tafiya zuwa Morocco tare da matarsa, iyali da abokansa kafin ya mutu. Ya ce iyalan marigayin za su fitar da cikakkun bayanai a lokacin da ya dace.

Ya roƙi ‘yan Najeriya da su nuna mutuntawa da goyon baya ga iyalan da ke cikin jimami, maimakon yada labaran da ba su da tushe, rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya mutu? An ji gaskiyar halin da yake ciki

Dr. Solomon Arase.
Hoton marigayi shugaban rundunar yan sandan Najeriya, Solomon Arase Hoto: @bukolasaraki
Source: Twitter

Agbonayinma ya aika sako ga yan Najeriya

“Dr. Solomon Arase ɗan ƙasa ne nagari, uba, kuma ɗan siyasa wanda ya yi wa Najeriya hidima da sadaukarwa. Mu girmama shi cikin mutunci da daraja. Ya mutu a matsayin gwarzo da za a ci gaba da tunawa da shi,” in ji shi.

Agbonayinma ya shawarci jama’a da su rika tantance bayanai daga sahihan majiyoyi kafin yada su, domin kada su zama hanyar yaɗa labaran ƙarya.

Dr. Arase, wanda ya rasu kwanan nan, shi ne Sufeton ƴan sanda na 18 a Najeriya, kuma an san shi sosai saboda gudummawar da ya bayar wajen tabbatar da tsaro da yaƙi da laifuffuka a ƙasar nan.

Tsohon dan takarar gwamna ya bar duniya

A wani labarin, kun ji cewa tsohon dan takarar gwamna a jihar Ondo karkashin inuwar jam'iyyar SDP , Otunba Bamidele Akingboyeya rasu yana da shekara 60.

Kara karanta wannan

Allah bai karbi addu'ar Sanku ba, mai wasan barkwanci ya mutu a hadarin mota

Har zuwa lokacin rasuwarsa, shi ne Shugaba a kamfanin Benshore Maritime da Clog Oil Systems, sannan kuma shugaban WeAfrica Group.

Shugaban jam’iyyar SDP a jihar Ondo, Ebenezer Akinbuli, ya yi alhini tare da mika sakon ta'aziyya ga iyalan mamacin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262