Abba Kabir Ya Isa London domin Bikin Yaye Sarki Sanusi II bayan Gama Digiri na 3
- Mai martaba Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya isa birnin London domin bikin yaye shi a Jami’ar SOAS
- An shirya gudanar da bikin da liyafar cin abinci inda Sanusi II zai kasance cikin wadanda za a ya ye bayan gama karatu
- Sarki Sanusi II zai kuma jagoranci Sallar Juma’a a Masallacin New Peckham, London, a ranar 5 ga Satumba, 2025
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
London – Za a gudanar da wani gagarumin biki da ya hada Mai martaba Khalifa Muhammadu Sanusi II, bayan kammala digirin digirgir a jami’ar SOAS ta London.
Rahotanni sun nuna cewa tun a shekarar 2024 Sarkin ya kammala karatu a jami'ar bayan shafe shekaru.

Source: Facebook
Sanarwar da Audu Bulama Bukarti ya wallafa a Facebook ta nuna cewa bikin zai gudana da misalin karfe 2:00 na rana a yau Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tarihin karatun Sarki Muhammadu Sanusi II
Sanusi II ya dade yana da neman ilimi tun kafin hawansa mulkin jihar Kano, a shekarar 1981 ya kammala digiri a fannin tattalin arziki.
Daily Trust ta rahoto cewa a 1997 ya sake samun digiri na biyu a fannin Fikihun Musulunci a wata jami'a da ke Khartoum, Sudan.
Bayan tsige shi daga mukamin Sarki a 2020 ta hannun tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, Sanusi II ya koma jami’ar London domin ci gaba da karatu.
Wannan mataki ya ja hankalin al’ummar Najeriya da dama da suka yaba da jajircewar sa wajen neman karin ilimi duk da dawainiyar da ke tattare matsayinsa.
Baya ga haka, kammala digirin digirgir watau PhD a fannin shari’ar Musulunci a shekarar 2024 ya kara tabbatar da Sanusi II a matsayin daya daga cikin sarakunan da suka kai matakin PhD.
Sanusi II zai jagoranci Juma'a a London
A shafinsa na Facebook, an sanar da cewa Sarki Sanusi II zai jagoranci sallar Juma’a a Masallacin New Peckham, London, ranar Juma’a 5 ga Satumba, 2025 da misalin karfe 1:30 na rana.
Ana sa ran hudubar za ta jawo daruruwan masoya Sarkin da al’ummomin Najeriya da ke Birtaniya domin halartar sallar da sauran shirye shirye.

Source: Facebook
Abba Kabir ya tafi birnin London
Hakazalika, Mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya bayyana cewa ya tafi London domin halartar bikin.
Sanusi Bature ya taya Sarkin murna inda ya wallafa sakon yabo da fatan nasara a shafinsa na Facebook.
Rahoto ya nuna cewa Sanusi Bature yana tare da gwamna Abba Kabir Yusuf kamar yadda wasu hotuna suka tabbatar.
A yanzu haka dai kallo ya koma London domin ganin yadda bikin zai cigaba da gudana da irin bakin da za su hallara.
Sanusi II ya ziyarci iyalan Buhari a Kaduna
A wani rahoton, kun ji cewa Khalifa Muhammadu Sanusi II ya ziyarci gidan marigayi shugaba Muhammadu Buhari a Kaduna.
Hakan na zuwa ne bayan iyalan marigayin sun bar gidansu na Daura bayan kammala zaman makoki a jihar Katsina.
Ziyarar Muhammadu Sanusi II ta kawo karshen ce-ce-ku-ce da ake yi na cewa bai je wa iyalan marigayin ta'aziyya ba.
Asali: Legit.ng

