Tura Ta Kai Bango: Mutanen Gari Sun Yi Zazzafan Artabu da 'Yan Bindiga
- 'Yan bindiga dauke da makamai sun kai hari a jihar Sokoto inda suka yi awon gaba da mutanen wani kauye zuwa cikin daji
- Mutanen garin da lamarin ya auku sun yi ta maza, suka fantsama cikin daji domin yin artabu da tantiran 'yan bindigan da suka kawo musu hari
- Namijin kokarin da jajirtattun mutanen garin suka yi, ya sanya sun samu nasara kan 'yan bindigan da suka zo cutar da su
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Sokoto - Mazauna garin Bimasa da ke karamar hukumar Tureta a Sokoto, sun yi arangama da 'yan bindiga.
Mazauna garin sun cire tsoro sun nuna jarumtar da ba ta da misali, inda suka fuskanci ‘yan bindiga aka yi artabu.

Source: Twitter
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutanen gari sun fafata da 'yan bindiga
Mutanen garin sun samu nasarar ceto jama’ar da 'yan bindigan suka sace, tare da kashe wasu daga cikin maharan.
Majiyoyi sun bayyana cewa mutanen garin, ba tare da jin tsoro ba, sun bi ‘yan bindigan zuwa maboyarsu a daji, inda suka yi arangama da su kai tsaye.
Artabun da jajirtattun mutanen suka yi, ya yi sanadiyyar mutuwar wasu daga cikin ‘yan ta’addan.
Al’ummar garin sun kuma samu nasarar ceto mutanen da aka yi garkuwa da su a lokacin harin.
Wani abin alfahari kuma shi ne, mazauna garin sun dawo da ɗaya daga cikin ‘yan bindigan da suka kama zuwa cikin gari, inda suka yi bikin nasarar da suka samu tare da nuna jarumtar hadin kansu.
Shugabannin al’umma sun yabawa mutanen garin bisa jajircewarsu, tare da yin kira ga hukumomi da su turo jami'an tsaro domin gudun ramuwar gayya daga ‘yan bindigan.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun yi wa jami'an tsaro kwanton bauna a Katsina, an samu asarar rayuka
Mutane sun yaba da jarumtarsu
Wasu mutane a kafafen sada zumunta sun yaba da jarumtar da suka nuna. Ga kadan daga cikinsu a kasa:.
@Ahmadgidado01:.
"Ya Allah ka karesu ina tsoron masu ramuwar gayyar azzaluman nan"
@dodonfta:
"Masha Allah, Allah ya kara karemu gabaki dayan mu"
@imb1604:
"Ya yi kyau, idn da mutane za su rika yin hakan da tuni matsalar 'yan bindiga ta zama tarihi."
@salim_bashir_um:
"Wannan shi ne abin da ya dace, mutane su hada kai su kare kansu."
@LantarkiW:
""Babbar jarumta. Wannan ita ce hanyar kawo karshen 'yan bindiga da sace mutane. A ba mutane makamai, sannan a tura musu sojoji idan akwai bukatar hakan."

Source: Original
Ya kamata mutane su cire tsoro
Wani mazaunin Sokoto, Dalhat Usman ya shaidawa Legit Hausa cewa tuni ya kamata mutane su cire tsoro wajen tunkarar 'yan bindiga.
"Mutanen nan sun fi mu tsoron mutuwa. Suna amfani da tsoron da ake jinne kawai suna aikata abin da suka ga dama."

Kara karanta wannan
Mutanen gari sun cire tsoro, sun yi gaba da gaba da 'yan bindiga a jihar Sakkwato
"Sun yi namijin kokari da suka tunkari 'yan bindiga kuma har Allah ya ba su nasara."
- Dalhat Usman
'Yan bindiga sun sace basarake a Kogi
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun tasa keyar wani basarake zuwa cikin daji a Kogi.
'Yan bindigan sun yi awon gaba da Hakimin Bagaji Odo a karamar hukumar Omala ta jihar Kogi, David Wada, lokacin da yake kan hanyarsa ta komawa gida bayan ya samu halartar wani taro.
Rundunar 'yan sandan jihar Kogi ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda ta ba da tabbacin cewa tana ci gaba da kokarin ganin an kubutar da basaraken.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
