Saudi da Faransa za Su Kawo Karshen Isra'ila game da Shiga Gaza
- Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ya ce shi da Yariman Saudiyya, Mohammed bin Salman, za su jagoranci taron nemawa Falasdinawa yanci
- Macron mai shekaru 77 ya soki matakin Amurka na hana jami’an Falasdinu biza, yana mai cewa hakan ya sabawa dokar Majalisar Dinkin Duniya
- Ya kara da cewa babban burinsu shi ne tabbatar da mafitar kasashe biyu, Falasdinu da Isra'ila domin kawo karshen zubar da jini a Gabas ta Tsakiya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Faransa – Shugaban ƙasar Faransa, Emmanuel Macron, ya tabbatar da cewa shi da Yariman Saudiyya, Mohammed bin Salman, za su nemawa Falasdinawa 'yanci.
Hakan na zuwa ne yayin da aka shirin taron kasa da kasa da zai gudana a birnin New York a ranar 22 ga watan Satumba 2025.

Kara karanta wannan
Tinubu ya amsa kira kan kirkirar 'yan sandan jihohi, ya gano sirrin magance ta'addanci

Source: Getty Images
Macron ya fadi haka ne a shafinsa na X jim kadan bayan tattaunawa da Yariman Saudiyya, yana mai cewa taron na da matuƙar muhimmanci wajen kawo karshen rikicin Falasdinu da Isra’ila.
Ya kuma yi tsokaci kan matakin Amurka na hana jami’an Falasdinu shiga kasar domin halartar taron, wanda ya kira da “abin da bai dace ba” tare da bukatar a soke wannan mataki.
Yadda za a nemawa mutanen Gaza 'yanci
Macron ya ce babbar manufarsa ita ce samar da goyon bayan kasashen duniya wajen cimma mafitar kafa kasashe biyu; Falasdinu da Isra'ila domin kawo zaman lafiya.
Rahoton Saudi Gazette ya nuna cewa ya ce dole ne a dakatar da yaki, a sako dukkan fursunoni da ake tsare da su kuma a kai kayan agaji da jin kai Gaza da kafa rundunar tabbatar da zaman lafiya.
Shugaban Faransan ya kara da cewa za a tabbatar da cewa Hamas ba ta kasance cikin gwamnati ba bayan an cimma matsayar, tare da inganta hukumar Falasdinu da sake gina Gaza gaba ɗaya.

Kara karanta wannan
Fadar shugaban kasa ta bayyana dalilin baiwa jihar Legas fifiko wajen ayyukan raya kasa
Matsayar Emmanuel Macron kan rikicin Gaza
Macron ya ce babu wani yunkuri na mamaya ko tilasta ƙaura da zai iya rushe shirin da aka fara tare da Yariman Saudiyya, wanda ya ce wasu ƙasashen duniya sun riga sun nuna goyon bayansu.
Ya ce taron da za a yi a New York zai kasance babbar dama wajen tabbatar da burin kafa kasashe biyu a yankin domin kawo zaman lafiya da tsaro a yankin Gabas ta Tsakiya.

Source: Twitter
Gaza: Falasdin ta samu goyon bayan kasashe
Sanarwar Macron ta zo ne a daidai lokacin da ake kara nuna damuwa kan matsanancin yanayin mutanen Gaza, wanda ya ta’azzara sakamakon hare-haren Isra’ila a yankin.
Yana cikin shugabannin kasashen Yamma da suka bayyana cewa za su amince da kafa kasar Falasdinu, abin da za a kammala a taron Majalisar Dinkin Duniya a Satumba.
Shugabanni daga Austrilia, Kanada, Portugal da Birtaniya sun bayyana shirin amincewa da Falasdinu.
Trump yana son sauya fasalin Gaza

Kara karanta wannan
'Ko a jiki na': Tinubu ya yi martani mai zafi kan harajin Trump ga Najeriya, ya samo mafita
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban Amurka, Donald Trump ya fara maganar korar Falasdinawa daga zirin Gaza.
Donald Trump ya bayyana cewa yana son a mayar da Falasdinawa zuwa wasu kasashen da za a kama musu haya.
Ya kara da cewa za a ba su kudin da zai ishe su fara rayuwa a wuraren da za su koma kafin lamuransu su daidaita.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng