NDLEA Ta Kama Kwalba 8,000 na Akuskura da Tabar Wiwi mai Yawa a Kano
- Hukumar NDLEA ta kama kwalaben akuskura 8,000 da ake zargin na dauke da miyagun kwayoyi da aka shigo da su a Kano
- Haka kuma an gano buhunan tabar wiwi guda 48 a cikin tirela daga Legas zuwa Maiduguri, yayin da ta ke kokarin shigo wa jihar
- An cafke mutum daya da ake zargi da hannu a safarar miyagun kwayoyin kuma tuni aka baza kwayoyin a dakin gwaje gwaje
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Jami’an Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA), rundunar Kano, sun kara samun nasarar kama miyagun kwayoyi masu hadari ga matasa.
Daga cikin kwayoyin da aka kama akwai kwalaben akuskura guda 8,000 da ake zargin na dauke da miyagun sinadarai da kuma bulo 48 na tabar wiwi.

Kara karanta wannan
Kano: An sake tono badakalar biliyoyi da ta shafi jami'in Abba da Gwamna yake Landan

Source: Facebook
Sanar da Sadiq Muhammad, Kakakin hukumar ya wallafa a shafin Facebook na cewa hukumar ta cafke wani 'dan shekara 37 mai suna Ali Muhammad da ake zargi da hannu a lamarin.
Hukumar NDLEA ta yi kame a Kano
Kakakin NDLEA a Kano, Sadiq Muhammad Maigatari ya shaidawa Legit cewa an gano kayan ne a kan hanyar Gadar Tamburawa, da ke titin Zaria – Kano, lokacin da aka dakatar da wata tirela mai dauke da kaya daga Legas zuwa Maiduguri.
Ya ce:
"An gano kayan ne a Gadar Tamburawa, hanyar Zaria – Kano, lokacin da aka dakatar da wata tirela mai dauke da kaya daga Legas zuwa Maiduguri. Tirelar cike take da Keke Napep, inda aka ɓoye kayan tsakanin Kekunan da kuma karkashin tirelar, inda aka gina wani rufin katako domin ɓoye su.
"Jami’an NDLEA sun gano wannan boyayyen wuri ne sakamakon jajircewa da kwazon da suka nuna."

Kara karanta wannan
Ministan Buhari ya karyata zargin kashe N100bn don samar da jirgin saman Najeriya
NDLEA za ta zurfafa bincike
NDLEA ta ce dukkanin kayan da aka kama suna hannunta domin ci gaba da bincike da kuma gwajin dakin gwaje-gwaje.

Source: Twitter
Kwamandan NDLEA Kano, ACGN A. I. Ahmad, ya bayyana godiya ga shugaban hukumar, Birgediya Janar Buba Marwa (rtd.), bisa irin goyon bayan da yake bayarwa don fatattakar kwaya.
Hukumar ta roki jama’a da su kasance cikin shiri wajen bayar da bayanai kan duk wani kaya ko harkar da ake zargin tana da alaka da miyagun kwayoyi, ta hanyar kai rahoto ofishin NDLEA mafi kusa ko kuma ga hukumomin tsaro.
Jami'an NDLEA sun kama tramadol a Kano
A baya, mun wallafa cewa Hukumar Yaki da Ta’ammali da Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA), reshen jihar Kano, ta samu nasarar cafke wani matashi mai suna Adamu Yusuf a ranar 23 ga watan Agusta, 2025.
A yayin samamen da aka yi a Kwanar Dangora, kan hanyar Zaria–Kano, jami’an NDLEA sun gano kwayoyin Tramadol guda 7,000, masu nauyin kilogram 4.1, da aka ɓoye a cikin jarkar mai.
Kakakin NDLEA, Sadiq Muhammad Maigatari, ya bayyana cewa duk da ƙoƙarin matashin na boye kayan ne domin ya kauce wa jami’an tsaro, Allah Ya baiwa jami'ansu sa'ar damke shi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng