Gwamna Bago Ya Kori Dukkan Kwamishinoni da Ya Rusa Majalisar Zartarwar Neja
- Gwamnan Jihar Neja, Umaru Mohammed Bago, ya amince da korar dukkan kwamishinoni da manyan jami’ansa a jihar daga yau Litinin
- Sai dai an ware shugaban ma’aikatan gidan gwamnati, mataimakinsa, sakataren gwamnatin jihar da manyan jami’an fadar gwamnati
- A shekarar 2023 ma gwamnan ya dauki irin wannan mataki na rushe hukumomi, kwamitoci da kuma cire masu rike da mukaman siyasa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja A yau Litinin, 1 ga watan Satumba, 2025, Gwamna Umaru Mohammed Bago na Jihar Neja ya ba da sanarwar rusa majalisar zartarwa ta jihar.
Matakin ya shafi dukkan kwamishinoni da manyan jami’an da ke rike da mukaman siyasa a jihar Neja.

Source: Facebook
Legit ta tattaro bayanai kan bayanin da gwamnan ya yi ne a cikin wani sako da hadiminsa, Balogi Ibrahim ya wallafa a Facebook.
Wannan ba shi ne karo na farko da gwamna Bago ya ɗauki irin wannan mataki ba, domin a shekarar 2023 ma ya rusa hukumomi.
Gwamna Bago ya rusa majalisar zartarwar Neja
Daily Trust ta rahoto cewa sanarwar da gwamnatin Neja ta fitar ta bayyana cewa umarnin rusa majalisar da gwamnan ya bayar ya fara aiki nan take.
An kuma umarci dukkan waɗanda abin ya shafa da su mika ragamar aiki da dukkan kayan gwamnati da ke hannunsu ga manyan daraktoci na ma’aikatunsu.
A cikin sanarwar da aka fitar, an bayyana cewa manyan jami’ai guda huɗu ne kawai suka tsira daga wannan umarni.
Sun haɗa da babban shugaban ma’aikata, mataimakinsa, sakataren gwamnatin jiha da kuma manyan jami’an ofishin fadar gwamnati.
Tarihin tsige Kwamishinonin jihar Neja
Rahoton Channels TV ya nuna cewa a 2023, gwamna Umaru Bago ya ya rusa dukkan kwamitoci, hukumomi da kuma cire dukkan masu rike da mukaman siyasa.
Wannan ya nuna cewa gwamnatinsa na ci gaba da bin tsari na sake fasalin shugabanci a duk lokacin da ya ga dama.
Matakin ya sake tabbatar da irin tunanin gwamnan wajen duba yadda ake tafiyar da gwamnati da kuma bukatar kawo sababbin fuskoki a cikin majalisar zartarwa.

Source: Twitter
Gwamna ya godewa wadanda abin ya shafa
Sanarwar ta kuma nuna godiyar gwamnan ga dukkan kwamishinoni da jami’an da aka rusa bisa gudummawar da suka bayar wajen ci gaban jihar Neja.
Gwamna Umaru Bago ya kuma musu fatan alheri a cikin sauran harkokin rayuwarsu da suka rage.
A yanzu haka dai al'ummar jihar Neja za su zuba ido wajen ganin matakin da gwamnan zai dauka na sake zabo wasu mutanen da zai yi aiki da su.
Umaru Bago ya durkusa a gaban Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa an hango gwamna Umaru Bago ya zauna a gaban shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Rahoton Legit Hausa ya gano cewa hoton ya dauki hankalin jama'ar Najeriya, musamman a kafafen sada zumunta.
Wasu daga cikin mutane sun yaba wa gwamna Bago bisa durkusawar da ya yi, yayin da wasu ke ganin hakan bai dace ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

