'Na Yi Rantsuwa da Allah,' Tinubu Ya Ce ba zai Nuna wa Wani Yanki Wariya ba
- Shugaba Bola Tinubu ya ce rantsuwar da ya yi a matsayin shugaban kasa ta shafi kowa a Najeriya, ba wani yanki kadai ba
- Ya jaddada cewa dukkan ayyukan da gwamnati ke aiwatarwa a sassa daban-daban na kasar na nufin ci gaban kasa baki daya
- Bola Tinubu ya ce babu wani dan kasa da ya fi wani daraja, kuma babu wani yanki da za a bari a baya a tafiyar mulkinsa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da aniyar sa ta ci gaba da zama shugaban kowa da kowa a Najeriya, ba tare da fifita wani yanki ko wani bangare na kasa ba.
Shugaban ya bayyana haka ne yayin da zarge zarge kan fifita jihar Legas da ya fito ke kara yawaita a Najeriya.

Source: Twitter
A wani rubutu da Bayo Onanuga ya wallafa a X a ranar Litinin, ya bayyana cewa rantsuwar da ya dauka a matsayin shugaban kasa ita ce ginshikin duk wani aiki da gwamnati ke aiwatarwa.
Tinubu ya ce tsarin mulkinsa yana kan tushen adalci da daidaito, tare da tabbatar da cewa kowane yanki na kasar ya ci gajiyar ci gaba da ayyukan raya kasa.
Tinubu na ayyuka don kowa da kowa
Shugaba Tinubu ya jaddada cewa duk wani babban aiki da ake aiwatarwa a sassan Najeriya ba na wani yanki kadai ba ne, illa na kasa baki daya.
Ya lissafa ayyuka kamar su hanyar Lagos–Calabar a Kudu, Sokoto–Badagry a Arewa, Port Harcourt–Maiduguri, da hanyar Abuja–Kaduna–Kano a matsayin shaidu kan manufarsa.
A cewarsa:
“Wadannan ba a yanki daya aka yi su ba."
Zuba jari a lantarki da kiwon lafiya
Tinubu ya kara da cewa gwamnati ta himmatu wajen zuba jari a fannin wutar lantarki da kiwon lafiya a dukkan jihohi.

Kara karanta wannan
Malaman Musulunci da Kirista sun 'karyata' ikirarin da Tinubu ya yi a Kasar Brazil
Ya kawo misali da farfado da tashar samar da wutar lantarki mai karfin 255MW a Kaduna, gyaran cibiyoyin lafiya da kuma aikin layin dogo na zamani a Lagos, Ogun, Kano da Kaduna.
Haka kuma ya ce ana gina muhimman gadar ruwa a Onitsha da Bonny, tare da fadada aikin hako mai a jihohin Bauchi da Gombe.

Source: Facebook
Shugaban ya kuma ambaci ci gaban da ake samu a aikin bututun gas na Ajaokuta–Kaduna–Kano (AKK), yana mai cewa wadannan ayyuka suna tabbatar ana yi wa kowa adalci.
Tinubu ya ce za a tafi da kowa
Tinubu ya bayyana cewa manufarsa ita ce tabbatar da cewa babu dan kasa da aka bari a baya a Najeriya, kuma babu wani yanki da za a bari a baya.
Leadership ta rahoto ya ce:
“Babu wani 'dan Najeriya da ya fi wani. Babu wani yanki da za a bar shi a baya. Tare za mu tashi a matsayin kasa daya, jama’a daya, da makoma daya.”
Malamai sun karyata ikirarin Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa wasu malaman addinin Musulunci da Kirista a Najeriya sun ce har yanzu akwai rashawa a kasar.

Kara karanta wannan
Tinubu ya fadi gaskiyar abin da ke kai shi kasashen waje bayan dawowa daga Brazil
Hakan na zuwa ne bayan shugaba Tinubu ya bayyana cewa ya kammala yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya a kasar Brazil.
Daya daga cikin malaman ya bayyana wa manema labarai cewa maganar da shugaban ya yi ma alama ce ta cewa akwai rashawa har yanzu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
