El Rufai Ya Nuna Yatsa ga Uba Sani bayan 'Yan Daba Sun Tarwatsa Taron ADC a Kaduna
- Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi magana kan tarwatsa taron jam'iyyar SDP da 'yan daba suka yi
- El-Rufai ya karyata zargin cewa shi da kansa ne ya jawo aka samu barkewar rikici a wajen taron na ADC
- Tsohon gwamnan ya nuna cewa gwamnati ce ta dauki nauyin 'yan daba, kuma ya shirya daukar mataki a kan lamarin
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kaduna - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya zargi gwamnatin gwamna Uba Sani da ɗaukar nauyin 'yan daba don tarwatsa taron jam'iyyar ADC.
Ana zargin dai wasu ‘yan daba da kai hari wajen taron jam’iyyar ADC a Kaduna a ranar Asabar.

Source: Twitter
El-Rufai ya yi zargin ne lokacin da yake magana a shirin 'Sunday Politics' na Channels Tv a ranar Lahadi, 31 ga watan Agustan 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan daba sun tarwatsa taron ADC a Kaduna
A ranar Asabar, wasu da ake zargi da ‘yan daba ne, sun afka wajen taron ADC a Kaduna, inda suka kai wa mahalarta hari tare da lalata kayayyaki.
An ce ‘yan daban sun yi amfani da adduna, sanduna, da duwatsu, inda suka jikkata mutane da dama tare da lalata motoci.
Wasu daga cikin hotuna da bidiyoyin da aka yada sun nuna yadda jama'a da dama suka jikkata sakamakon harin.
El-Rufai ya musanta hannu a dauko 'yan daba
El-Rufai ya karyata zargin cewa shi ne ya shirya rikicin.
“Wauta ce babba ga duk wanda zai yi tunanin cewa zan kira ‘yan daba su kai hari wajen taron jam’iyyata.”
- Nasir El- Rufai
Tsohon gwamnan ya kuma yi ikirarin cewa ’yan sanda da ke bakin aiki sun ba ‘yan daban kariya lokacin da suke yin barna.
"Yan sanda suna wurin, ban san abin da suke bincike yanzu ba. Sun san abin da ya faru, sun ba da kariya ga ‘yan daban domin su aikata abin da suka aikata."
"Don haka, gwamnati ce ta dauki ‘yan daban. Mun san su, mun san ‘yan sandan da suka kasance a wurin."
- Nasir El-Rufai

Source: Twitter
Malam El-Rufai ya zargi gwamnatin Uba Sani
El-Rufai ya zargi gwamnatin jihar Kaduna da laifin daukar nauyin rikicin.
Tsohon gwamnan na Kaduna ya kuma bayyana cewa zai shigar da kara a gaban shugaban ’yan sanda na kasa kan lamarin.
"Gwamnatin jihar Kaduna ce ta dauki nauyin lamarin. Zan gabatar da hujjoji na ga hukumar kula da ’yan sanda da kuma shugaban ’yan sanda na kasa, idan suna son ɗaukar mataki."
- Nasir El-Rufai
El-Rufai ya yi zargi kan gwamnatin Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da daurewa 'yan bindiga gindi.
El-Rufai ya bayyana cewa gwamnatin tarayya tana biyan 'yan bindiga kudade wanda hakan ke sanyawa suna kara sayan muggan makamai don aikata ta'addanci.
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa suna da hujjojin da za su tabbatar da zargin da suke yi a kan gwamnatin tarayya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

