Najeriya Ta Yi Rashi: Tsohon Babban Sufeta Janar na Ƴan Sandan Ƙasar Ya Rasu

Najeriya Ta Yi Rashi: Tsohon Babban Sufeta Janar na Ƴan Sandan Ƙasar Ya Rasu

  • Rundunar ƴan sanda ta Najeriya ta tabbatar da rasuwar tsohon Sufeto Janar na hukumar a yau Lahadi
  • An tabbatar da mutuwar, Solomon Ehigiator Arase, wanda ya rasu a Asibitin Cedarcrest da ke birnin Abuja a Najeriya
  • An ce Arase ya rasu yana da shekara 69, inda babban Sufeta janar, Kayode Egbetokun ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Rundunar yan sanda a Najeriya ta yi babban rashin tsohon Sufeta Janar na hukumar a Najeriya.

Rundunar ta tabbatar da rasuwar Solomon Ehigiator Arase, wanda shi ne Sufeto Janar na 18 a Najeriya.

Tsohon sufeta janar na yan sanda ya mutu
Tsohon sufeta janar na yan sanda, Solomon Arase ya bar duniya. Hoto: Nigeria Police Force.
Source: Twitter

An sanar da mutuwar tsohon sufeta janar

Hakan na cikin wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafin Facebook a yau Lahadi 31 ga watan Agustan 2025.

Kara karanta wannan

Kano: Duniyar Musulmi ta yi rashi, babban malamin Musulunci ya rasu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Marigayin ya taba rike shugabancin Hukumar kula da ayyukan yan sanda a Najeriya.

Arase ya rasu ne a yau Lahadi a Asibitin Cedarcrest na birnin Abuja bayan wata gajeriyar rashin lafiya.

An bayyana cewa marigayin ya bar duniya yana da shekara 69 inda ya bar mata da yara.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, DCP Olumuyiwa Adejobi, ya ce:

“Sufeta Janar na yan sanda, Kayode Egbetokun ya samu labarin rasuwar marigayin ta hannun ɗansa.”
Sufeta janar na yan sanda ya yi ta'aziyya
Babban sufeta janar na yan sanda a Najeriya, Kayode Egbetokun. Hoto: Nigeria Police Force.
Source: Twitter

Egbetokun ya ziyarci iyalan marigayi, Arase

Kayode Egbetokun ya kai ziyara ta’aziyya ga iyalan marigayin a Abuja, inda ya mika sakon jaje a madadin rundunar da kuma bayyana gudummuwarsa.

An haifi Arase a 21 ga Yuni 1956 a karamar hukumar Owan ta Yamma da ke jihar Edo a Kudu maso Kudancin Najeriya.

Ya yi digirin dinsa a bangaren siyasa da kuma shari’a, da digirin digirgir a sashen Shari'a.

Kara karanta wannan

An harbe tsohon shugaban majalisar tarayya har lahira, shugaban ƙasa ya girgiza a Ukraine

Ya shiga rundunar ƴan sanda a 1 ga Disamba 1981, inda ya yi aiki a matsayin kwamishina a Akwa Ibom, AIG na FIB, da DIG na CID.

Yaushe marigayin ya yi ritaya?

Arase ya zama Sufeto Janar a watan Afrilu 2015, inda ya yi ritaya a ranar 21 ga Yuni 2016 bayan hidima mai cike da sauye-sauye.

Sanarwar ta ce:

“A lokacin jagorancinsa, ya kafa sashen korafe-korafe don kare haƙƙin jama’a da tabbatar da amsa kiran gaggawa.
“Arase ya nuna ƙwarewa, jarumta, da jagoranci, yayin da gudunmawarsa wajen tsaro da gyaran rundunar ke ci gaba da tasiri har yanzu.”
“Ta hanyar Gidauniyar Solomon Ehigiator Arase, ya tallafa da guraben karatu ga ɗaliban Najeriya musamman ’ya’yan jami’an da suka mutu da marasa galihu.”

Yayin ziyarar ta’aziyya, Egbetokun ya ce wannan babban rashi ne ga rundunar, yana yabawa da jarumta da ƙwarewar jagoranci na tsohon IGP.

Tsohon mataimakin sufetan yan sanda ya rasu

Kun ji cewa Allah ya karbi ran tsohon mataimakin sufetan ƴan sanda (AIG), Emmanuel Adebola Longe.

Shugaban kungiyar lauyoyi reshen Oyo, Ibrahim Lawal ya tabbatar da rasuwar tsohon AIG a wata sanarwa.

Marigayin dai ya yi abubuwan da zai wahala a manta da shi a rundunar ƴan sanda, ya shafe sama da shekara 30 a bakin aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.