Kano: Duniyar Musulmi Ta Yi Rashi, Babban Malamin Musulunci Ya Rasu

Kano: Duniyar Musulmi Ta Yi Rashi, Babban Malamin Musulunci Ya Rasu

  • Jihar Kano ta yi rashin malamin Musulunci, Sheikh Manzo Arzai, a yau Lahadi 31 ga Agusta, 2025 da muke ciki
  • Imam Muhammad Nur Muhammad Arzai ya sanar da lokacin jana’izar, inda ya ce za a yi sallar gawar marigayin da misalin karfe 2:30 na rana
  • Jana’izar za ta gudana a Zawiyar Sheikh Manzo Arzai da ke Unguwar Arzai a Kano, inda aka yi addu’ar Allah ya gafarta masa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Rahotannin da muke samu sun tabbatar da cewa an sanar da rasuwar babban malamin Musulunci a Kano.

Majiyoyi suka ce marigayin, Sheikh Manzo Arzai ya rasu a yau Lahadi 31 ga watan Agustan 2025 da muke ciki.

Malamin Musulunci ya rasu a Kano
Sheikh Manzo Arzai kenan kafin rasuwarsa a jihar Kano. Hoto: Mustapha Arzai.
Source: Facebook

Babban Malamin Musulunci ya rasu a Kano

Rahoton Aminiya ya tabbatar da haka a yau Lahadi 31 ga watan Agustan 2025 inda aka sanya lokacin gudanar da sallar jana'izar marigayin.

Kara karanta wannan

Siyasar Sanatan APC da ministan Tinubu na fuskantar matsala, an bukaci su ja baya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin wata sanarwa da na kusa da marigayin ya fitar, Imam Muhammmad Nur Muhammad Arzai, ya fadi lokacin sallar jana'iza.

Ya ce za a yi sallar jana'iza a yau Lahadi 31 ga watan Agustan 2025 da misalin karfe 2:30 na rana.

Sanarwar ta ce:

"Za a yi jana’izar fitaccen Malamin addinin Musuluncin nan Khalifan Sheikh Manzo Arzai Khalifa Muktar (Alaramma) Sheikh Manzo Arzai, a yau Lahadi.
"Za a gudanar da sallar jana'izar da misalin ƙarfe 2:30 na rana, a Zawiyar Sheikh Manzo Arzai, da ke Unguwar Arzai a Kano."

Daga karshe, ya yi addu'ar Ubangiji ya gafarta masa ya kuma saka masa da gidan aljanna Firdausi.

An yi rashin malamin Musulunci a Kano
Taswirar jihar Kano da ke Arewa maso Yamma a Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Kano: Daya daga yaran marigayin ya magantu

Daya daga cikin yaran marigayin ya tabbatar da rasuwar inda ya yi masa addu'ar neman gafara da samun rahama a lahira.

Mustapha Arzai ya bayyana sakon rasuwar a shafin Facebook inda ya bukaci addu'o'i daga al'umma da yan uwa da abokan arziki.

Kara karanta wannan

Allahu Akbar: Babbar mota ta murkushe Musulmi yana sauri zuwa masallacin Juma'a, an yi rikici

Mustapha Arzai ya ce:

"Inna Lillahi wa inna ilaihi rajiun.
"Allah ya yi wa babanmu Malam Muktari rasuwa khalifan Sheikh Manzo Arzai.
Muna tawassuli da Shugaba S.A.W A Allah ya sada shi da Shugaba S.A.W., mu na yiwa yan uwa ta'aziyya Allah ya gafarta masa, Amin."

Mutane da dama sun yi jimamin rasuwar malamin inda suke yabon halayensa da cewa za su yi rashin mutumin kirki.

A yanzu haka, an fara shirye-shiryen sallar jana'izarsa da aka shirya da misalin karfe 2:30 na rana da ake tsammanin manyan mutane za su halarta.

Malamin Musulunci ya riga mu gidan gaskiya

A baya, mun ba ku labarin cewa duniyar Musulunci ta yi babban rashi na fitaccen malamin addini wanda ya rasu a ranar Lahadi da ta wuce a Gombe da ke Arewa maso Gabas.

Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya bayyana jimami kan rasuwar babban malami Sheikh Umar Bojude, babban limamin masallacin AG Dalibi a Gombe.

Ya ce Sheikh Bojude ya rayu cikin ibada da jagoranci na addini, inda ya zama ginshiƙi ga darikar Tijjaniyya da al’umma baki ɗaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.