Babbar Magana: Gwamnonin Arewa Sun Hango Masifa a 2026, Sun Roki Tinubu

Babbar Magana: Gwamnonin Arewa Sun Hango Masifa a 2026, Sun Roki Tinubu

  • Gwamnonin Arewa maso Gabas sun fito sun yi gargadi na musamman game da abin da zai faru a Najeriya a 2026
  • Gwamnonin sun bayyana cewa za a samu tsadar kayan noma da zai iya haddasa ƙarancin abinci a shekarar 2026 da ke tafe
  • Sun roƙi gwamnati ta kara tallafin manoma da kuma fadada shirin noma na damina da rani domin kauce wa matsalolin abinci

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Jaingo, Taraba - Gwamnonin Arewa maso Gabas (NEGF) sun nuna damuwa kan abin da ka iya faruwa a shekarar 2026.

Gwamnoni sun yi fargabar za a samu tsadar kayan aikin noma da ke ƙaruwa a ƙasar nan a cewar sanarwar da suka fitar.

Gwamnonin Arewa sun fadi barazanar da ke tunkarar Najeriya a 2026
Gwamnonin Arewa maso Gabas a taron da suka yi a Jalingo. Hoto: Isma'ila Uba Misilli.
Source: Facebook

Gwamnonin Arewa sun tattauna kan matsalolin yankinsu

Sun bayyana hakan ne a ranar Asabar a bayan taron su na 12 da aka gudanar a Jalingo, jihar Taraba da mai masaukin baki, Gwamna Agbu Kefas ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Jerin ayyukan Naira tiriliyan 3.9 da aka amince a yi a Lagos a shekara 2 na Tinubu

Yayin taron, gwamnonin yankin sun tattauna matsalolin Arewa maso Gabas da yadda za a shawo kan matsalolin.

Sanarwar, wadda gwamna Babagana Zulum na Borno kuma shugaban kungiyar ya sanya hannu, ta ce tsadar kayan noma na iya haddasa ƙarancin abinci.

Mafita kan barazanar karancin abinci a Arewa

Kungiyar ta ce za a iya rage matsalar karancin abinci ne idan aka kara tallafin manoma tare da ƙara shirin noma na damina da rani.

Sanarwar ta ce:

"Kungiyar ta yaba da nasarorin yaki da ta'addanci a yankin, amma tana bakin cikin cewa har yanzu akwai matsalolin jin kai da gina abubuwa."
Gwamnonin Arewa sun yi gargadi kan yunwa a 2026
Gwamnonin Arewa maso Gabas a birnin Jalingo na Taraba. Hoto: Isma'ila Uba Misilli.
Source: Facebook

Gwamnonin sun yi gargadi kan ambaliyar ruwa

Gwamnonin sun kuma nuna damuwa game da yiwuwar ambaliyar ruwa a yankin, bisa hasashen da cibiyoyin kula da yanayi suka fitar na baya-bayan nan.

Sun bukaci a ƙara wayar da kai ga jama'a da ke zaune kusa da koguna tare da ɗaukar matakai na gaggawa domin rage illolin bala'i.

Kara karanta wannan

Rigimar shugabanci a ADC ta gawurta, yankin Atiku sun jawo rikici ya dawo danye

Kungiyar ta roƙi gwamnatin tarayya da Hukumar Cigaban Arewa maso Gabas (NEDC) su fifita gyaran gadojin da rikici da ambaliya suka lalata.

Za a gudanar da baje kolin kasuwanci a Arewa

Gwamnonin sun ce kungiyar ta yanke shawarar gudanar da baje kolin kasuwanci na Arewa maso Gabas a Maiduguri, Borno, a watan Disamba 2025.

Dangane da makamashi, sun umurci kwamitinsu ya tsara shirin samar da makamashin yankin, inda suka nuna hasken rana a matsayin hanya mafi sauki.

Kungiyar ta kunshi gwamnonin jihohin Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba da kuma Yobe waɗanda ke hada kai wajen fuskantar matsalolin yankin.

Buhari: Gwamnonin Arewa sun ba da hutu

Mun ba ku labarin cewa kungiyar gwamnonin Arewa maso Yamma ta ba da hutun kwana guda a jihohin yankin bakwai domin girmama Muhammadu Buhari.

A wata sanarwa da shugaban ƙungiyar kuma gwamnan Katsina ya fitar, ta ce rasuwar Buhari babban rashi ne ga ƙasa baki ɗaya duba da irin gudunmawar da ya bayar.

Tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya rasu ne bayan jinyar makonni a wani asibiti a birnin Landan na ƙasar Birtaniya a ranar 13 ga watan Yulin 2025.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.