Manyan Jami’an Gwamnatin Kano da ake Zargi da Rashin Gaskiya a Zamanin Abba
Kusan shekaru biyu gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta yi a Kano, amma an fara zargin hadiman gwamna da almundahana ko karkatar da kuɗin gwamnati da sauran nau'in rashin gaskiya.
Jihar Kano – An zargi wasu daga cikin hadiman gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano da almundahana iri-iri da ya shafi batun tallafin shinkafa da aka raba wa jama’a a baya.
Wasu kuma ana zarginsu da hannu a karbo belin fitaccen dilan ƙwaya, Suleiman Ɗanwawu, wasu kuma ana zarginsu da karkatar da makudan kuɗi daga asusun gwamnati.

Source: Facebook
Duk da haka, gwamnatin Kano ta bayyana cewa tana bin doka wajen hukunta duk wanda aka samu da laifi, kana kuma tana kallon wasu daga cikin zarge-zargen a matsayin shirin kawar da martabar gwamnati.
Legit ta tattaro jerin manyan jami'an gwamnatin Abba Kabir Yusuf da aka yi wa zargin almundahana da matakan da aka dauka a kansu.
1. An zargi hadimin Abba kan karkatar da shinkafa
Daya daga cikin manyan badakalar da ta girgiza gwamnatin Kano shi ne na Tasiu Adamu Al’amin Roba, tsohon Mai Ba da Shawara na Musamman (SSA).
Channels TV ta wallafa cewa kwamitin bincike ya gano cewa Tasi'u yana da hannu a sake buhunan tallafin shinkafa da aka ajiye a wani rumbu a Sharada.
Ana zarginsa da haɗa hannu wajen sauya wa shinkafar buhu tare da karkatar da su zuwa kasuwanni.

Source: Facebook
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce wannan ya sabawa manufar gwamnati wacce ta ware shinkafar domin marasa galihu.
Bayan gano hakan, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tsige shi daga mukami, tare da ba shi umarnin mika dukkanin kayan gwamnati da ke hannunsa.
Haka kuma an gurfanar da shi a kotu bisa laifin sata da haɗa baki da aikata laifi.
2. An zargi Kwamishinan Abba da belin Ɗanwawu
Wani al’amari da ya tayar da kura shi ne na Ibrahim Namadi, tsohon Kwamishinan Sufuri na jihar Kano.
Rahoton kwamitin bincike ya tabbatar da ya yi nazari a kan zargin Namadi da tsaya wa wani da ake zargi da dilan ƙwayoyi ne, Sulaiman Aminu Danwawu, a kotu.

Source: Facebook
Wannan mataki ya jawo cece-kuce a Kano, musamman ganin irin tasirin matsalar miyagun ƙwayoyi a jihar da faɗan daba.
Biyo bayan matsin lamba daga jama’a da rahoton kwamitin, Namadi ya ayi murabus daga mukaminsa.
Hadimin gwamna, Sanusi Bature D-Tofa ya wallafa a Facebook cewa hakan ya zama babbar hujja cewa gwamnatin Abba tana kokarin kawo ƙarshen abin da zai hargitsa Kano.
3. Abba ya kori hadiminsa saboda Ɗanwawu
Haka zalika, rahoton kwamitin bincike da gwamnatin Kano ta kafa ya bayyana sunan Abubakar Umar Sharada, tsohon SSA kan Siyasa, a matsayin wanda ya jagoranci shirya belin Suleiman Danwawu
Shaidun da aka tattara sun nuna cewa Abubakar shi ne ya yi tsayin daka wajen ganin an saki wanda ake zargin, abin da ya saba da manufar gwamnati wajen yaki da miyagun ƙwayoyi.

Source: Facebook
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tsige shi daga mukami a ranar 9 ga watan Agusta, 2025, tare da bayyana cewa gwamnatin sa ba za ta lamunci wani jami’i da zai ci amanar al’umma ba. 4. An zargi hadimin Abba ya karkatar da N60.5bn Wata babbar magana da ta sake tayar da kura ita ce zargin da aka yi wa Abdullahi Ibrahim Rogo, Daraktan Harkokin Fadar Gwamnatin Kano.
Wani rahoto ya bayyana cewa Rogo ya karkatar da Naira biliyan 6.5 ta hanyar amfani da kamfanoni da ‘yan canji.

Source: Facebook
Rahotan ya ci gaba da cewa tuni ya mayar da wani kaso na kuɗin ga asusun ICPC, duk da dai gwamnatin Kano ta ƙaryata zancen.
Sai dai gwamnatin Kano ce ofishin Rogo na kashe kuɗin da aka ware wa bangarensa ne kawai, kuma a bisa ka'ida.
Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta jaddada cewa duk wani jami’in da aka samu da laifi zai fuskanci hukunci, domin gwamnatin ta sa a gaba manufar tsabtace gwamnati daga cin hanci da rashawa.
Amma ta yi gargaɗin cewa ba za ta lamunci a rika cin zarafinta ko na hadimanta da ke aiki tukuru ba.'
Hadimin Abba ya maka ɗan jarida a kotu
A wani labarin, kun ji cewa Wata Kotun Majistare ta 15 a Kano, karkashin jagorancin Alkalin Malam Abdulaziz M. Habib, ta fara saurarar koken Abdullahi Ibrahim Rogo.
Kotun ta bayar ada umarnin gudanar da cikakken bincike kan zarge-zargen da jaridar Daily Nigerian ta wallafa inda ta ce Rogo na da hannu a Karkara da N6.8bn.
Rogo ya ce wallafe-wallafen da aka buga a ranakun 22 da 25 ga Agusta, 2025 sun bata masa suna, inda aka kira shi “ɓarawon hadimin gwamna," kuma yana so a bi masa hakkinsa.
Asali: Legit.ng


