Kamfanin Teckopi Ya ba Matasa 20 Horo kan Adabi da Zane a Jihar Gombe

Kamfanin Teckopi Ya ba Matasa 20 Horo kan Adabi da Zane a Jihar Gombe

  • An gudanar da horo na musamman na kwana biyu a Gombe domin inganta basirar matasa a sha’anin zane da adabi
  • Taron ya samu halartar mutum 20 da aka zaɓa bisa jajircewa da himmar da suka nuna a adabin Turanci da zane
  • An gudanar da shi ne karkashin Tectopi bisa jagorancin Usman Usman da hadin gwiwar cibiyar Amurka ta USIDHR

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe – An kammala wani shiri na musamman a jihar Gombe, wanda ya mayar da hankali wajen horar da matasa masu tasowa a fagen adabi da zane.

Shirin da ya gudana a tsawon kwana biyu, ya samu halartar mutum 20 da aka zaɓa bisa jajircewa da sha’awar kawo cigaba da suka nuna.

Wasu daga cikin wadanda suka halarci shirin a jihar Gombe
Wasu daga cikin wadanda suka halarci shirin a jihar Gombe. Hoto: Usman Usman
Source: Facebook

Wacce ta jagoranci shirin, Aisha Muhammad Lamido ta bayyanawa Legit Hausa cewa an shirya shi ne domin ba wa matasan damar fahimtar yadda za su habaka basirar da Allah ya ba su.

Kara karanta wannan

Malaman Musulunci da Kirista sun 'karyata' ikirarin da Tinubu ya yi a Kasar Brazil

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda shirin ya gudana a jihar Gombe

Shirin ya gudana ne karkashin Tectopi Nigeria bisa jagorancin shugaban ta, Usman Usman, tare da haɗin gwiwar cibiyar USIDHR ta Amurka.

An bayyana cewa babbar manufar taron ita ce kawo karshen tsohuwar al’adar da ke takaita basirar matasan Gombe a cikin gida kawai.

A cewar masu shirya taron, ana son tabbatar da cewa matasan jihar Gombe sun yi kafada-da-kafada da takwarorinsu na fadin duniya.

Me Tectopi ya koya wa matasan?

Matasan da suka halarci shirin sun amfana da darusa da dama da aka tsara musamman domin inganta fasahar su a fannin adabin Turanci da zane.

Daga cikin batutuwan da aka tattauna sun haɗa da koyar da yadda mutum zai samu cigaba wajen bunkasa basirar da Allah ya ba shi.

Baya ga haka, an karantar da mahalarta shirin fahimtar matsayinsu na masu fasaha a cikin al'umma da yadda hakan zai kara karfafa musu gwiwa.

Kara karanta wannan

Jerin ayyukan Naira tiriliyan 3.9 da aka amince a yi a Lagos a shekara 2 na Tinubu

Daga cikin abubuwan da aka koyar akwai nuna musu yadda za su iya tallata basirar adabi da zane da suke da ita a duniya a matsayin haja da za ta amfanar da su da al'umma baki daya.

An gayyato kwararru daga fannoni daban-daban domin bayar da horon, ciki har da, Malam Muhammad Isa Gaude, Aliyu Danladi, Adamu Usman Garko da Hassana Absolon.

Daya daga cikin wadanda suka horas da matasan, Muhammad Isa Gaude
Daya daga cikin wadanda suka horas da matasan, Muhammad Isa Gaude. Hoto: Usman Usman
Source: Facebook

Tasirin horon ga matasan jihar Gombe

Rahotanni sun nuna cewa matasan da aka horar sun nuna jajircewa da sha’awa duk da tsawon lokacin da aka dauka ana gudanar da shirin.

Sun bayyana cewa shirin ya ba su damar koyon sababbin dabarun da za su iya sauya fasahar su zuwa sana’a mai tasiri.

Aishatu Lamido ta bayyana cewa nasarar shirin ta samu ne saboda haɗin kai tsakanin masu shirya shi da kuma jajircewar mahalarta.

Masu shirya taron sun bayyana cewa burinsu shi ne ganin matasan da suka horar sun yi tasiri a matakin ƙasa da ƙasa.

Za a horas da matasa miliyan 1.5

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Kano karkashin Abba Kabir Yusuf ta shirya horas da matasa milliyan 1.5.

Kara karanta wannan

Babu zama: Kwankwaso ya dura Legas bayan ruguza kasuwar Hausawa

Shirin zai mayar da hankali ne wajen koyar da matasan jihar sana'o'in da ke da alaka da fasahar zamani.

Rahoton da Legit Hausa ta samu ya nuna cewa burin gwamnatin Kano shi ne koyawa matasan sana'o'i domin rage zaman banza.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng