Ana Fargabar Zanga Zanga kan Cire Sarkin da Ya Yi Abin Kunya a Amurka

Ana Fargabar Zanga Zanga kan Cire Sarkin da Ya Yi Abin Kunya a Amurka

  • Wata kotun Amurka ta daure Oba Joseph Oloyede, Sarkin Ipetumodu, shekaru hudu da 'yan watanni saboda zamba
  • Hukuncin ya tayar da rikicin gadon sarauta a tsakanin gidajen sarauta biyu na Aribile da Fagbemokun
  • Gwamnatin Osun ta ce za ta dauki mataki ne bayan ta samu takardar hukuncin kotun (CTC) daga Amurka

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Osun - An shiga dar-dar a garin Ipetumodu na karamar hukumar Ife ta Arewa a jihar Osun bayan da wata kotun Amurka ta daure sarkin garin, Oba Joseph Oloyede.

Legit ta rahoto cewa an daure sarkin ne bisa laifin zamba da ya shafi makudan kudin tallafin COVID-19.

Sarkin Osun da aka kama a Amurka, Oba Joseph Oloyede
Sarkin Osun da aka kama a Amurka, Oba Joseph Oloyede. Hoto: Osun Defenders
Source: Twitter

The Nation ta rahoto cewa Oba Oloyede da ke da takardun zama dan kasa a Najeriya da Amurka ya sha daurin shekaru hudu da watanni a gidan yari.

Kara karanta wannan

Abubuwa sun dauki zafi, an fara yunkurin tsige Sarki mai martaba a Najeriya

Tun bayan hukuncin, sarautar ta fada cikin rikici yayin da ‘ya’yan gidan sarauta na Aribile da Fagbemokun suka shiga fafutukar neman kujerar mulkin gargajiya.

Rawar da masu nada Sarki ke takawa

Masu nadin sarauta a karkashin jagorancin Asalu na Ipetumodu, Cif Sunday Afolabi, sun fara zama kan makomar kujerar.

Punch ta wallafa cewa gwamnatin jihar ta bayyana cewa ba za ta dauki mataki ba sai bayan samun kwafin hukuncin kotun Amurka (CTC).

Wasu daga cikin ‘yan takarar da ke neman kujera sun fara shirin shigar da korafi ga gwamnati domin hanzarta tsarin nada sabon sarki.

Duk da haka, an ce gwamnatin jihar na bin matakai ne don kaucewa matsaloli da sabani a nan gaba.

Ra’ayoyin al’umma da fushin masu sarauta

Wasu fitattun ‘yan gidan sarautar yankin sun bayyana rashin jin dadinsu matuka da abin da ya faru.

Yarima Taiwo Ayoola daga gidan Aribile ya ce abin da ya faru abin kunya ne da bai taba shiga tarihin garin ba.

Kara karanta wannan

China ta ba da tallafin ambaliya, za a raba Naira biliyan 1.5 a jihohin Arewa

Taiwo Ayoola ya bayyana cewa sarkin da aka samu da laifi dumu dumu ba shi da ikon ci gaba da zama a matsayin.

Ya kara da cewa al’ummar Ipetumodu suna cikin bakin ciki da kunya sakamakon hukuncin da aka yanke a Amurka, inda makwabta ke yi musu dariya da habaici.

Gwamnan Osun yayin da ya ke zaune a ofishinsa
Gwamnan Osun yayin da ya ke zaune a ofishinsa. Hoto: Osun State Government
Source: Instagram

Nada Sarki: Ana fargabar zanga zanga

Yanzu haka, ana ci gaba da tarurruka tsakanin masu rike da mukaman gargajiya da shugabannin al’umma, yayin da ake jiran hukuncin gwamnati.

Wasu mazauna garin sun fara shirye-shiryen gudanar da zanga-zanga don ganin an hanzarta zaben sabon sarki.

A halin yanzu, garin Ipetumodu na cikin wani yanayi na rashin tabbas, inda mutanen gari ke jiran makomar sarautar su bayan gurfanar da sarkinsu a wata kasa.

INEC ta kare yawan masu rajista a Osun

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta bayyana cewa ba sabon abu ba ne a samu mafi yawan masu rajistar mallakar katin zabe a Osun.

Hakan na zuwa ne bayan kakakin jam'iyyar adawa ta ADC, Bolaji Abdullahi ne ya yi korafi a wata sanarwa da ya fitar.

Tun da farko dai hukumar INEC ta bayyana cewa jihar Osun ce ke kan gaba a rajistar mallakar katin zabe da aka fara ta yanar gizo.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng