'Yan Bindiga Sun Ga Ta Kansu yayin da Gwamnatin Katsina Ta Tashi Tsaye
- Jihar Katsina na daya daga cikin jihohin da suke fama da matsalar rashin tsaro musamman a shekaru 10 da suka wuce zuwa yau
- Gwamnatin Katsina na daukar matakai domin ganin cewa ta shawo kan matsalar wadda ta dade ta yi sanadiyyar rayuka da dukiya
- Matakai na baya-bayan nan da ta dauka sun hada da sayo kayan aiki ga jami'an tsaro domin taimaka musu a aikin da suke yi na murkushe 'yan bindiga
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Katsina - Gwamnatin jihar Katsina ta amince da sayen kayan aiki domin tunkarar matsalar 'yan bindiga.
Gwamnatin ta amince da sayen babura 700 da kuma motocin Hilux 20 a matsayin wani sabon mataki na yaki da ’yan bindiga, garkuwa da mutane da sauran miyagun ayyuka a fadin jihar.

Source: Twitter
Babban sakataren yada labaran gwamna, Ibrahima Kaulaha Mohammed, ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan
Ana hallaka jama'ansa, Gwamna Radda zai kashe Naira miliyan 680 a gyaran maƙabartu
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amincewar ta samu ne a lokacin taron majalisar zartarwar jihar, wanda Gwamna Dikko Umaru Radda ya jagoranta a gidan gwamnati, da ke Katsina.
Meyasa gwamnatin Katsina za ta sayo kayan aiki?
Kwamishinan harkokin tsaron cikin gida na jihar, Dr. Nasiru Mu’azu Danmusa, ya ce an dauki wannan mataki ne sakamakon yanayin kasar jihar, wadda ke da wahalar shiga ga motoci domin zuwa wasu yankunan da ke cikin hadari.
"Gwamnati ta bayyana matsayinta a fili, tsaro shi ne na farko, na biyu da kuma na uku a jerin abubuwan da wannan gwamnati ta dauka da muhimmanci. Mun kuduri aniyar shawo kan matsalar tsaro baki ɗaya.”
- Dr. Nasiru Muazu Danmusa
Baya ga motocin, majalisar ta kuma amince da sayen kayan aikin dabarun tsaro, wadanda za su taimakawa jami'an tsaro.
Wadannan kayayyakin za su tallafa wa rundunar C-Watch tare da hadin gwiwar hukumar tsaron farin kaya (DSS) da sauran hukumomin tsaro.
Za a sayo motocin yaki da 'yan bindiga
Dr. Nasiru Muazu Danmusa ya kuma bayyana cewa majalisar ta amince da sayen motoci masu sulke kirar Toyota Land Cruiser (Buffalo) guda takwas, domin kara samun saukin tafiya da kuma samun damar shiga yankunan da ’yan bindiga ke yawan addaba.

Source: Facebook
"Wadannan matakan wani bangare ne na kokarin da ake ci gaba da yi na karfafa tsaron al’umma da kuma bai wa hukumomin tsaro kamar ’yan sanda, DSS, da Sibil Difens kayan aikin da za su taimaka musu wajen yaki da rashin tsaro yadda ya kamata.”
- Dr. Nasiru Muazu Danmusa
Ya yi kira ga jama’a da su ci gaba da goyon bayan kokarin gwamnati ta hanyar addu’a da hadin kai, yana tabbatar musu da cewa gwamnatin jihar ta kuduri aniyar dawo da zaman lafiya mai dorewa a duk fadin Katsina.
Shiri ne mai kyau
Umar Sharehu ya yaba da matakin da gwamnatin ta dauka na siyo karin kayan aiki ga jami'an tsaro.
"Gwamnati ta yi kokari wajen samar da rundunar C-Watch, domin suna taimakawa sosai wajen samar da tsaro."
"Sayo musu karin kayan aiki zai taimaka sosai a kokarin da suke yi na murkushe miyagu."
- Umar Sharehu
Gwamna Radda ya kai ziyarar ta'aziyya
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya kai ziyara kauyen Mantau bayan harin 'yan bindiga.
Gwamna Radda ya ziyarci kauyen ne domin yin ta'aziyya da kuma ganewa idonsa irin barnar da 'yan bindigan suka yi.
A yayin ziyarar, Gwamna Radda ya daukarwa mutanen kauyen alkawura domin kyautata rayuwarsu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

