Reno Omokri Ya Dauko Batu Mai Girma, Ya Ce ba a Yiwa Musulmi Adalci ba a Najeriya
- Reno Omokri ya soki tsarin aiki ranar Juma'a da kuma hutu a ranar Lahadi a Najeriya saboda bai yiwa al'ummar musulmi adalci ba
- Tsohon hadimin shugaban kasa ya ce ya kamata a canza tsarin da ake amfani da ahi yanzu, domin ba haka yake ba kafin zuwan turawan mulkin mallaka
- Omokri ya bayar da shawarar yadda za a gyara tsarin domin bai wa musulmi damar tashi daga aiki a kan lokaci a ranar Juma'a
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Tsohon hadimin shugaban kasa, Reno Omokri, ya yi kira da a sake duba tsarin lokacin aiki a Najeriya domin baiwa Musulmi damar yin ibadarsu ta ranar Juma’a.
Reno Omokri ya ce ba a yi wa al'ummar musulmin Najeriya adalci ba a tsarin da ake amfani da shi yanzu, wanda ya tanadi aiki ranar Juma'a da hutu ranar Lahadi.

Kara karanta wannan
'Na shirya rungumar zaman lafiya': Bello Turji ya dauki alkawari, ya fadi sharrin da ake yi masa

Source: Facebook
A wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Juma’a, Omokri ya bayyana cewa kafin zuwan turawan mulkin mallaka, ranar Juma’a ana daukarta a matsayin ranar hutun Musulmi.
Omokri: Ba a yiwa Musulmi adalci ba
Ya jaddada cewa yayin da Lahadi ke kasancewa ranar hutu ga Kiristoci, Musulmi kuwa ana tilasta musu yin aiki a ranar Juma’a duk da muhimmancin ranar wajen gudanar da ibadarsu.
Tsohon hadimin shugaban kasar ya bayar da shawarar cewa za a iya samun daidaito ta hanyar gyara lokacin fara aiki a kowace rana.
A cewarsa, za a iya fara aiki da wuri daga Litinin zuwa Alhamis, sannan a rufe ofisoshi da rana a ranar Juma’a.
Wannan gyara, in ji shi, ba zai rage yawan aiki ko shafar tattalin arzikin kasa ba, amma zai baiwa Musulmi damar halartar sallar Juma’a.
Ta ya za a gyara tsarin aikin Najeriya?

Kara karanta wannan
Karfin hali: Ɗan Najeriya ya maka gwamna sukutum a kotu, ya faɗi ƙuncin da ya jefa shi
“Ba na ganin an yiwa al’ummar Musulmi adalci idan har aka ci gaba da daukar Juma’a a matsayin ranar aiki a Najeriya. A asali, kafin mulkin mallaka, ba haka abin yake ba.
"Yanzu muna da Lahadi a matsayin ranar hutu, amma Juma’a kuma ranar aiki ce. Ina ganin za mu iya samun daidaito.
"Maimakon a fara aiki daga Litinin zuwa Juma’a da karfe 9:00 na safe ko 8:00, za mu iya farawa da 7:30 na safe daga Litinin zuwa Alhamis, sannan a ranar Juma’a a tashi da karfe 12:00 na rana."
- Reno Omokri.

Source: Facebook
Reno Omokri ya fadi yadda za a samu daidaito
Omokri ya bayyana cewa a wannan tsarin, za a dauko wasu awanni aikin ranar Juma'a adawo da su ranakun Litinin zuwa Alhamis.
A rahoton Tribune Nigeria, Omokri ya ci gaba da cewa:
"Lokacin da za mu rasa a Juma’a, za mu dawo da shi daga Litinin zuwa Alhamis. Don haka, tsarin ba zai rage aikin kasa ko shafi tattalin arziki ba.
"Kuma hakan zai baiwa Musulmi damar rufe ofis da karfe 12:00 don su halarci sallar Juma’a. A haka za a samu adalci da daidaito tsakanin rayuwar aiki da ibada a Najeriya.”

Kara karanta wannan
Allahu Akbar: Babbar mota ta murkushe Musulmi yana sauri zuwa masallacin Juma'a, an yi rikici
Wani ma'aikacin gwamnati musulmi, Lawal Ahmed ya shaida wa Legit Hausa cewa akwai tsarin zuwa Masallaci a kowane wurin aiki, amma damuwar dole sai ka dawo ofis.
Ya ce musulmi za su so su samu damar yin addu'o'i a wannan rana duk da dai a addinance, musulunci bai hana zuwa neman halak ranar Juma'a ba.
"Shawarar da Omokri ya bayar mai kyau ce, akalla dai idan muka tafi sallah karfe 12:00 ya zama mun tashi kenan babu dawowa ofis, hakan zai taimaka mana gaskiya," in ji shi.
Sultan ya koka kan karuwar rashin adalci
A wani rahoton, kun ji cewa Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III ya ce adalci a Najeriya ya zama na mai kuɗi yayin da talaka ke fama da kunci.
Mai alfarma Sarkin Musulmin ya ce a yanzu masu kudi ne kawai ke iya sayen adalci a kotunanan Najeriya, amma idan baka da kudu ba ka tabbacin samun adalci.
Ya nuna takaicinsa kan yadda bangaren shari'a ya lalace a kasar nan, yana mai bayyana cewa lokaci ya yi da za a kawo dauki matakan gyara.
Asali: Legit.ng