Duniya Budurwar Wawa: Fitaccen Malamin Addini Ya Bar Duniya Yana da Shekaru 89

Duniya Budurwar Wawa: Fitaccen Malamin Addini Ya Bar Duniya Yana da Shekaru 89

  • Al'ummar Kiristoci a Najeriya sun yi rashi da mutuwar fitaccen malamin coci a jihar Enugu da ke Kudu maso Gabashin Najeriya
  • Babban Fasto na Nsukka, Rabaran Francis Okobo, ya rasu yana da shekara 89 a asibitin 'Niger Foundation, Enugu' da ke jihar
  • An haifi Okobo ranar 4 ga Nuwamba, 1936, an nada shi limami a 1966, kuma ya zama babban Fasto na Nsukka a 1990

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Enugu - An shiga wani irin yanayi bayan sanar da mutuwar babban malamin addinin Kirista a Najeriya.

Babban Fasto a Nsukka, Rabaran Francis Okobo, ya riga mu gidan gaskiya bayan fama da jinya da ya yi na tsawon lokaci.

Fasto ya mutu a Enugu bayan fama da jinya
Babban Faston Nsukka, Rabaran Francis Okobo. Hoto: Nsukka Catholic Diocese.
Source: Facebook

An yi rashin babban Fasto a Najeriya

Rahoton Punch ya tabbatar da mutuwar marigayin a yau Juma'a 29 ga watan Agustan 2025 da muke ciki.

Kara karanta wannan

Yayin da Assadus Sunnah ke kiran sulhu, Hatsabibin ɗan bindiga ya kuma sakin mutane 142

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutuwar Faston ya ta da hankulan jama'a a yankin wanda ya zama jagoran addinin Kirista inda suke yabon mu'amalarsa da mutane.

Sanarwar daga sakatariyar 'Catholic of Nigeria' ta tabbatar da hakan ranar Juma’a inda ta ce ya rasu yana da shekaru 89.

An ce Okobo ya rasu ne a asibitin 'Niger Foundation' da ke Enugu, yana da shekaru 89, labari ya girgiza mabiya cocin sosai.

“Da cikakken miƙa wuya ga Allah da fatan tashin matattu, muke sanar da rasuwar Rabaran Francis Emmanuel Ogbonnia Okobo."

- Cewar sanarwar

Babban Fasto a Najeriya ya mutu a Enugu
Taswirar jihar Enugu da ke Kudu maso Gabas a Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Takaitaccen tarihin marigayi Rabaran Francis Okobo

An haifi Okobo ranar 4 ga Nuwamba, 1936, an nada shi limami ranar 4 ga Yuni, 1966, sannan ya shiga matsayin manya inda ya zama babban Fasto a 1990.

Ya karɓi nadin 'Bishop' na Nsukka ranar 6 ga Janairu, 1991, daga bisani ya yi murabus a matsayin a ranar 13 ga Afrilu, 2013.

Sanarwar ta kuma tabbatar da cewa za a bayyana lokaci da kuma bayanai kan jana’izar marigayin daga baya, Daily Post ta tabbatar.

Kara karanta wannan

Daga Kudu zuwa Arewa: Yadda matatar Dangote take sauya tattalin arzikin Najeriya

Daga bisani, sanarwar ta yi addu'o'i ga marigayin tare da rokon Ubangiji ya yi masa rahama ya yafe masa kura-kuransa da ya aikata lokacin da yake raye.

Sanarwar ta kara da cewa:

"Muna yi maka addu'ar samun rahama, Ubangiji ya kai haske kabarinka ya gafarta maka."

Al'ummar yankin da dama sun nuna jimami kan mutuwar Faston wanda suka dauke shi a matsayin shugaba kuma mutum mai haba-haba da jama'a.

Fasto ya mutu bayan zuwa otal da budurwarsa

A baya, mun ba ku labarin cewa wani faston ɗariƙar Katolika ya yi bankwana da duniya bayan ya je otal cin duniya da tsinke tare da masoyiyarsa.

Fasto Joseph Kariuki Wanjiku mai shekara 43 a duniya ya kama ɗaki ne a otal ɗin da yammacin ranar Juma'a 7 ga watan Yulin 2023.

Sai dai, faston ya mutu ne da safiyar ranar Asabar bayan ya kwashe wasu sa'o'i a otal ɗin tare da budurwarsa wanda hakan ya daga wa al'umma hankali inda suke ta mamakin lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.