'Yan Bindiga Sun kai Hari Kano da Dare, Sun Sace Mata bayan Kashe Rai
- ‘Yan bindiga sun kutsa cikin gidan wani mutum a Kano, inda suka kashe mutum daya tare da sace matansa biyu
- Wannan lamarin ya faru ne da tsakar dare, lokacin da maharan dauke da makamai suka kai farmaki cikin al’umma
- Hukumomi sun ce an fara bincike domin ceto wadanda aka sace da kuma kamo wadanda suka aikata wannan danyen aiki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - An sake samun wani mummunan hari na ‘yan bindiga a jihar Kano, wanda ya haifar da asarar rai da kuma sace mata biyu.
Lamarin ya faru ne a kauyen Kwanar Dangora da ke karamar hukumar Kiru, inda al’ummar yankin ke cikin fargaba sakamakon harin da aka kai musu.

Source: Original
Legit Hausa ta tattaro bayanai kan harin ne a cikin wani sako da Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X.

Kara karanta wannan
Ana hallaka jama'ansa, Gwamna Radda zai kashe Naira miliyan 680 a gyaran maƙabartu
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yaushe aka kai hari Kano?
Bayanan da aka samu sun tabbatar da cewa maharan sun kutsa cikin gidan wani mutum mai suna Alhaji Ibrahim da misalin karfe 12:30 na dare.
An ce su je wajen dauke da makamai masu hadari, inda suka firgita al’umma tare da yin garkuwa da matansa biyu.
An gano sunayen matan da aka sace a matsayin Safara’u Ibrahim da Altine Ibrahim, lamarin da ya bar iyali da mazauna yankin cikin tashin hankali da damuwa.

Source: Facebook
An kashe mutum 1 a harin Kano
A yayin harin, an harbi wani matashi mai suna Abdul Usman, mai shekaru 27, wanda mazauna suka bayyana shi a matsayin makwabcin gidan da aka kai harin.
Rahotanni sun tabbatar da cewa harbin da 'yan ta'addan suka masa ya yi sanadiyyar mutuwarsa nan take .
Bayanai sun nuna cewa rundunar ‘yan sanda ta ziyarci wurin da lamarin ya faru, an kuma mika gawar mamacin ga iyalansa domin gudanar da jana’iza bisa tsarin Musulunci.
Wannan kisan ya kara tayar da hankalin jama’a musamman a wannan lokaci da ake ta fuskantar matsalolin tsaro a sassa daban-daban na kasar.
Matakan hukumomi suka dauka
Rahotanni sun ce jami’an tsaro sun fara gudanar da bincike domin gano hanyar da maharan suka bi da kuma inda suka kai wadanda suka sace.
Haka kuma, an tabbatar da cewa ana gudanar da ƙoƙarin ceto matan da aka sace cikin koshin lafiya.
Hukumomi sun ce suna ɗaukar lamarin da muhimmanci, domin tabbatar da cewa irin wannan mummunan hari ba zai sake faruwa ba a yankin.
An kashe 'yan bindiga 50 a Neja
A wani rahoton, kun ji cewa dakarun sojin Najeriya sun yi nasarar kashe 'yan bindiga 50 a wata musayar wuta da suka yi a jihar Neja.
Bayanan da Legit Hausa ta samu sun bayyana cewa sojoji sun gwabza da 'yan ta'adda kimanin 300 ne a lokacin da suka nufi kai hari ofishin hukumar DSS.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa bayan kashe 'yan ta'addan, sauran 'yan bindigan da suka tsira sun dauki gawarsu bayan sun sanya su a cikin buhu.
Asali: Legit.ng
