Abubuwa Sun Dauki Zafi, An Fara Yunkurin Tsige Sarki Mai Martaba a Najeriya
- Sarkin Ipetumodu ya fara shiga matsalar da ka yi raba shi da sarauta a jihar Osun bayan hukuncin dauri da kotun Amurka ta yanke masa
- Mai martaba Sarkin zai shafe sama da shekara hudu a gidan yarin Amurka bayan kama shi da laifin cinye kudin tallafin COVID-19
- Wannan hukunci ya sa masu ruwa da tsaki a masarautar da masu zaben Sarki suka fara yunkuri tsige shi da kuma maye gurbinsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Osun - An shiga damuwa a garin Ipetumodu da ke karamar hukumar Ife ta Arewa a jihar Osun bayan yanke wa mai martaba Sarki, Oba Joseph Oloyede, hukuncin dauri a Amurka.
Oba Oloyede, wanda ke da shaidar zama dan kasa a Najeriya da Amurka, ya shiga hannu a watan Mayun 2024 kan zargin karkatar da kudin tallafin COVID-19 da ya kai Dala miliyan 4.2.

Kara karanta wannan
Tinubu ya fadi gaskiyar abin da ke kai shi kasashen waje bayan dawowa daga Brazil

Source: Twitter
Wata kotu a Ohio ƙarƙashin alkalin Amurka, Christopher A. Boyko, ta yanke masa hukuncin zaman gidan yari na watanni 56, kamar yadda Tribune Nigeria ta kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sarkin, wanda ya hau gadon sarauta a ranar 26 ga Oktoba, 2019 bayan fafatawa da yan takara 10, ya ruguza tsohuwar fada domin gina sabuwa kafin kama shi.
Abin da ya faru kafin daure Sarkin a Amurka
Bayan hukuncin, tashin hankali ya dawo tsakanin gidajen sarauta biyu, Aribile da Fagbemokun, inda ’ya’yan sarauta suka fara neman a tsige Sarkin a maye gurbinsa.
Wannan yunkuri ya ƙara karfi bayan rashin ganin Sarkin a addu’ar shekara da kungiyar kiristoci watau CAN ta shirya a garin ranar 11 ga Janairu, 2025.
Sai dai shugaban ƙungiyar raya Ipetumodu (IPU), Dr. Israel Akinjogbin, ya roƙi jama’a da su kwantar da hankali, yana mai cewa duk da Sarkin ya yi nisa, har yana ganawa ta yanar gizo da manyan fadawansa.
Yadda aka fara kokarin sauke Sarkin Ipetumodu
Wata majiya ta ce:
“Tun kafin a yanke masa hukunci a Amurka, mun yi ta tuntubar gwamnatin jihar Osun kan matakin da ya kamata a dauka amma babu amsa.
"Yanzun mun sake bin sawu, sai kwamishinan kananan hukumomi da harkokin masarauta, Dosu Babatunde, ya fada mana gwamnati za ta ɗauki mataki bayan ta samu takardar hukuncin kotun Amurka (CTC).
"Ana sa ran wasu masu neman sarautar za su shigar da ƙorafi ga gwamnati tare da takardun CTC don hanzarta tsarin naɗa sabon Sarki.”

Source: Twitter
Masu zaben Sarki sun fara kiran taruka
Haka kuma wata majiya mai tushe ta ce sarakuna da manyan unguwanni a karkashin jagorancin Asalu na Ipetumodu, Sunday Afolabi, wanda shi ne shugaban masu nada Sarki, sun riga sun fara zama kan lamarin.
Duk kokarin jin ta bakin shugaban masu zaben Sarki, Cif Afolabi, ya ci tura, domin bai ɗaga waya ko ya amsa sakon da aka tura masa ba.

Kara karanta wannan
Baltasar: Kotu ta hukunta jami'in gwamnatin da bidiyoyin lalatarsa da mata suka yadu
Gwamna na duba yiwuwar tsige Sarki
A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya fara tunanin tsige Mai Martaba Sarkin Ipetumodu, Oba Joseph Oloyede.
Hakan dai ya biyo bayan kama shi da laifin karkatar da kudin COVID-19 da kuma hukuncin da kotun Amurka ta yanke masa.
Rahotanni sun nuna cewa matukar ba a samu wani sauyi daga baya ba, Gwamna Adeleke zai tube wa Sarkin rawani sakamakon laifin da ya aikata.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
