An Ware Filin Kafa Cibiyar Kera Kayan Gini a Legas, Kano da Gombe za Su Biyo Baya
- Gwamnatin Tarayya ta samu hekta 200 a Lekki da ke jihar Legas domin gina cibiyar kayan gine-gine da nufin rage farashin gina gidaje
- Ministan gidaje, Ahmed Dangiwa, ya ce cibiyar za ta taimaka wajen rage dogaro da kayayyakin waje tare da ƙarfafa tattalin Najeriya
- Ana shirin gina makamantan cibiyoyi a kowace shiyya ta ƙasar domin samar da ayyukan yi da tallafawa wajen samar da gidaje masu araha
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Legas - Gwamnatin Tarayya ta ɗauki mataki domin rage tsadar gina gidaje a Najeriya, ta hanyar gina cibiyar kayan gine-gine a Lekki, jihar Legas.
An tabbatar da cewa an samu fili mai girman hekta 200 a cikin yankin kasuwanci na Lekki domin wannan aiki.

Source: Facebook
Rahoton Nairametrics ya nuna cewa ministan gidaje, Ahmed Dangiwa, ne ya bayyana hakan yayin ziyarar sa yankunan masana’antu na Lekki da ke Lagos.

Kara karanta wannan
Tinubu ya fadi gaskiyar abin da ke kai shi kasashen waje bayan dawowa daga Brazil
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce manufar cibiyar ita ce inganta samar da kayayyaki a cikin gida tare da rage dogaro da kaya daga kasashen waje.
Za a yi cibiyar kayan gine-gine a Lagos
A cewar ministan, cibiyar da za a yi a Lekki za ta kasance cike da abubuwan more rayuwa na zamani kamar hanyoyin jirgin ƙasa.
Ya ce za a samar da tashar jiragen ruwa, da kuma manyan hanyoyi domin tabbatar da isar kayayyakin cikin sauƙi.
Ya bayyana cewa cibiyar za ta mayar da hankali wajen samar da abubuwa kamar rufin gidaje, ƙofofi da tagogi, da sauran muhimman kayayyaki da ake amfani da su wajen gina gidaje.
Dangiwa ya kuma tabbatar da cewa cibiyar za ta samar da wutar lantarki da ruwan sha ga masana’antun da za su yi aiki a cikinta tare da masauki ga ma’aikata.
Shirin samar da cibioyin a jihohi
A watan Agustan 2024, gwamnatin tarayya ta sanar da shirin gina irin waɗannan cibiyoyin kayan gine-gine a kowane yanki na ƙasar guda shida.
Wannan tsari ya samu muhimmanci a kasafin kuɗin shekarar 2025 na ma’aikatar gidaje da ci gaban birane.

Source: Twitter
Baya ga Lekki, sauran wuraren da aka zaɓa sun haɗa da Sagamu a Ogun, Aba a Abia, Warri/Asaba a Delta, Ajaokuta a Kogi, Kano a Kano da kuma Gombe a Gombe.
Tsari ya haɗa da baiwa masu zuba jari filaye aƙalla hekta 100 domin su zuba kuɗi da yin gini, amma bayan sun dawo da jarinsu, za a mayar da mallakar cibiyoyin ga gwamnati.
Tsarin da za a yi a cibiyar gine ginen
Ministan ya bayyana cewa za a ba da cikakkiyar dama wajen tsara gine-gine da gudanar da masana’antu a cibiyar.
A matsayin kari, gwamnati za ta sauƙaƙa musu wajen shigo da injina da kayan aiki ba tare da harajin kwastam ba.
An kafa kamfanin takalma a Legas
A wani rahoton, kun ji cewa uwargidan shugaban kasa, Sanata Remi Tinubu ta kaddamar da kamfanin hada takalma a Legas.
Gwamnatin jihar Legas ta bayyana cewa baya ga takalma, za a rika hada bel, jaka da sauran kayayyakin da ake yi da fata a masana'antar.
Hadimin tsohon gwamnan Kano, Salihu Tanko Yakasai ya yi korafi da cewa a Arewacin Najeriya ya kamata a samu irin kamfanin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
