Tinubu Ya Fadi Gaskiyar Abin da ke kai Shi Kasashen Waje bayan Dawowa daga Brazil

Tinubu Ya Fadi Gaskiyar Abin da ke kai Shi Kasashen Waje bayan Dawowa daga Brazil

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa duk wata tafiyarsa zuwa kasashen waje tana nufin bude kofar hanyoyin cigaban kasa
  • Ya ce a kasar Japan, Najeriya ta karfafa zumunci da zai kawo jarin masana’antu, fasaha da kuma inganta bangaren ilimi da kwarewa
  • A Brazil kuma ya ce an samar da hadin gwiwa a fannonin kasuwanci, noma, sufurin jiragen sama da kudi domin karfafa tattalin Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa tafiye tafiye da ya yi zuwa kasashen Japan da Brazil ba yawon gantali ba ne.

Ya ce babbar manufarsa ita ce neman hanyoyin da za su taimaka wajen kirkirar ayyukan yi, bunkasa harkokin kasuwanci, da kuma kara wa Najeriya daraja a idon duniya.

Kara karanta wannan

China ta ba da tallafin ambaliya, za a raba Naira biliyan 1.5 a jihohin Arewa

Shugaba Tinubu yayin tafiya kasar waje
Shugaba Tinubu yayin tafiya kasar waje. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Tinubu ya yi wannan bayani ne a shafinsa na X bayan dawowarsa daga ziyarar kwanaki 10 a Brazil, Japan tare da dan jinkiri a Los Angeles, Amurka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin tafiye tafiyen Tinubu ketare

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa duk wata yarjejeniya da ya rattabawa hannu a kasashen waje na da nufin kawo ci gaba a Najeriya.

A cewarsa:

"A 2023 kuka daura mani nauyin dawo da martabar Najeriya a idon duniya. Kuma na dukufa wajen cimma wannan"
“Duk hannun da muka sa kowace yarjejeniya, da kowace tattaunawa suna karkashin manufa guda daya ce: Samar da damar da za ta haifar da ci gaba, ayyukan yi da kuma walwalar ’yan Najeriya.”

The Cable ta rahoto ya ce wannan ne ginshikin sabuwar Najeriya da ake son gina wa – kasa mai dogaro da kai da dorewa.

Abubuwan da Tinubu ya cimma a Japan

Tinubu ya bayyana cewa a kasar Japan, Najeriya ta zurfafa alakar da za ta kawo zuba jari a bangaren masana’antu da fasahar zamani.

Kara karanta wannan

Abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da Sarkin da ya 'kunyata' Najeriya a Amurka

Haka kuma ya ce an samu tattaunawa kan bunkasa ilimi da kwarewar dan Adam a fannoni daban daban.

Wannan, a cewar sa, zai taimaka wajen samar da kwararru da za su taka rawa wajen cigaban kasa.

Shugaba Tinubu na shirin fita a cikin jirgi
Shugaba Tinubu na shirin fita a cikin jirgi. Hoto: Bayo Onanuga
Source: UGC

Ya kara da cewa Najeriya ta bukaci kasashen abokan hulda bayar da muhimmanci kan zuba jarin da zai haifar da canji mai dorewa ga al’umma.

Tinubu ya ce ya samu nasara a Brazil

A Brazil kuwa, Tinubu ya bayyana cewa Najeriya ta samu gagarumin ci gaba wajen karfafa huldar tattalin arziki.

Ya ce kasashen biyu sun kulla yarjejeniya a fannonin kasuwanci, noma, harkokin kudi da kuma sufurin jiragen sama.

Wannan, in ji shi, zai taimaka wajen karfafa karfin gwiwa a kan tattalin arzikin Najeriya da kuma samar da damar kasuwanci ga al’ummar kasa.

An nemi Tinubu ya saki Ramzy

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyoyin farar hula sun yi Allah wadai da kama shugaban Falasdinya a Najeriya, Ramzy Abu Ibrahim.

Kungiyoyin sun ce kama shugabannin Falasdinawa a Najeriya saboda ra'ayin siyasa ya saba dimokuradiyya.

Sun bukaci a saki shugaban ba tare da wani sharadi ba, tare da kira ga Najeriya ta kaucewa shiga rikicin Gabas ta Tsakiya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng