Tsautsayi: Yadda N8,000 Ta Jawo Asarar Rai a Kasuwar Legas
- Rikicin rabon kuɗi N8,000 ya jawo kashe wani matashin mai talla a kasuwar Mandillas, da ke jihar Legas ya jawo tashin hankali
- ’Yan sanda sun ce ba rikicin kabilanci ba ne, kamar yadda ake yada wa illa dai sabanin ’yan a tsakanin 'yan talla da abokan huldarsu
- Lamarin ya jawo tsaiko ga hada-hada a kasuwar bayan da aka tabbatar da rasuwar Sodiq Ibrahim da wani 'dan kabilar Ibo ya kashe
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Lagos – Rahotanni sun bayyana cikakken bayani kan rikicin da ya kai ga mutuwar wani mai talla, Sodiq Ibrahim, a yankin Mandillas a kasuwar Legas a ranar Laraba.
Wani abokin aikinsa mai suna Ebuka Adindu ne ake zargi da kashe shi, bayan sun samu sabani kan rabon kuɗi N8,000 da aka ba su.

Source: Facebook
Jaridar Punch ta ce bayan lamarin ya auku, ’yan kasuwa sun rufe shaguna na ɗan lokaci a kasuwar Balogun, amma daga baya kasuwanci ya ci gaba da tafiya ranar Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan sanda sun magantu kan kisa a Legas
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin, tare da kore batun kabilanci a rikicin.
Ya bayyana cewa:
“Ebuka Adindu daga jihar Abia ya daba wa Sodiq Ibrahim daga jihar Kogi wuƙa har ya mutu. Bayan haka kuma ya daba kansa a kafaɗa, yanzu haka yana asibiti inda ake tsare da shi. Ana ci gaba da bincike, bayan ya warke za a gurfanar da shi a kotu.”

Source: UGC
Shaidun ganin da ido sun bayyana Ibrahim da Adindu da cewa 'yan ƙungiyar Oso Ahia, wadda ake kira masu kawo kwastomomi cikin shaguna domin a ba su kamasho.
Shaidu sun magantu kan kisa a Legas
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa abin da ya jawo rikicin da har ya jawo asarar rai bai taka kara ya karya ba.
Wata ’yar kasuwa mai suna Funmi Arewa ta ce:
“Su biyu ne kawai masu kawo kwastomomi. Sun kawo kwastoma guda ɗaya tare, sai mai shago ya ba su N8,000 su raba. Da suka fara gardama ne rikicin ya ɓarke.”
Wani 'dan kasuwa, Moshood, ya ce:
“Rikicin bai da nasaba da kabilanci. Rikicin kuɗi ne kawai tsakanin masu talla. Mun yanke shawara cewa irin waɗannan ’yan talla ba za a sake bari su yi aiki a kasuwar nan ba.”
Haka kuma wani 'dan kasuwa, Abiola Shittu, ya bayyana cewa rufe shagunan da aka yi safiyar Alhamis ba saboda rikicin ba ne, illa dai saboda tsaftar kasuwa da ake yi a kullum.
ACF ta koka kan rusau a Legas
A baya, mun wallafa cewa kungiyar Arewa Arewa Consultative Forum (ACF) ta nuna damuwa sosai kan matakin da gwamnatin jihar Legas na rusau a hadaddiyar kasuwar Alaba Rago.
Kasuwar Alaba Rago, wadda ta shafe sama da shekaru 50 ana kasuwanci ta kasance muhimmiyar kafa ta tattalin arzikin dubunnan ’yan Najeriya, musamman Hausawan Arewa.
Rahotanni sun nuna cewa an fara rushe kasuwar tun daga ranar Lahadi, 17 ga watan Agusta, har zuwa Laraba, 20 ga watan Agusta, lamarin da ya jefa 'yan kasuwa a cikin wahala.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

