An Sako Tinubu a gaba kan Kama Shugaban Falasdinawa a Najeriya
- Kungiyoyin farar hula sun bukaci a gaggauta sakin shugaban al’ummar Falasdinawa da aka kama a Abuja
- Bayanin da suka fitar ya zargi jami’an tsaro da karya dokokin kare hakkin Bil’adama wajen kama shugaban
- Kungiyoyin sun gargadi gwamnati da kada Najeriya ta shiga rikicin Gabas ta Tsakiya ta hanyar nuna son kai
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FC,T, Abuja - Kungiyoyin farar hula a Najeriya karkashin hadin gwiwar UAD sun yi kira ga Bola Ahmed Tinubu da ya bada umarnin sakin shugaban Falasdinawa da aka tsare a Abuja.
Shugaban Falasdinawa, Ramzy Abu Ibrahim, tare da wasu jagororin al’ummar, sun shiga hannun jami’an da ake kyautata zaton rundunar yaki da ta’addanci ce.

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa kungiyoyin sun ce bai kamata Najeriya ta gallazawa Falasdinawa a kasar nan ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kafin lamarin, Ibrahim ya kasance mai fafutukar tabbatar da zaman lafiya a rikicin Isra’ila da Falasdinu, abin da kungiyoyin suka ce shi ne dalilin tsare shi.
Zargin karya dokokin hakkin bil’adama
Kungiyoyin farar hula sun bayyana tsare shugaban al’ummar Falasdinawa a matsayin abin da ya saba doka, tare da karya yarjejeniyoyin kasa da kasa da Najeriya ta rattaba hannu a kansu.
A cikin wata sanarwa da shugaban UAD, Kunle Ajayi, ya fitar a ranar Laraba, an yi gargadin cewa kamata ya yi gwamnatin Najeriya ta mutunta hakkokin Falasdinawa da ke zaune a kasar.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa hanyar da aka bi wajen tsare su ta sabawa ka’ida, tana mai jaddada cewa hakan ya sabawa tsarin doka da hukunce-hukuncen duniya kan hakkin bil’adama.
Gargadin Najeriya kan rikicin Falasdinawa
Kungiyoyin sun ce Najeriya na fama da matsaloli, ciki har da koma bayan tattali, rashin tsaro da rikicin manoma da makiyaya, don haka bai kamata a jefa kasar a rikicin Falasdinu da Isra’ila ba.
Kungiyoyin sun kuma jaddada bukatar gwamnati ta tabbatar cewa Falasdinawa da ke Najeriya ba su fuskantar cin zarafi, tsangwama ko tauye hakkinsu saboda ra’ayoyin siyasa.
Kiran a sake duba yarjejeniyoyi da Isra’ila
Sanarwar ta kara da cewa ya zama wajibi a sake nazarin duk wata yarjejeniya da Najeriya ta kulla da Isra’ila wadda za ta iya tauye ikon kasa da ‘yancin dimokaradiyya.
Kungiyoyin sun yi kira ga 'yan Najeriya da su tsaya a kan gaskiya, tare da kin amincewa da duk wani yunƙuri na amfani da kasar wajen murkushe zaman lafiya da ‘yancin Falasdinawa.

Source: Twitter
Kungiyoyin sun yi kira da cewa dole ne a gaggauta sakin Abu Ibrahim da sauran shugabannin Falasdinawa don kare martabar kasa da kuma tabbatar da adalci ga dukkan mazauna Najeriya.
Wani rahoto da Trust TV ta wallafa ya nuna cewa wasu kungiyoyi sun yi zanga zanga kan kama shugaban da aka yi.
Makari ya soki kama shugaban Falasdinawa
A wani rahoton, kun ji cewa limamin babban masallacin kasa na Abuja, Farfesa Ibrahim Makari ya yi kira da a saki shugaban Falasdinawa.
Farfesa Makari ya bayyana cewa tsare shugaban Falasdinawa a Najeriya cin fuska ne ga Musulmi a kasar nan.
Malamin ya kare da cewa kama shugaban ya kara nuna inda Najeriya ta dosa wajen yin biyayya ga muradun Isra'ila.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


