Katsina: Za a Rika ba Limamai, Masu Sharar Masallatan Izala da Darika Kudin Wata

Katsina: Za a Rika ba Limamai, Masu Sharar Masallatan Izala da Darika Kudin Wata

  • Gwamna Dikko Radda ya ce yaki da rashin tsaro shi ne babban ajandar gwamnatinsa tun daga ranar farko da ya hau karagar mulki
  • Ya amince da karin albashi ga dagatai da tallafin kudi ga masu unguwanni 6,652, limamai sama da 3,000 da masu share masallatai
  • Gwamnatin ta kuma ware Naira miliyan 20 ga kowace karamar hukuma domin gyaran makabartu a fadin jihar Katsina

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina - Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda, ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da daukar matakai masu tsauri wajen yaki da rashin tsaro.

Ya bayyana hakan ne lokacin da ya karbi bakuncin sarakuna daga masarautun Katsina da Daura a fadar gwamnati.

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda. Hoto: Ibrahim Kaulaha Muhammad
Source: Facebook

Mai magana da yawun gwamnan, Ibrahim Kaulaha Muhammad ne ya wallafa bayanin da gwamnan ya yi a wani sako da ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Ana hallaka jama'ansa, Gwamna Radda zai kashe Naira miliyan 680 a gyaran maƙabartu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya jaddada cewa gwamnati na iya samun nasara ne kawai idan jama’a da shugabannin al’umma suka hada kai domin fuskantar barazanar ’yan bindiga da sauran miyagu.

Matakan Gwamna Radda wajen yaki da rashin tsaro

Radda ya tunatar da cewa tun daga ranar da ya hau mulki ya dauki magance matsalar tsaro da muhimmanci, kuma sama da matasa 1,500 aka horas a shirin yaki da rashin tsaro.

Premium Times ta wallafa cewa gwamnan ya ce karin matasa 550 sun kammala samun horo yayin da rukuni na uku ke ci gaba da atisaye.

Radda ya yi wa limamai da dagatan Katsina gata

A cewar Gwamna Radda, an kafa sabuwar doka wacce ta tabbatar da cewa dagatai za su rika samun albashin da bai gaza na matakin matsayi na 16 zuwa sama ba a aikin gwamnati.

Haka kuma, sama da masu unguwanni 6,652 a duk fadin jihar za su rika karbar alawus-alawus na wata-wata domin tallafa musu.

Kara karanta wannan

Harin masallaci: Gwamna Radda ya ziyarci kauyen Mantau, ya dauki alkawura

Fiye da limamai 3,000 da na’ibansu daga manyan masallatan Juma’a suma za su samu tallafin kudi.

Haka nan masu share masallatan Izala da Darika a kananan hukumomi 34 za su ci gajiyar wannan shiri.

Dikko Radda tare da Hafsun tsaro, Janar Musa
Dikko Radda tare da Hafsun tsaro, Janar Musa. Hoto: Ibrahim Kaulaha Muhammad
Source: Facebook

Za a gyara makabartun jihar Katsina

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnati ta ware fiye da Naira miliyan 20 ga kowace karamar hukuma domin gyara makabartu.

Dikko Radda ya ce wannan aikin ibada ne da kuma hidima ga al’umma da za ta jawo rahamar Allah ga jihar.

Ya kuma yi kira ga shugabannin gargajiya da na addini da su rika wayar da kai domin jama’a su gane cewa nasarar yaki da rashin tsaro na bukatar hadin kai.

Sarakunan Kastina da Daura sun yaba da matakin da gwamnan ya dauka da kuma alkawarin cigaba da tallafawa wajen yaki da rashin tsaro.

Limamin Izala ya rasu a Kebbi

A wani rahoton, kun ji cewa shugabana kungiyar Izala a karamar hukumar Birnin Kebbi ya rasu bayan rashin lafiya.

Rahotanni sun nuna cewa Sheikh Tukur Kola ya rasu ne a jihar Kebbi kuma an masa sallah a masallacin Juma'ar da ya ke limanci.

Malamai da dama a Najeriya, ciki har da Sheikh Ibrahim Aliyu Kaduna sun yi jimamin rasuwar malamin da ya dade yana karantarwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng