Gwamna Ya Kara Mafi Karancin Albashi, Karamin Ma'aikaci Zai Samu N90,000 duk Wata
- Mafi karancin albashin ma'aikata a jihar Ebonyi ya tashi daga N70,000 da aka amince da shi a matakin kasa zuwa N90,000
- Gwamna Francis Nwifuru ya kara mafi karancin albashin ne a wani bangare na inganta walwala da jin dadin ma'aikatan gwamnati a Ebonyi
- Kwamishinan yada labarai da wayar da kan jama'an Ebonyi ya ce Gwamna Nwifuru ya biya hakkokin duka ma'aikatan da suka yi ritaya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Ebonyi - Gwamna Francis Nwifuru ya kara mafi karancin albashin ma'aikatan gwamnati a jihar Ebonyi da ke Kudu maso Gabashin Najeriya.
Gwamna Nwifuru na jam'iyyar APC ya zarce mafi karancin albashi na N70,000 da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya amince da shi har ya zama doka a Najeriya.

Source: Facebook
Gwamna ya kara mafi karancin albashi

Kara karanta wannan
"Ana barazana ga rayuwata," Shugaban NNPCL ya tona masu son raba shi da mukaminsa
Jaridar Tribune ta rahoto cewa gwamnan Ebonyi ya kara wa ma'ikata albashi, inda za a rika biyan N90,000 a matsayin mafi karancin albashi a jihar da ke Kudu.
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a na jihar, Cif Ikeuwa Omebe, ne ya bayyana haka a ranar Alhamis da yake hira da manema labarai bayan taron majalisar zartarwar Ebonyi.
A cewar Omebe, sabon mafi karancin albashi na N90,000 zai fara aiki nan take kuma ya shafi dukkan rukunan ma’aikatan gwamnatin Ebonyi.
“Muna tabbatar maku da cewa wannan ba siyasa ba ce, domin gwamnati mai ci ba ta wasa da jin daɗin ma’aikata,” in ji shi.
Gwamna Nwifuru ya biya hakkokin yan fansho
Ya ƙara da cewa gwamnati ta biya bashin fansho da hakkokin ma’aikata tun daga lokacin da aka ƙirƙiri jihar Ebonyi a shekarar 1996 har zuwa yau.
Haka kuma, ya bayyana cewa ana ci gaba da tantance tsofaffin ma’aikatan ƙananan hukumomi, kuma bayan an kammala, za a biya su hakkokinsu.
Kwamishinan ya jaddada cewa ƙarin albashin shaida ce da ke tabbatar da aniyar gwamnatin Nwifuru ta kula da jin dadi da walwalar ma’aikata.
"Idan tun farko gwamnati ba ta yi siyasa da kudi masu nauyi ba, ba za ta yi siyasa da ƙarin N20,000 kacal ga ma’aikata ba,” in ji shi.

Source: Twitter
An fara yabon gwamnan jihar Ebonyi
Omebe ya yabawa Gwamna Francis Nwifuru, yana mai bayyana shi a matsayin “jagora, mai gina ɗan Adam.”
Kwamishinan ya kara da cewa gwamnatin Ebonyi tana tafiya ne da manufar “bukatar jama’a” kamar yadda littafi mai tsarki ya tanada, cewar rahoton The Nation.
Haka kuma, ya bayyana cewa majalisar zartarwar jihar ta amince da aiwatar da kudirin wa’adin shekaru takwas ga daraktoci a hukumomin gwamnati a Ebonyi.
Amurka ta soki mafi karancin albashin Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa Amurka ya bayyana cewa albashi mafi karanci da ake biyan ma'aikata a Najeriya ba zai iya fitar da 'yan kasa daga talauci da matsi ba.
Rahoton da ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar, ya ce duk da karin albashin da aka yi, har yanzu wasu jihohin Najeirya kasa biyan N70,000.
A rahoton, Amurka ta bayyana cewa wannan albashin ba zai dauki nauyin ma'aikaci ba, sannan ba zai iya ceto mutanen Najeriya daga talauci ba.
Asali: Legit.ng
