Mako 2 bayan Gwamna Ya Sauke Shi, Tsohon Shugaban Jami'a Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Mako 2 bayan Gwamna Ya Sauke Shi, Tsohon Shugaban Jami'a Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Jami'ar jihar Edo da ke garin Iyahmo ta rasa tsohon mukaddashin shugaban makarantar, wanda ya mika ragamar mulki ga sabon shugaba
  • A wata sanarwa da hukumar jami'ar ta fitar yau Alhamis, ta ce Farfesa Dawood Egbefo ya rasu ranar Laraba, 27 ga watan Agusta, 2027
  • Hukumar makaranta, ma'aikata da dalibai sun yi alhinin rasuwar Farfesa Dawood, tare da mika sakon ta'aziyya ga iyalansa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Edo - Tsohon mukaddashin shugaban jami’ar jihar Edo da ke Iyahmo, Farfesa Dawood Egbefo, ya rasu makonni biyu bayan ya mika ragamar mulki ga magajinsa.

Rahotanni sun bayyana cewa Farfesan ya riga mu gidan gaskiya ne a ranar 27 ga Agusta, 2025 a jihar Edo da ke Kudu maso Kudancin Najeriya.

Farfesa Dawood Egbefo.
Hoton tsohon shugaban Jami'ar Jihar Edo, Farfesa Dawood Egbefo Hoto: University Of Edo
Source: Facebook

Mai magana da yawun jami’ar, Amaechi Kelly Quincy, ne ya tabbatar da wannan labari cikin wani sakon da ya wallafa a shafin Facebook na jami’ar Edo.

Kara karanta wannan

Makinde: Gwamna zai mika ragamar mulki ga mataimakinsa, an ji dalili

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna ya sauya shugaban jami'ar Edo

Daily Trust ta ruwaito cewa a ranar 8 ga Agusta, 2025, gwamnan Edo, Monday Okpebholo, ya sanar da nadin sabon shugaban jami’ar, Farfesa Victor Adetimirin Olawale.

Farfesa Adetimirik Olawale ya maye gurbin Egbefo, wanda ya jagoranci jami'ar a matsayin shugaban rikon kwarya.

Tsohon shugaban jami'ar Edo ya rasu

Sai dai a sanarwar jami’ar ta fitar yau Alhamis, 28 ga watan Agusta, 2025 ba ta bayyana musabbabin mutuwar Farfesa Dawood ba.

A cewar Quincy:

“Egbefo malami ne kwararre, masani, mai hikima kuma hazikin jagora, wanda ya yi tasiri wajen jagorantar dalibai da kuma ma’aikata.”

Farfesa Egbefo ya kammala karatun digiri na farko, na biyu da kuma digirin digirgir (PhD) a fannin Tarihi da Nazarin Huldar Kasa da Kasa daga Jami’ar Ilorin.

Ya fara aikin koyarwa a Jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) da ke Lapai, kafin daga bisani ya koma Jami’ar Edo, Iyahmo a 2017 a matsayin wanda ya kusa zama Farfesa

Kara karanta wannan

ASUU: Malaman jami'a sun fara yi wa gwamnatin Tinubu zanga zanga a fadin Najeriya

Hukumar jami'a ta mika sakon ta'aziyya

Rasuwarsa ta girgiza jami’ar, inda malamai da dalibai ke bayyana shi a matsayin mutum mai jajircewa, dattijo mai hangen nesa kuma wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen gina ilimi da raya al’umma.

Jami'ar jihar Edo.
Hoton babban allon da ke gefen jami'ar jihar Edo Hoto: Edo State University
Source: Facebook
"Hukumar makaranta, ma’aikata da daliban jami’ar Jihar Edo na alhinin rasuwar tsohon mukaddashin shugaban jami’a, Farfesa Dawood O. Egbefo.
"Muna mika ta’aziyyarmu ta musamman ga iyalansa, abokan aiki, abokai da dukkan al’ummar da wannan babban rashi ya shafa.
"Allah Madaukaki Ya ji kan sa, Ya ba shi hutu, Ya kuma ba iyalansa hakuri da ƙarfin zuciya wajen jure wannan babban rashi," in ji sanarwar.

Malamin jami'a ya mutu a otal a Kogi

A wani rahoton, kun ji cewa Dr. Olabode Ibikunle, babban malami a Jami’ar PAAU da ke Kogi, ya rasu yayin da yake lalata da wata ɗaliba.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Kogi, SP William Aya, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an tsinci gawar malamin a wani otal a garin Anyigba.

SP Aya ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, yana mai cewa an riga an gudanar da binciken gawar malamin domin gano musabbabin rasuwarsa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262