An Zo Wajen: Ministan Tinubu Ya Fadi Lokacin Kawo Karshen Matsalar Rashin Tsaro
- 'Yan Najeriya nan ci gaba da kokawa kan matsalolin rashin tsaron da ake fama da su a sassan daban-daban na kasar nan
- Ministan yada labarai, Mohammed Idris, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na bakin kokari don ganin an shawo kan matsalar
- Mohammed Idris ya kwantar da hankalin 'yan Najeriya, inda ya nuna cewa za a kawo karshen 'yan bindiga da 'yan ta'adda
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Zamfara - Ministan yaɗa labarai da wayar da kan al'umma, Mohammed Idris, ya sake yin magana kan matsalar rashin tsaro.
Mohammed Idris ya ba da tabbacin cewa matsalolin tsaro da Najeriya ke fuskanta za su zama tarihi nan gaba kaɗan.

Source: Twitter
Jaridar Tribune ta ce ministan ya bayyana hakan ne yayin wani shirin wayar da kai kan ayyukan gwamnatin Bola Tinubu da aka gudanar a birnin Gusau, jihar Zamfara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mohammed Idris ya samu wakilcin shugaban ma’aikatar yaɗa labarai ta tarayya a Zamfara, Alhaji Auwal Balarabe.
Minista ya ce ana daukar matakan kawo tsaro
Ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta dukufa wajen kawar da ta’addanci da ’yan ta’adda cikin kankanin lokaci.
Haka kuma, ya bayyana cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta riga ta samar da manyan nasarori da tsare-tsare masu ma’ana.
"Yadda kuka sani, aikin ma’aikatar yaɗa labarai da shi ne bayani kan manufofin gwamnatin tarayya tare da wayar da kan ’yan kasa game da ayyukan da ake gudanarwa domin amfanin kowa da kowa."
- Mohammed Idris
A cewarsa, aikin wayar da kan zai bai wa ’yan Najeriya damar sanin muhimman ayyukan ci gaba da gwamnatin Tinubu ke gudanarwa, musamman a fannonin tsaro, ababen more, noma, ilimi da sauransu.
"Ina farin cikin sanar da ku cewa an samu manyan nasarori, ciki har da dalibai sama da 300,000 da suka ci moriyar shirin ba da lamuni na NELFUND, mutane 900,000 sun amfana da lamunin tallafin kuɗi na shugaban kasa."
"Aikin gina tituna sama da 440 na ci gaba da gudana, sannan kuma an fara biyan mafi karancin albashi na N70,000. Haka kuma akwai tallafin noma da sauran shirye-shiryen gwamnatin tarayya."
- Mohammed Idris
Minista ya bayyana cewa waɗannan matakai da tsare-tsaren gwamnati za su rage tsananin ƙuncin da ’yan Najeriya ke fuskanta, sannan ya yi kira ga al’ummar Jihar Zamfara da su amfana da wadannan shirye-shirye domin jin daɗin dimokuraɗiyya.

Source: UGC
Yaushe za a kawo karshen rashin tsaro?
"A wannan lokaci, ina mika ta’aziyyar gwamnatin tarayya bisa matsalar ta’addanci da ’yan bindiga da ake fuskanta a wannan yanki."
"Ina tabbatar muku cewa matsalolin tsaro za su zama tarihi nan ba da daɗewa ba, domin gwamnatin tarayya ta kuduri aniyar kawar da ta’addanci da ’yan ta’adda gaba daya."
- Mohammed Idris
Daga ƙarshe, ya yaba wa gwamnatin jihar Zamfara bisa goyon baya da ƙoƙarinta wajen ganin an kammala shirin cikin nasara, tare da gode wa dukkan mahalarta taron.
Abdulwahab Ahmad ya shaidawa Legit Hausa cewa wasu daga cikin ministocin Tinubu suna yin kalamai ne kawai don kare kujerunsu.
"Ta yaya zai zo ya bude bakinsa kawai ya kama cewa nan ba da jimawa ba za a kawo karshen matsalar rashin tsaro? Sau nawa ana fadin irin hakan amma abubuwa kullum kara tabarbarewa suke yi."
"Mun gaji da gafara sa ba mu ga kaho ba. Ya kamata gwamnati ta nuna da gaske take yi ta hanyar daukar matakan da suka dace don kawo karshen matsalar."
- Abdulwahab Ahmad
Sojoji sun dakile harin 'yan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasara kan 'yan bindiga a jihar Zamfara.
Sojojin na rundunar Operation Fansan Yamma sun dakile wani harin 'yan bindiga kam hanyar Gusau-Tsafe.
Hakazalika, jami'an tsaron sun kwato babura guda hudu tare da raunata 'yan bindiga da dama bayan an yi artabu mai tsanani.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


