Shugaba a Izala, Sheikh Tukur Kola Ya Rasu a Jihar Kebbi
- An sanar da rasuwar Sheikh Imam Tukur Kola, shugaban kungiyar JIBWIS a ƙaramar hukumar Birnin Kebbi
- Malamin ya rasu bayan doguwar jinya, inda aka shirya gudanar da jana’izarsa yau Alhamis da misalin ƙarfe 2:30 na rana
- Mazauna Birnin Kebbi da sauran al’ummar Musulmi sun yi jimamin rashin, suna masa addu’ar rahama da aljanna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kebbi – Al’umma a jihar Kebbi sun shiga jimami bayan rasuwar babban malami kuma jagora, Sheikh Imam Tukur Kola.
Rahotanni sun nuna cewa shi ne shugaban kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Ikamatus Sunnah (JIBWIS) na ƙaramar hukumar Birnin Kebbi.

Source: Facebook
Legit ta tattaro bayanai kan rasuwar malamin ne a cikin wani sako da shafin Jibwis Kebbi ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sheikh Kola ya yi jinya a Kebbi
Rahotanni sun nuna cewa Sheikh Kola ya rasu ne bayan wata doguwar jinya da ya sha fama da ita kafin Allah ya karbi ransa a yau ranar Alhamis 28 ga watan Agusta, 2025.
Bayanai sun tabbatar da cewa za a gudanar da jana’izarsa a masallacin Juma’a na Dr. Bello Haliru da ke Birnin Kebbi da misalin ƙarfe 2:30 na rana.
Jama'a sun yi jimamin rasuwar malamin
Wani jagoran kungiyar JIBWIS a jihar Kebbi, Kamaludeen Alhassan Imam Libata, ya bayyana mutuwar a matsayin babban rashi ga al’umma baki ɗaya.
Ya yi addu’a da cewa:
“Allah ya jikansa da rahama, ya sanya Aljanna ce makomarsa.”
Haka kuma, Hussaini Abubakar Giro ya nuna alhini kan mutuwar Sheikh Tukur Kola, yana mai yi masa addu'a.
A sakon da ya wallafa a Facebook, ya ce:
“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un. Allah ya yi wa Sheikh Tukur Kola rasuwa, shugaban Izala na Birnin Kebbi. Allah ya jikansa da rahama.”
Haka zalika, malamin Musulunci, Sheikh Ibrahim Aliyu daga Kaduna ya bayyana cewa sun yi babban rashi.
A wani sako da ya wallafa a Facebook, malamin ya ce:
“Mun yi rashin babban malami, uba, jagora Sheikh Tukur Kola jihar Kebbi. Allah ya gafarta masa.”
Wannan jawabi ya nuna irin daraja da matsayin da marigayin yake da shi a tsakanin malamai da mabiyansa, musamman wajen jagoranci da kuma koyar da darussan addini.

Source: Facebook
Jama’a da dama sun bayyana ta’aziyya da addu’o’i a kafafen sada zumunta, inda aka rika tura sakonnin jimami da fatan samun rahamar Allah ga marigayin.
An bayyana Sheikh Kola a matsayin malami mai kishin al’umma, mai faɗakarwa da kuma jagora wanda ya yi tasiri wajen yada sunnah da koyar da addinin musulunci cikin gaskiya da jajircewa.
Malamin Musulunci ya rasu a Saudi
A wani rahoton, kun ji cewa Allah ya yi wa wani malamin addinin Musulunci, Sheikh Abdul Wakeel Al-Hashimi rasuwa.
Gwamnatin kasar Saudiyya ce ta sanar da rasuwar malamin tare da cewa duniyar Musulunci ta yi babban rashi.
Malamai da dama da dalibai sun bayyana cewa Sheikh Abdul Wakeel ya shafe shekaru da dama yana koyar da ilimin addini.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

