An Kama 'Dan Daban da Ya Fito da Wani Salo domin Firgita Kano da Makamai

An Kama 'Dan Daban da Ya Fito da Wani Salo domin Firgita Kano da Makamai

  • Rundunar ’yan sandan Kano ta kama sanannen ɗan daba Mohammed Isma’il da ake kira da Linga tare da abokinsa
  • An kama su ne da makamai masu haɗari yayin da suke yada bidiyo a TikTok da Facebook suna tada hankalin jama’a
  • Kwamishinan ’yan sanda ya gargadi matasa da duk wanda ya sake yin irin haka zai fuskanci hukunci mai tsanani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta bayyana cewa ta samu nasarar cafke wasu fitattun ’yan daba da ake zargi da tada hankula da tayar da rikici a cikin al’umma.

Mutanen sun shahara wajen yada bidiyo a shafukan sada zumunta suna nuna makamai suna kuma ɗaukar matasa don aikata barna.

Kakakin 'yan sandan jihar Kano yana bayani a wani taro
Kakakin 'yan sandan jihar Kano yana bayani a wani taro. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

Kakakin 'yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana haka a wani sako da ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Mutane za su gwabza da 'yan bindiga a Katsina, 'dan majalisa ya saye makamai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan mataki na zuwa ne bayan korafe-korafe daga al’umma da suka nuna damuwa kan yadda bidiyon ke jefa tsoro da fargaba a zukatan jama’a musamman mazauna Dala da kewaye.

Kwamishinan ’yan sanda na jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya tabbatar da cewa jami’ansa sun dauki matakin gaggawa domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Kano: An kama 'yan daba Linga da Guchi

An kama sanannen ɗan daba Mohammed Isma’il wanda aka fi sani da Linga tare da wani abokinsa mai suna Sani Abdulsalam wanda ake kira Guchi.

A lokacin da aka cafke su, jami’an tsaro sun gano wuka mai tsawo da kuma manyan sanduna guda biyu da suke amfani da su wajen firgita da jama’a.

Rahotanni sun nuna cewa mutanen suna amfani da kafafen sada zumunta musamman TikTok da Facebook wajen yada bidiyo suna nuna makaman.

Kwamishinan 'yan sandan Kano, CP Bakori
Kwamishinan 'yan sandan Kano, CP Bakori. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

Yan sanda sun ce suna kuma kiran matasa su biyo su domin tada tarzoma, wanda hakan ya sanya jama’a cikin tsoro da fargaba saboda yiwuwar barkewar rikici.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari a Kano, an yi garkuwa da mutane

Gargadin ’yan sanda ga jama'an Kano

Kwamishinan ’yan sanda ya bayyana cewa za a kama duk wanda aka samu yana yada irin wannan bidiyo ko kuma yana amfani da makamai wajen tada rikici ba tare da izini ba.

Bayan kama mutum, rundunar ta ce za a gurfanar da shi a gaban kotu tare da fatan fuskantar hukunci mai tsauri.

CP Bakori ya shawarci iyaye da masu kula da yara da su sanya ido sosai a kan ’ya’yansu domin kada su fada tarkon yin daba ko aikata miyagun laifuffuka.

Rundunar ta nanata cewa za ta ci gaba da aiki tukuru wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a ba tare da sassauci ba.

'Yan bindiga sun kai hari a jihar Kano

A wani rahoton, kun ji cewa wasu 'yan bindiga da ba a gano ko su waye ba sun kai farmaki jihar Kano.

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun yi nasarar awon gaba da wani mutum yayin da suka farmaki unguwarsu.

An bukaci hukumomi su cigaba da sa ido da daukar matakan da suka dace domin hana yaduwar ta'addanci a jihar Kano.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng