Rigimar Sarauta na Neman Haɗa Gwamnoni 2 Faɗa, Sarki Ya Gargaɗi Gwamnan Jiha

Rigimar Sarauta na Neman Haɗa Gwamnoni 2 Faɗa, Sarki Ya Gargaɗi Gwamnan Jiha

  • An taso gwamna a gaba kan zargin kokarin kakaba sabon Sarki ga al'umma ba bisa ka'ida ba wanda zai iya jawo rigima
  • Sarkin Irokun, Oba Buari Ola Balogun, ya bukaci gwamnatin Ondo ta daina yunƙurin da ya kira wanda ba bisa ka’ida ba na naɗa Sarki
  • Ya gargadi cewa shirin kawo wani Sarki a ranar 31 ga Agusta zai iya haddasa rikici, tashin hankali da asarar rayuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abeokuta, Ogun - Ana ci gaba da takun saka tsakanin al'umma da gwamnatin Ondo game da nadin sabon Sarki.

Rigimar ta taso ne yayin da gwamnatin Ondo ke kokarin nada Sarki wanda aka ce a jihar Ogun yake ba Ondo ba.

Sarki ya gargadi Gwamna kan nada sabon basarake
Gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa yayin wani taro a Akure. Hoto: Lucky Aiyedatiwa.
Source: Twitter

Sarki ya gargadi gwamna kan nadin basarake

Sarkin Irokun na masarautar Irokun da ke karamar hukumar Ogun Waterside a jihar Ogun, Oba Buari Ola Balogun ya gargadi gwamnatin Ondo, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da Sarkin da ya 'kunyata' Najeriya a Amurka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Basaraken ya bukaci gwamnatin Ondo ta daina yunƙurin naɗa sabon Sarki ba bisa ka’ida ba.

Ya jaddada cewa wannan yanki tun a tarihi, doka, tsarin mulki da siyasa mallakar Ogun ne, ba na Ondo ba, don haka ba su da hurumin nada shugaba.

Oba Balogun ya yi gargadin cewa shirin nada sabon Sarki zai iya jawo rikici, tashin hankali da asarar rayuka.

Sanarwar ta ce:

"Dole a dauki mataki dokin hana afkuwar rikici wanda gwamnatin Ondo ke kokarin nada Sarki a yankin da ke karkashin ikon gwamantin Ogun ba Ondo ba."
Nadin Sarki na neman hada gwamnoni 2 fada
Gwamna Lucky Aiyedatiwa da takwaransa na Ogun, Dapo Abiodun. Hoto: Lucky Aiyedatiwa, Prince Dapo Abiodun.
Source: Facebook

Sarauta: Sarki ya kalubalanci gwamnatin Ondo

Ya ce an taba yi wa yankin hakan a 2022 lokacin da aka naɗa Oba na Irokun daga gwamnatin Ondo, amma mutumin ya rasu cikin kwanaki uku kacal, wanda har yanzu hankalinsu suke kwance lafiya, Vanguard ta ruwaito.

Ya kara da cewa tun kafin shi, sarakuna sama da bakwai sun zauna bisa karagar mulki a Irokun, kuma dukkaninsu gwamnatin Ogun ta tabbatar da su, karkashin kulawar babban Sarki na Ijebu.

Kara karanta wannan

Gwamna ya samu gagarumin goyon baya, ana so ya nemi takarar shugaban kasa a 2027

Oba Balogun ya bayyana cewa shi ne halataccen Onirokun, gwamnatin Ogun ta naɗa shi kuma ya shafe shekaru 18 yana mulki cikin kwanciyar hankali a masarautar.

Ya yi zargin cewa wasu da suka hada da Idowu Akinjirin na Igbo-edu da goyon bayan wasu jami’an Ondo suna neman tada rikici ta hanyar shirin tursasa shugabanci a kan masarautar.

Ya kara da cewa akwai sahihin rahoton leken asiri da ke nuna wani sabon nadin da aka shirya a ranar Lahadi 31 ga Agusta 2025 da goyon bayan gwamnatin Ondo da jami’an tsaro.

Ya ce:

"Dole a dakile wannan shiri na gwamnatin Ondo domin mallake yankin ta hanyar nada Sarki a masarautar."

Kotu ta hana Gwamna Lucky nada sabon Sarki

Mun ba ku labarin cewa wata kotu a garin Okitipupa ta yi hukunci kan karar da aka shigar da gwamna inda ya gargade shi kan nada Sarki.

Gwamna Lucky Aiyedatiwa nada Sarki a Alagbon a karamar hukumar Ilaje a jihar Ondo da ke Kudancin Najeriya.

Kotun ta dakatar da gwamnati da masu ruwa da tsaki daga daukar mataki bayan an amince da Ajaka a matsayin Gbogunron na Idi-Ogba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.