Bayan Kwashe Kwanaki a Kasashen Waje, Jirgin Shugaba Tinubu Ya Iso Najeriya
- Ziyarar da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kai zuwa wasu kasashen duniya ta zo karshe
- Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya dawo daga Najeriya bayan ya kammala gudanar da abubuwan da suka kai shi
- Shugaban kasan dai ya dawo gida ne tare da tawagar da ta yi masa rakiya zuwa kasashen da ya ziyarta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dawo gida Najeriya bayan ya kammala ziyarar da yaje yi.
Shugaba Bola Tinubu ya dawo gida Najeriya ne daga kasar Brazil a ranar Alhamis, 28 ga watan Agustan 2025.

Source: Twitter
Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ne ya sanar da hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bola Tinubu ya ziyarci wasu kasashe
Shugaba Tinubu ya tashi daga Abuja a ranar Alhamis, 14 ga Agusta, zuwa kasashen biyu watau Japan da Brazil.

Kara karanta wannan
"Ya godewa Allah": Tsohon dan takarar shugaban kasa ya ba Tinibu shawara kan 2027
A Japan, Shugaba Tinubu ya halarci taron Tokyo International Conference on African Development (TICAD9) karo na tara, wanda aka gudanar a birnin Yokohama daga ranar 20 zuwa 22 ga watan Agusta.
Shugaba Tinubu ya bar Japan a daren ranar Alhamis, inda ya yada zango na kwana uku a birnin Los Angeles na kasar amurka kafin daga bisani ya wuce zuwa Brazil
Abubuwan da Tinubu ya yi a Brazil
A Brazil kuma, Shugaba Tinubu ya gudanar da taron tattaunawar haɗin gwiwa da shugaban kasar, sannan ya halarci wani taron kasuwanci tare da ’yan kasuwa na Brazil.
Tun da farko Bayo Onanuga a shafinsa na X, ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu na kan hanyar dawowa gida Najeriya.
Bayo Onanuga ya kuma bayyana yadda ziyarar shugaba kasan zuwa Brazil ta kasance.
"Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nufi Abuja daga Brazil bayan ziyarar da ya kai, wadda ta mayar da hankali wajen karfafa dangantaka tsakanin Najeriya da Brazil."
"Jirgin fadar shugaban kasa ya tashi daga filin jirgin saman kasa da kasa na Brasília da misalin ƙarfe 12:57 na rana (lokacin kasar Brazil)."
"Jakadan Brazil a Najeriya, Amb. Carlos José Areias Moreno Garcete, da kuma Amb. Carlos Sérgio Sobral Duarte, sakatare na musamman kan harkokin Afirka da Gabas ta Tsakiya, sun halarci filin jirgin domin yi masa bankwana."
"Haka zalika, karamar ministar harkokin kasashen waje, Bianca Odumegwu-Ojukwu, tare da wasu jami’an gwamnati, sun kasance a wajen."
"Shugaba Tinubu ya isa Brasília da sassafe a ranar Litinin, 25 ga watan Agusta, domin gudanar da wannan muhimmin aikin diflomasiyya."
"Bayan isarsa, gwamnatin Brazil ta yi masa tarba ta musamman, inda aka shimfiɗa jan dadduma tare da yi masa girmamawar soja a Palácio do Planalto."
"Daga bisani, Shugaba Tinubu ya gana da Shugaban Brazil, Luiz Inácio Lula da Silva, tare da manyan jami’an kasar."
"Shugabannin biyu sun shaida rattaba hannu kan yarjejeniyoyi guda biyar (MoUs), waɗanda suka shafi bangarorin jiragen sama, harkokin kasashen waje, kimiyya da fasaha, da kuma aikin gona, manyan muhimman fannoni a cikin tsarin ci gaban Najeriya."
- Bayo Onanuga

Source: Twitter
An ba Tinubu shawara kan zaben 2027
A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar SDP a zaben 2023, Adewole Adebayo, ya ba Shugaba Bola Ahmed Tinubu shawara.
Adewole Adebayo ya shawarci Tinubu da ya hakura da neman tazarce idan abubuwa ba su sauya ba zuwa nan da 2027.
Ya bukace shi da ya koma gida, ya godewa Allah cewa ya taba mulkar Najeriya har na tsawon shekara hudu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

