2027: Kungiyar Kiristoci ta CAN Ta fitar da Sanarwa kan Yankan Katin Zabe
- Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) a Arewa ta yi kira ga jama’a da su yi rajistar katin zaɓe na dindindin (PVC) da INEC ke gudanarwa
- Shugaban CAN na Arewa, Fasto John Joseph Hayab, ya ce rajistar katin zaɓe ita ce matakin farko na kawo canji a shugabanci
- Ya bukaci malaman addinai da su wayar da kan jama’a tare da jaddada cewa ƙarfin sauyi a Najeriya yana hannun masu kada ƙuri’a
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) reshen jihohin Arewa ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi rajistar katin zaɓe da INEC ke gudanarwa a halin yanzu.
Shugaban CAN na Arewa, Fasto John Joseph Hayab, ya bayyana cewa yin rajista domin samun katin zaɓe shi ne matakin farko ga kowane ɗan ƙasa da ke son kawo sauyi.

Kara karanta wannan
ASUU: Malaman jami'a sun fara yi wa gwamnatin Tinubu zanga zanga a fadin Najeriya

Source: Facebook
Vanguard ta wallafa cewa Hayab ya yi nuni da cewa rashin rajista da kuma yin watsi da zaɓe na ƙara bai wa ‘yan siyasa damar yin abin da bai dace ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Ƙarfinku yana cikin ƙuri’arku” – CAN
Fasto Hayab ya jaddada cewa ƙuri’ar ‘yan ƙasa tana da muhimmanci, domin kuwa da ba ta da amfani ba, ba za a taɓa ganin ana sayen ta da kuɗi ba.
Ya ce:
“Ya kamata 'yan Najeriya su gane cewa ƙarfi na gaskiya yana hannun masu ƙuri’a, ba cikin kuɗin da ake raba wa a lokacin zaɓe ba.”
Shugaban CAN ya kuma yi kira ga malaman addinai su ɗauki nauyin wayar da kan jama’a domin zaburar da mutane su yanki katin.
Ya bayyana wannan mataki a matsayin hanya mafi tasiri wajen tura saƙon wayar da kan jama’a cikin sauƙi.
Bukatar sauƙaƙa rajista ga jama’a
Kungiyar CAN ta kuma roƙi hukumar INEC da ta ƙara kusantar da cibiyoyin rajista ga jama’a musamman a yankunan karkara.

Kara karanta wannan
INEC: An bayyana jihar da ta fi ko ina kokari, mutane miliyan 1.3 sun yi rajistar katin zabe
Wannan, a cewar Hayab, zai bai wa ‘yan Najeriya da dama damar shiga cikin tsarin ba tare da wahala ba.
Hukumar zaɓe ta bayyana cewa an buɗe shafin rajistar yanar gizo a ranar 18 ga watan Agusta, 2025, sannan rajistar kai tsaye ta fara a ranar 25 ga watan Agusta, 2025.

Source: Getty Images
Za a ci gaba da gudanar da aikin har zuwa ranar 30 ga watan Agusta, 2026 a ofisoshi 811 na jihohi da ƙananan hukumomi a faɗin ƙasar.
INEC ta ƙara da cewa sama da mutane miliyan 1.3 ne suka kammala rajistar ta yanar gizo a mako na farko, yawancin su matasa masu shekaru tsakanin 18 zuwa 34.
Osun ta wuce Kano a yankar katin zabe
A wani rahoton, kun ji cewa hukumar INEC ta fitar da sanarwa bayan cika mako daya da fara rajistar katin zabe ta yanar gizo.
Rahotanni sun nuna cewa jihar Osun ce ta farko, Legas na biye da ita yayin da a jihohin Arewa kuma Kaduna ta zamo ta farko.
Masana sun bayyana cewa zaben gwamna da za a yi a Osun a 2026 na da nasaba da yadda mutane ke yankar kati sosai a jihar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng