Kudi Ya Hada Rigima tsakanin Gwamnatin Tinubu da Gwamna, An Tafi Kotun Koli
- Jihar Osun ta kai ƙara kotun koli tana kalubalantar rike kuɗin kananan hukumomi da gwamnatin tarayya ta yi
- Ƙarar ta dogara da hukuncin kotunan baya da suka tabbatar da sahihancin zaben kananan hukumomin da aka yi a jihar
- Osun na neman kotu ta umarci sakin kuɗin gaba ɗaya tare da hana gwamnatin tarayya sake yin irin hakan a nan gaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Osun - Gwamnatin jihar Osun ta dauki mataki mai tsauri inda ta shigar da ƙarar gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu a gaban kotun koli.
Ta ce an rike kuɗin da ake warewa ga kananan hukumomin jihar tun watan Maris na shekarar 2025.

Source: Twitter
Jaridar Tribune ta wallafa cewa karar, wacce aka shigar a ranar Litinin, ta samu jagorancin fitattun lauyoyi Mike Ozekhome (SAN) da Musibau Adetunbi (SAN).
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sun nemi kotun koli ta tilasta gwamnatin tarayya ta saki kuɗin gaba ɗaya tare da dakatar da abin da suka bayyana a matsayin karya kundin tsarin mulki.
Osun ta shigar da gwamnatin tarayya kara
A cikin ƙarar, gwamnatin Osun ta bayyana cewa babban lauyan gwamnatin Najeriya ya gaza bin hukuncin kotun tarayya na Osogbo.
Ta ce an yanke hukuncin ne a rangwar 30 ga Nuwamba, 2022, da kuma na kotun daukaka ƙara da aka yanke a ranar 13 ga Yuni, 2025.
Punch ta wallafa cewa jihar Osun ta ce hukunce hukuncen ne suka tabbatar da sahihancin zabukan da aka gudanar a karkashinta.
Ta kara da cewa matakin gwamnatin tarayya na ci gaba da rike kuɗin duk da wadannan hukunce hukuncen ya sabawa sashi na 7 da na 287 na kundin tsarin mulkin Najeriya.

Source: Twitter
Me gwamnatin Osun ke so kotu ta yi?
Gwamnatin Osun ta nemi kotun koli ta bayar da umarni a saki dukkan kuɗin da aka rike tun watan Maris, kuma a biya su kai tsaye zuwa asusun hukumomin da aka zaba.

Kara karanta wannan
Abin kunya: Amurka ta daure Sarkin Najeriya da ya sace Naira biliyan 6.4 na COVID 19
Haka kuma ta nemi kotu ta bayar da umarnin dindindin da zai hana gwamnatin tarayya sake rike kuɗin nan gaba muddin an zabi shugabannin kananan hukumomi bisa ka’ida.
Ta bayyana cewa;
“Rikewa, tsayarwa ko kin biyan kuɗin da ya kamata a tura wa kananan hukumomi abu ne da ya sabawa kundin tsarin mulki, kuma ya wuce ikon babban lauyan gwamnatin tarayya.”
Babban sakataren ma’aikatar kananan hukumomi da harkokin gargajiya na Osun, Olufemi Akande Ogundun, ya bayyana matakin gwamnatin tarayya a matsayin “raina doka da oda.”
Haka kuma, gwamnatin Osun ta kalubalanci matakin babban alkalin kotun tarayya na sauya shari’ar daga Osogbo zuwa Abuja a lokacin hutu, tana mai cewa hakan ya saba dokokin kotu.
Kotu ta daure basaraken Osun a Amurka
A wani rahoton, kun ji cewa wata kotun kasar Amurka ta daura wani basarake dan asalin jihar Osun bayan kama shi da laifi.
Rahotanni sun nuna cewa an samu Sarkin ne da laifi bayan dogon bincike da aka masa kan karkatar da kudi.
Legit Hausa ta gano cewa Sarkin ya hada kai da wani abokinsa wajen karkatar da makudan kudin tallafin annobar korona.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
