Kwana na Gaba: Mataimakin Gwamnan Taraba Ya Dawo bayan Watanni Yana Jinya

Kwana na Gaba: Mataimakin Gwamnan Taraba Ya Dawo bayan Watanni Yana Jinya

  • Mataimakin gwamnan jihar Taraba ya kwashe dogon lokaci ba ya gudanar da aiki a ofis dinsa saboda rashin lafiyar da yake fama da ita
  • Alhaji Aminu Alkali ya kwashe watanni ba tare da gudanar da aikinsa, inda har Gwamna Agbu Kefas, ya bukaci a sanya shi a addu'a
  • Sai dai, mataimakin gwamnan ya dawo birnin Jalingo, duk da cewa gwamnati ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan hakan ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Taraba - Mataimakin gwamnan jihar Taraba, Alhaji Aminu Alkali, ya dawo Jalingo, babban birnin jihar.

Alhaji Aminu Alkali ya dawo jihar ne bayan ya kwashe dogon lokaci ba ya nan.

Mataimakin gwamnan Taraba ya koma ofis
Hotunan Gwamnan Taraba, Agbu Kefas da mataimakinsa, Alhaji Aminu Alkali Hoto: @GovAgbuKefas
Source: Facebook

Majiyoyi sun shaida wa jaridar Daily Trust cewa Alhaji Aminu Alkali ya shigo jihar ne ta filin jirgin sama na Yola a jihar Adamawa.

Kara karanta wannan

Badakalar N6.5bn: Gwamnatin Kano ta bar manyan lam'a wajen wanke hadimin Abba

Mataimakin gwamnan Taraba ya dawo ofis

Duk da cewa babu wata sanarwa ta hukuma daga gwamnati game da dawowarsa, an rika yada wani gajeren bidiyo nasa a shafukan sada zumunta.

An ce ya iso daga Abuja sannan aka kai shi gidansa da ke fadar gwamnati cikin rukunin motoci guda huɗu.

Lokaci na karshe da aka ga Alhaji Aminu Alkali, wanda yake fama da wata rashin lafiya da ba a bayyana ba, a ofis a shi ne watanni takwas da suka gabata.

Wani jami’i da ke aiki a ofishin mataimakin gwamnan, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce:

"Yau ne aka shaida mani cewa mataimakin gwamna ya dawo Jalingo ba tare da sanarwa ba. Ban gan shi lokacin da na shiga ofis ba, amma an gaya mani cewa ya shiga ofishinsa na ɗan lokaci ya gana da wasu manyan jami’ai.”

Me gwamnatin Taraba ta ce kan lamarin?

Kara karanta wannan

'Na yi mulkin gaskiya': Ganduje ya yi zazzafan martani ga Gwamna Abba kan zarge zarge

Mataimakin gwmnan na Taraba ba shi da sakataren yaɗa labarai, amma babban sakataren yaɗa labarai na Gwamna Agbu Kefas, Yusuf Sanda, ya ce bai samu wani rahoto na hukuma ba game da dawowarsa.

Mataimakin gwamnan Taraba ya koma ofis
Hoton mataimakin gwamnan Taraba, Alhaji Aminu Alkali yana jawabi a wajen wani taro Hoto: @Tarabafacts
Source: Twitter
"Na kalli wani gajeren bidiyo da ke nuna mataimakin gwamna a ofis, amma ban san daga ina aka samo shi ba."

- Yusuf Sanda

Mai ba da shawara na musamman kan harkokin yada labarai da sadarwar zamani ga Gwamna Agbu Kefas, Emmanuel Bello, ya bayyana cewa ba zai iya yin wata sanarwa a hukumance ba saboda shi mai magana da yawun gwamna ne.

"Na ga bidiyon da kake magana a kai, amma ba zan iya yin tsokaci ba. Kwamishinan yaɗa labarai ne kawai zai iya yin wata sanarwa ta hukuma kan gwamnatin jiha."

- Emmanuel Bello

Gwamna ya bukaci ayi wa mataimakinsa a addu'a

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas, ya damu da rashin lafiyar mataimakinsa, Alhaji Aminu Alkali.

Gwamna Agbu Kefas ya bukaci mutanen jihar da su sanya mataimakinsa a cikin addu'o'insu domin ya samu lafiya daga jinyar ciwon da yake yi ta tsawon watanni.

Alhaji Aminu Alkali dai ya shafe watanni yana jinya a wani asibiti da ke Abuja, wanda hakan ya hana shi zuwa ofis.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng