Hatsarin Jirgi Ya Rutsa da Manoma a Hanyar zuwa Neman Abinci, An Rasa Rayuka

Hatsarin Jirgi Ya Rutsa da Manoma a Hanyar zuwa Neman Abinci, An Rasa Rayuka

  • An rasa rayuka yayin da jirgin ruwa da ya dauko manoma akalla 20 ya gamu da hatsari a jihar Borno ranar Litinin, 25 ga watan Agusta, 2025
  • Rahotanni sun bayyana cewa manoman sun hau jirgin ne domin su ketare ruwa zuwa gonakinsu, amma tsautsayi ya rutsa da su
  • A rahoton da hukumar NEMA ta fitar kan abin da ya faru, ta ce an yi nasarar ceto mutane 17 a raye yayin da sauran mutum 3 suka rasu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Borno - Manoma uku sun rasa rayukansu bayan jirgin ruwan da suke ciki ya kife a lokacin da suke jigilar doya daga bakin ruwa a kauyen Kubo, karamar hukumar Shani a jihar Borno.

Rahotanni sun bayyana cewa jirgin na dauke da manoma 20 lokacin da ya nutse a ruwa ranar Litinin da ta wuce, amma ma'aikatan agaji sun ceto mutane 17 a raye.

Kara karanta wannan

NSIB ta gano wasu bayanai kan hatsarin jirgin Kaduna, an ji halin da fasinjoji 6 ke ciki

Taswirar Borno
Taswirar jihar Borno a Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Punch ta tattaro cewa rahoton hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) ta yankin Arewa maso Gabas ya bayyana cewa daga cikin manoma 20 da ke cikin jirgin, an ceto mutum 17.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda jirgin ruwa ya kife da manoma

Shugaban karamar hukumar Shani, Abdu Labaki, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce jirgin ya kife ne a lokacin da manoma 20 ke kokarin ketarawa zuwa gonakinsu da safiyar Litinin

Rahoton da NEMA ta fitar kan hatsarin jirgin ya ce:

“Shugaban karamar hukumar Shani ya tabbatar da cewa lamarin ya faru ne da sassafe ranar Litinin, 25 ga Agusta, 2025, lokacin da manoma 20 ke kokarin ketarawa zuwa gonakinsu da ke bakin ruwa.
“Jirgin ya kife saboda nauyin abubuwan da ya dauko sun zarce karfinsa. An ceto mutum 17, amma uku sun mutu kuma an fito da gawawwakin su."

Mazauna yankin sun fadi abin da ya faru

Kara karanta wannan

Hotuna: Jirgin kasar Kaduna zuwa Abuja dauke da fasinjoji ya yi hastari a Hanya

Wani mazaunin yankin, Audu Abu, ya tabbatar da faruwar lamarin ta wayar tarho, inda ya ce har yanzu ana ci gaba da bincike don gano ko akwai wasu da suka bace.

A ruwayar Vanguard, Audu Abu ya ce:

“Hatsarin ya faru ne a Kogin Kubo, a kauyen Kubo na karamar hukumar Shani. Jirgin, wanda ke dauke da sama da mutum 27, ya kife, inda mutane uku suka mutu.
“Muna addu’ar Allah Ya jikan wadanda suka mutu Ya ba iyalan wadanda lamarin ya shafa hakuri, kuma muna rokon Allah ya ba kowa tsaro da kariya,” in ji shi.
Jirgin ruwa.
Hoton wasu jiragen ruwa na gargajiya a cikin kogi Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Wannan lamari na zuwa ne yayin da wasu rahotanni ke nuna cewa ambliyar ruwa ta yi barna sosai a wasu sassan jihar Borno da ke Arewa maso Gabas.

Jirgi ya nutse da mutane a Sokoto

A wani rahoton, kun ji cewa wani jirgin ruwa na kwale-kwale ya gamu da hatsari a karamarnhukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto da ke Arewa maso Yamma.

Rahotanni sun bayana cewa mutanen da hatsarin kwale-kwalen ya rutsa da su suna hanya ne da nufin tsere qa harin yan bindiga a yankin.

Wani mazauni yankin ya bayyana cewa firgici ya barke ne lokacin da mutanen suka hango ‘yan bindigan na kusantowa, abin da ya tilasta musu yin gaggawar tserewa ta ruwa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262