Duk da Ya Yi Murabus, an Dakatar da Tsohon Shugaban Majalisar Dokokin Benue

Duk da Ya Yi Murabus, an Dakatar da Tsohon Shugaban Majalisar Dokokin Benue

  • Tsohon shugaban majalisar dokokin jihar Benue, Aondona Dajoh, ya fuskanci hukunci bayan ya yi murabus daga kan mukaminsa
  • 'Yan majalisar dokokin sun dauki matakin da tsohon shugabanau yayin zaman da suka gudanar a ranar Talata, 26 ga watan Agustan 2025
  • Hakazalika, majalisar ta kuma tabbatar da nadin wasu mutane da Gwamna Hyacinth Alia, yake son ba mukamai a gwamnatinsa

Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Benue - Majalisar dokokin jihar Benue ta dauki matakin dakatar da tsohon shugabanta, Aondona Dajoh.

Majalisar dokokin ta Benue ta dakatar da Aondona Dajoh ne har na tsawon watanni uku bisa zargin kokarin tsige Gwamna Hyacinth Alia.

An dakatar da tsohon shugaban majalisar dokokin Benue
Hoton majalisar dokokin jihar Benue Hoto: Benue State House of Assembly
Source: Facebook

Majalisa ta dakatar da Aondona Dajoh

Jaridar The Punch ta rahoto cewa an dakatar da Aondona Dajoh ne yayin zaman majalisar na ranar Talaga, 26 ga watan Agustan 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dakatarwar da aka yi wa Aondona Dajoh ta biyo bayan wani kuduri da ɗan majalisa mai wakiltar mazabar Kyan, Terna Shimawua, ya gabatar.

Kara karanta wannan

Bayan zargin gwamna da rike kuɗin jama'a, an dakatar da ɗan majalisa na wata 3

James Umoru daga mazabar Apa ya mara wa kudirin baya a yayn zaman majalisar na ranar Talata, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

Terna Shimawua, wanda ya gabatar da ƙudurin, yana ɗaya daga cikin ’yan majalisar da Dajoh ya dakatar a ranar Juma’a da ta gabata kafin ya yi murabus daga kujerar shugaban majalisar.

Shugaban majalisar na yanzu, Alfred Berger, wanda ya yanke hukunci kan kudurin, ya rage dakatarwar Dajoh daga watanni shida zuwa uku ba tare da neman a kada kuri’a kan lamarin ba kamar yadda aka saba.

'Yan majalisa sun amince da bukatar Gwamna Alia

Hakazalika majalisar dokokin ta kuma tabbatar da nadin Timothy Yangien Ornguga a matsayin kwamishina.

Timothy Yangien Ornguga, malami a fannin karatun lauya a jami’ar jihar Benue, na daga cikin mutanen da majalisar karkashin jagorancin Aondona Dajoh, ta ki amincewa da nadinsu.

An dakatar da Aondona Dajoh
Hoton tsohon shugaban majalisar dokokin Benue, Aondona Dajoh Hoto: Hon. Aondona Dajoh
Source: Facebook

Sai dai, sabon shugaban majalisar, yayin da yake karanta wata wasika daga Gwamna Hyacinth Alia a ranar Talata, ya tantance karin mutane biyar da aka nada.

Alfred Berger ya bayyana cewa gwamnan na da yakinin cewa Ornguga da James Dwem, wadanda tsohon kakakin ya ki amincewa da nadinsu, ba a taba samun su da laifi a kotu ba duk da koke-koken da aka shigar kan nadin nasu.

Kara karanta wannan

Makinde: Gwamna zai mika ragamar mulki ga mataimakinsa, an ji dalili

Abin mamaki, ’yan majalisar da a da suka yi adawa da tabbatar da nadin na su a wancan lokacin, sun yi shiru baki ɗaya lokacin da shugaban majalisar ya tabbatar da su ba tare da yin kuri’ar “eh” ko “a’a” kamar yadda aka saba ba.

Majalisar ta kuma dage dakatar da wasu masu rike da mukamai guda uku da gwamnan ya dakatar a baya.

Majalisar dokokin Benue ta yi sabon shugaba

A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar dokokin jihar Benue ta zabi sabon shugaba biyo bayan murabus din Aondona Dajoh.

Majalisar dokokin ta Benue ta zabi Alfred Berger a matsayin sabon shugabanta wanda zai ci gaba da jan ragamarta.

Zamansa shugaba dai na zuwa ne bayan an janye dakatarwar da aka yi masa tare da wasu 'yan majalisa guda uku.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng