INEC: An bayyana jihar da ta fi ko ina kokari, mutane miliyan 1.3 sun yi rajistar katin zabe
- Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, INEC ta ce sama da mutum miliyan 1.3 ne suka yi rajistar zaɓe a cikin sati guda
- Hukumar ta sanar da cewa jihar Osun ta jagoranci jihohi da mafi yawan masu rajista sama da dubu 393
- INEC ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da rajistar har zuwa 30 ga watan Agusta, 2026 domin ba ƴan Najeriya cikakkiyar dama
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Osun – Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa akalla mutum 1,379,342 ne suka kammala rajistar zaɓe ta intanet a cikin mako guda na fara aikin.
Kwamishinan INEC na ƙasa kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai da wayar da kan masu zaɓe, Sam Olumekun, ne ya bayyana hakan.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa INEC ta bayyana rukuni na mutane da jihohin da su ka mayar da hankali wajen rajistar katin zaɓen ta intanet.
INEC: Ƴan Najeriya suna rajistar katin zabe
Jaridar Punch ta wallafa cewa a cikin sanarwa da INEC ta fitar a ranar Litinin, ta ce an samu ƙarin masu rajistar ne daga ranar 18 zuwa 24 ga watan Agusta.
Sam Olumekun ya ce cikin waɗanda suka yi rajista akwai maza 661,846 (47.96%) da mata 717,856 (52.04%).
Daga cikin wannan adadi, matasa ‘yan shekaru 18 zuwa 34 sun fi yawa da mutum 860,286 (62.37%) wajen yin rajista.
Ya ƙara da cewa daliban da su ka yi rajista aun kai 374,534 (27.15%), yayin da masu buƙata ta musamman 27,089 (1.96%) suma suka shiga ciki.
'Osun na kan gaba a rajistar zabe,' INEC
Bincike ya nuna cewa jihohi ya nuna Osun ta samu mafi yawan rajistar katin zaɓen da mutum 393,269 (28.5%).
Sai kuma jihar Legas mai mutum 222,205 (16.1%), sai Ogun da mutum 132,823 (9.6%) da kuma Babban Birnin Tarayya (FCT) da mutum 107,682.

Source: Twitter
Jihohi mafi ƙarancin rajistasun haɗa da Ebonyi (261), Imo (481), Enugu (484), Abia (772) da Taraba (2,395).
A Arewa, mutum 61,592 ne su ka yi rajista a Kaduna, sai Kogi da mutum 58,546 da Kebbi 35,009.
Masana sun ce yawan fitowar jihar Osun na da alaƙa da zaɓen gwamnan 2026, inda ake sa ran za a fafata kafin zaɓen 2027.
ACF ta magantu kan rajistar katin zabe
Mai magana da yawun ƙungiyar ACF a Kano, Bello Sani Galadanchi ya ce dole ƴam Arewa su yi rajistar katin zabe.
Ya ce:
"Damar ka ita ce waɗanda ba su ƙarasa shekaru 18 a wancan zaɓe, su ka iso wadannan shekaru, ya kamata su je su yi rajista."
"Wadanda su ka canja muhalli, su ma su ke su yi rajista, wanda kuma ya ke da ƴan matsaloli game da katinsa na zabe, shi ma ya je a gyara masa."
"Bai kamata sauran sassan kasar nan sun ɗauki abin nan da muhimmanci ba, a ce mu muna wasa da shi."
INEC ta fara rajistar zaɓe
A wani labarin, mun wallafa cewa Hukumar INEC ta kaddamar da sabon tsarin rajistar masu kada kuri’a a fadin ƙasar daga ranar Litinin, 18 ga watan Agusta, 2025.
Za a fara ne da rajistar farko ta yanar gizo, kafin a buɗe ofisoshin hukumar a jihohi da kananan hukumomi daga ranar 25 ga watan Agusta gabanin zaɓen 2027.
A sanarwar da hukumar zaɓe ta ƙasa, INEC ta fitar, ta ce an buɗe rajista ofisoshinta na jihohi 36 da kuma kananan hukumomi 774 a fadin Najeriya.
Asali: Legit.ng


