Kwana Ya Kare: Fitaccen Mawakin Najeriya, Alhaji Bello Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- Fitaccen mawakin gargajiya da al'adun yarbawa, Isma'ila Dele Bello, wanda aka fi sani da Alhaji Ahuja Bello ya riga mu gidan gaskiya
- Diyarsa, Bello Festus Aderemi ce ta tabbatar da rasuwar mawakin, tana mai bayyana irin girman rashin da suka yi
- Rahotanni sun bayyana cewa sanannen mawakin ya rasu ne sa'o'i 24 kacal bayan ya cika shekara 83 da haihuwa a duniya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Oyo - Fitaccen mawakin al'adun yarbawa a Najeriya, Alhaji Ahuja Bello, ya rasu da safiyar Litinin, kwana guda bayan ya yi bikin cika shekaru 83 da haihuwa.
Ahuja Bello ya shahara a shekarun 1970s da 1980s, lokacin da manyan mawaka irin su King Sunny Ade da Commander Ebenezer Obey ke haskawa a fagen waka.

Source: Facebook
An tabbatar da rasuwar Alhaji Ahuja Bello
Diyar marigayi mawakin, Bello Festus Aderemi ce ta tabbatar da rasuwar mahaifin ta a wata sanarwa da ta wallafa a shafin Facebook yau Litinin.
Ta rubuta cewa:
“Ka huta lafiya mahaifina da nake kauna, Alhaji Ahuja Bello. Muna sonka amma Allah ya fi sonka.”
Shafin tawagarsa mai suna Ahuja Bello and His Golden Eagles Band ya tabbatar da rasuwar a sakon da ya wallafa a Facebook yau Litinin, inda aka rubuta cewa:
“Ko da ka tafi, haskenka yana ci gaba da haskawa a zukatanmu. Allah ya jikan Ahuja Bello.”
Takaitaccen tarihin fitaccen mawakin
An haifi Ahuja Bello, aka rada masa sunan Ismaila Dele Bello a ranar 24 ga Agusta, 1942, a garin Iseyin, jihar Oyo.
Ya kasance shahararren mawakin gargajiya na yarbawa watau mai kida da waka, wanda ya yi fice a shekarun 1970s zuwa 1980s.
Kafin ya rungumi harkar waka, ya fara aikinsa a matsayin kwararren mai gyaran na’urorin lantarki, daga bisani ya kafa kungiyarsa mai suna Ahuja Bello and His Golden Eagles Band a shekarar 1976.

Kara karanta wannan
'Iya kudinka, iya gaskiyarka,' Sarkin Musulmi ya ce mai dukiya ke sayen adalci a Najeriya
Ya kasance fitacce a duniyar wakar gargajiya a Najeriya, kuma ya kara samun shahara ta hanyar fitattun kundin wakokinsa irinsu “Awa ti Danfo” da “Ariya ti de”.

Source: Facebook
Yadda Ahuja Bello ya samu daukaka a Landan
A shekarar 1979, ya yi tafiya zuwa Landan domin daukar wakar "Ahuja a London, inda ya hadu kuma ya yi abota da fitaccen mawakin nan, Bob Marley.
Sai dai a ranar 24 ga Yuli, 1982, wani hatsari ya rutsa da shi, wata guda kafin zagayowar ranar haihuwarsa ta 40, lamarin da ya shafi aikinsa.
Duk da haka, daga baya ya sake dawo da karfin sa a harkar waka a wancan lokaci, yanzu kuma Allah ya karbi ranaa a 2025, cewar rahoton The Cable.
'Yar wasar barkwanci ta mutu tana wasa a Abia
A baya, kun ji cewa fitacciyar mai rawar barkwanci da nishadantar da al'umma, Mrs. Nwandinma Dickson, wadda aka fi sani da “Nwayi Garri,” ta rasa ranta.
Mai wasan barkwancin ta gamu da ajali ne bayan ta fadi tana cikin wasa a taron da aka shirya a karamar hukumar Ugwunagbo a jihar Abia.
Bayanai sun nuna cewa ta shirya yin rawa da wasan kwaikwayo a babban taron da ake zargin matar gwamnan jihar Abia, Priscilla Chidinma Otti, ce ta shirya.
Asali: Legit.ng
