'Dalilin da Ya Sa Obasanjo Ya Tsani Buhari', Garba Shehu Ya Yi Bayani
- Mai magana da yawun tsohon shugaban kasa, marigayi Muhammadu Buhari, ya yi bayani kan sabanin da ke tsakanin ubangidansa da Olusegun Obasanjo
- Garba Shehu ya bayyana cewa Obasanjo ya tsani Buhari ne kawai saboda ya gaza biya masa wata bukata da ya nema lokacin da yake kan mulki
- Martanin na sa na zuwa ne bayan Obasanjo ya yi kalamai masu kaushi kan gwamnatin marigayi Buhari wanda ya rasu a watan Yunin 2025
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Mai magana da yawun tsohon shugaban kasa marigayi Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu, ya yi wa Olusegun Obasanjo, martani kan sukar ubangidansa.
Garba Shehu ya bayyana sukar da Obansanjo ya yi wa Buhari a matsayin wanda ba don komai ba, sai don tsanar da ya yi masa.

Source: Twitter
Jaridar Leadership ta ce ta tuntubi Garba Shehu don yin martani ga kalaman da Obasanjo ya yi a kan gwamnatin tsohon shugaban kasa Buhari.

Kara karanta wannan
"Mafi muni a tarihin Najeriya": Obasanjo ya hada Buhari da Tinubu ya yi musu saukale
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Obasanjo ya caccaki gwamnatin Buhari
Olusegun Obasanjo dai ya caccaki gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari a cikin wani sabon littafi da ya rubuta.
A cikin littafin, ya bayyana gwamnatin Buhari a matsayin gwamnatin farar hula mafi muni a tarihin Najeriya.
Tsokacin Garba Shehu kan alakar Buhari-Obasanjo
A cewar Garba Shehu, ya riga ya bayyana dalilin da ya sa Obasanjo bai taɓa son Buhari ba a cikin littafinsa na baya-bayan nan mai suna “According to the President: Lessons from a Presidential Spokesman’s Experience”.
Tsohon hadimin na Buhari ya shawarci a duba littafin domin ganin cikakkun dalilan.
Duk da haka, Garba Shehu ya ce marigayi tsohon shugaban kasar ya mutunta Obasanjo sosai, sai dai sun samu rashin jituwar ne kan wani buƙata da bai biya masa ba.
Meyasa Obasanjo yake adawa da Buhari?
A cikin littafin, wanda Garba Shehu ya fitar, ya yi zargin cewa Obasanjo ya gabatar da wasu bukatu ga Buhari a lokacin yana kan mulki.

Kara karanta wannan
Shugaba Tinubu ya kadu da Allah ya yiwa tsohon gwamna kuma jigon APC rasuwa a Abuja

Source: Twitter
"Akwai mutane da dama na kusa da Buhari da suke ganin babban dalilin da ya haddasa rikici tsakaninsa da wanda ya fi shi a soja, wato Shugaba Olusegun Obasanjo, wanda yake girmamawa kuma yake daraja shi sosai."
"Shi ne kan wata bukata da Obasanjo ya gabatar masa, cewa a ba wani dan kwangila da ya fi so, kwangilar aikin samar da wutar lantarki ta Mambilla."
"A kan wannan batu ne Buhari cikin ladabi ya ce wa tsohon shugaban kasan ya bar shi ya tafiyar da al’amarin yadda ya dace, tare da bin ka’idojin tsarin da aka tanada."
- Garba Shehu
Obasanjo ya soki bangaren shari'a
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya nuna damuwarsa kan yadda abubuwa suka tabarbare a bangaren shari'a.
Olusegun Obasanjo ya nuna damuwa kan yadda alkalai suka fi maida hankali wajen karbar cin hanci, maimakon tabbatar da gaskiya da adalci.
Tsohon shugaban kasan ya bayyana cewa wannan koma baya da aka samu a wajen alkalai, ya sanya jama'a suka dawo daga rakiyar bangaren shari'a.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng